Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

33 Al-'Aĥzāb ٱلْأَحْزَاب

< Previous   73 Āyah   The Combined Forces      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

33:53 يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ لَا تَدْخُلُوا۟ بُيُوتَ ٱلنَّبِىِّ إِلَّآ أَن يُؤْذَنَ لَكُمْ إِلَىٰ طَعَامٍ غَيْرَ نَـٰظِرِينَ إِنَىٰهُ وَلَـٰكِنْ إِذَا دُعِيتُمْ فَٱدْخُلُوا۟ فَإِذَا طَعِمْتُمْ فَٱنتَشِرُوا۟ وَلَا مُسْتَـْٔنِسِينَ لِحَدِيثٍ ۚ إِنَّ ذَٰلِكُمْ كَانَ يُؤْذِى ٱلنَّبِىَّ فَيَسْتَحْىِۦ مِنكُمْ ۖ وَٱللَّهُ لَا يَسْتَحْىِۦ مِنَ ٱلْحَقِّ ۚ وَإِذَا سَأَلْتُمُوهُنَّ مَتَـٰعًا فَسْـَٔلُوهُنَّ مِن وَرَآءِ حِجَابٍ ۚ ذَٰلِكُمْ أَطْهَرُ لِقُلُوبِكُمْ وَقُلُوبِهِنَّ ۚ وَمَا كَانَ لَكُمْ أَن تُؤْذُوا۟ رَسُولَ ٱللَّهِ وَلَآ أَن تَنكِحُوٓا۟ أَزْوَٰجَهُۥ مِنۢ بَعْدِهِۦٓ أَبَدًا ۚ إِنَّ ذَٰلِكُمْ كَانَ عِندَ ٱللَّهِ عَظِيمًا
33:53 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada kũ shiga gidãjen Annabi, fãce fa idan an yi izni a gare ku zuwa ga wani abinci, bã da kun tsaya jiran nunarsa ba, kuma amma idan an kira ku, to, ku shiga, sa'an nan idan kun ci, to ku wãtse, kuma bã da kun tsaya kunã masu hĩra da wani Iãbãri ba. Lalle wannan yanã cũtar da Annabi, to, yanã jin kunyarku, alhãli kuwa Allah bã Ya jin kunya daga gaskiya. Kuma idan zã ku tambaye su waɗansu kãyã, to, ku tambaye su daga bãyan shãmaki. Wannan ya fi muku tsarki ga zukãtanku da zukãtansu. Kuma bã ya halatta a gare ku, ku cũci Manzon Allah, kuma bã ya halatta ku auri mãtansa a bãyansa har abada. lalle wannan a gare ku yã kasance babban abu a wurin Allah. - Abubakar Gumi (Hausa)