Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

4 An-Nisā' ٱلنِّسَاء

< Previous   176 Āyah   The Women      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

4:92 وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ أَن يَقْتُلَ مُؤْمِنًا إِلَّا خَطَـًٔا ۚ وَمَن قَتَلَ مُؤْمِنًا خَطَـًٔا فَتَحْرِيرُ رَقَبَةٍ مُّؤْمِنَةٍ وَدِيَةٌ مُّسَلَّمَةٌ إِلَىٰٓ أَهْلِهِۦٓ إِلَّآ أَن يَصَّدَّقُوا۟ ۚ فَإِن كَانَ مِن قَوْمٍ عَدُوٍّ لَّكُمْ وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَتَحْرِيرُ رَقَبَةٍ مُّؤْمِنَةٍ ۖ وَإِن كَانَ مِن قَوْمٍۭ بَيْنَكُمْ وَبَيْنَهُم مِّيثَـٰقٌ فَدِيَةٌ مُّسَلَّمَةٌ إِلَىٰٓ أَهْلِهِۦ وَتَحْرِيرُ رَقَبَةٍ مُّؤْمِنَةٍ ۖ فَمَن لَّمْ يَجِدْ فَصِيَامُ شَهْرَيْنِ مُتَتَابِعَيْنِ تَوْبَةً مِّنَ ٱللَّهِ ۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمًا
4:92 Kuma bã ya kasancẽwa ga mũmini ya kashe wani mũmini, fãce bisa ga kuskure. Kuma wanda ya kashe mũmini bisa ga kuskure, sai ya 'yanta wuya mũmina tare da mĩƙa diyya ga mutãnensa, ãce idan sun bari sadaka. Sa'an nan idan (wanda aka kashe) ya kasance daga wasu mutãne maƙiya a gare ku, kuma shi mũminine, sai ya 'yanta wuya mũmina. Kuma idan ya kasance daga wasu mutãne ne (waɗanda) a tsakãninku da tsakãninsu akwai alkawari, sai ya bãyar da diyya ga mutãnensa, tare da 'yanta wuya mũmina. To, wanda bai sãmi (wuyan ba) sai azumin watanni biyu jẽre, dõmin tũba daga Allah. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima. - Abubakar Gumi (Hausa)