Selected
Original Text
Abubakar Gumi
Abdullah Yusuf Ali
Abdul Majid Daryabadi
Abul Ala Maududi
Ahmed Ali
Ahmed Raza Khan
A. J. Arberry
Ali Quli Qarai
Hasan al-Fatih Qaribullah and Ahmad Darwish
Mohammad Habib Shakir
Mohammed Marmaduke William Pickthall
Muhammad Sarwar
Muhammad Taqi-ud-Din al-Hilali and Muhammad Muhsin Khan
Safi-ur-Rahman al-Mubarakpuri
Saheeh International
Talal Itani
Transliteration
Wahiduddin Khan
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.
16:1
أَتَىٰٓ أَمْرُ ٱللَّهِ فَلَا تَسْتَعْجِلُوهُ ۚ سُبْحَـٰنَهُۥ وَتَعَـٰلَىٰ عَمَّا يُشْرِكُونَ
16:1
Al'amarin Allah yã zo, sabõda haka kada ku nẽmi hanzartãwarsa. Tsarkin Allah ya tabbata, kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:2
يُنَزِّلُ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةَ بِٱلرُّوحِ مِنْ أَمْرِهِۦ عَلَىٰ مَن يَشَآءُ مِنْ عِبَادِهِۦٓ أَنْ أَنذِرُوٓا۟ أَنَّهُۥ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱتَّقُونِ
16:2
Yanã sassaukar da malã'iku da Rũhi daga umurninSaa kan wanda Yake so daga bãyinSa, cẽwa ku yi gargaɗi cẽwa: Lalle ne shĩ, bãbu abin bautãwa fãce Ni, sabõda haka ku bĩ Ni da taƙawa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:3
خَلَقَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ بِٱلْحَقِّ ۚ تَعَـٰلَىٰ عَمَّا يُشْرِكُونَ
16:3
Ya halicci sammai da ƙasa da gaskiya. Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:4
خَلَقَ ٱلْإِنسَـٰنَ مِن نُّطْفَةٍ فَإِذَا هُوَ خَصِيمٌ مُّبِينٌ
16:4
Ya halicci mutum daga maniyyi, sai gã shi yanã mai husũma bayyananniya. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:5
وَٱلْأَنْعَـٰمَ خَلَقَهَا ۗ لَكُمْ فِيهَا دِفْءٌ وَمَنَـٰفِعُ وَمِنْهَا تَأْكُلُونَ
16:5
Da dabbõbin ni'ima, Ya halicce su dõminku. A cikinsu akwai abin yin ɗumi da waɗansu amfãnõni, kuma daga gare su kuke ci. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:6
وَلَكُمْ فِيهَا جَمَالٌ حِينَ تُرِيحُونَ وَحِينَ تَسْرَحُونَ
16:6
Kuma kunã da kyau a cikinsu a lõkacin da suke kõmõwa daga kĩwo da maraice da lõkacin da suke sakuwã. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:7
وَتَحْمِلُ أَثْقَالَكُمْ إِلَىٰ بَلَدٍ لَّمْ تَكُونُوا۟ بَـٰلِغِيهِ إِلَّا بِشِقِّ ٱلْأَنفُسِ ۚ إِنَّ رَبَّكُمْ لَرَءُوفٌ رَّحِيمٌ
16:7
Kuma sunã ɗaukar kãyanku mãsu nauyi zuwa ga wani gari, ba ku kasance mãsu isa gare shi ba, fãce da tsananin wahalar rãyuka, Lalle ne Ubangijinka ne, haƙĩƙa, Mai tausayi, Maijin ƙai. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:8
وَٱلْخَيْلَ وَٱلْبِغَالَ وَٱلْحَمِيرَ لِتَرْكَبُوهَا وَزِينَةً ۚ وَيَخْلُقُ مَا لَا تَعْلَمُونَ
16:8
Kuma da dawãki da alfadarai da jãkuna, dõmin ku hau su, kuma da ƙawa. Kuma Yana halitta abin da ba ku sani ba. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:9
وَعَلَى ٱللَّهِ قَصْدُ ٱلسَّبِيلِ وَمِنْهَا جَآئِرٌ ۚ وَلَوْ شَآءَ لَهَدَىٰكُمْ أَجْمَعِينَ
16:9
Kuma ga Allah madaidaiciyar hanya take kuma daga gare ta akwai mai karkacẽwa. Kuma da Yã so, dã Ya shiryar da ku gabã ɗaya. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:10
هُوَ ٱلَّذِىٓ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً ۖ لَّكُم مِّنْهُ شَرَابٌ وَمِنْهُ شَجَرٌ فِيهِ تُسِيمُونَ
16:10
Shĩ ne Wanda Ya saukar da ruwa daga sama dõminku, daga gare shi akwai abin sha, kuma daga gare shi itãce yake, a cikinsa kuke yin kĩwo. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:11
يُنۢبِتُ لَكُم بِهِ ٱلزَّرْعَ وَٱلزَّيْتُونَ وَٱلنَّخِيلَ وَٱلْأَعْنَـٰبَ وَمِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِ ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ
16:11
Yanã tsirar da shũka game da shi, dõminku zaitũni da dabĩnai da inabai, kuma daga dukan 'yã'yan itãce. Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke yin tunãni. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:12
وَسَخَّرَ لَكُمُ ٱلَّيْلَ وَٱلنَّهَارَ وَٱلشَّمْسَ وَٱلْقَمَرَ ۖ وَٱلنُّجُومُ مُسَخَّرَٰتٌۢ بِأَمْرِهِۦٓ ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ
16:12
Kuma Ya hõrẽ muku dare da wuni da rãnã da watã kuma taurãri hõrarru ne da umurninSa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke hankalta. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:13
وَمَا ذَرَأَ لَكُمْ فِى ٱلْأَرْضِ مُخْتَلِفًا أَلْوَٰنُهُۥٓ ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً لِّقَوْمٍ يَذَّكَّرُونَ
16:13
Kuma abin da Ya halitta muku a cikin ƙasa, yana mai sãɓãnin launukansa. Lalle ne a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke tunãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:14
وَهُوَ ٱلَّذِى سَخَّرَ ٱلْبَحْرَ لِتَأْكُلُوا۟ مِنْهُ لَحْمًا طَرِيًّا وَتَسْتَخْرِجُوا۟ مِنْهُ حِلْيَةً تَلْبَسُونَهَا وَتَرَى ٱلْفُلْكَ مَوَاخِرَ فِيهِ وَلِتَبْتَغُوا۟ مِن فَضْلِهِۦ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
16:14
Kuma Shĩ ne Ya hõrẽ tẽku dõmin ku ci wani nama sãbõ daga gare shi, kuma kunã fitarwa, daga gare shi, ƙawã wadda kuke yin ado da ita. Kuma kuna ganin jirãge sunã yankan ruwa a cikinsa kuma dõmin ku yi nẽman (fatauci) daga falalarSa. Kuma mai yiwuwa ne kuna gõdẽwa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:15
وَأَلْقَىٰ فِى ٱلْأَرْضِ رَوَٰسِىَ أَن تَمِيدَ بِكُمْ وَأَنْهَـٰرًا وَسُبُلًا لَّعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ
16:15
Kuma Ya jẽfa, a cikin ƙasa, tabbatattun duwatsu dõmin kada ta karkata da ku, da kõguna da hanyõyi, ɗammãninku kunã shiryuwa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:16
وَعَلَـٰمَـٰتٍ ۚ وَبِٱلنَّجْمِ هُمْ يَهْتَدُونَ
16:16
Kuma da waɗansu alãmõmi, kuma da taurãri sunã mãsu nẽman shiryuwa (ga tafiyarsu ta fatauci). - Abubakar Gumi (Hausa)
16:17
أَفَمَن يَخْلُقُ كَمَن لَّا يَخْلُقُ ۗ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
16:17
Shin, wanda Yake yin halitta yanã yin kama da wanda ba ya yin halitta? Shin fa, bã ku tunãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)
16:18
وَإِن تَعُدُّوا۟ نِعْمَةَ ٱللَّهِ لَا تُحْصُوهَآ ۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ
16:18
Kuma idan kun ƙidãya ni'imar Allah, bã ku iya lissafa ta. Lalle ne Allah, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:19
وَٱللَّهُ يَعْلَمُ مَا تُسِرُّونَ وَمَا تُعْلِنُونَ
16:19
Kuma Allah Yanã sanin abin da kuke asirtãwa da abin da kuke bayyanãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:20
وَٱلَّذِينَ يَدْعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ لَا يَخْلُقُونَ شَيْـًٔا وَهُمْ يُخْلَقُونَ
16:20
Kuma waɗanda suke kira, baicin Allah, ba su halicci kõme ba, kuma sũ ne ake halittawa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:21
أَمْوَٰتٌ غَيْرُ أَحْيَآءٍ ۖ وَمَا يَشْعُرُونَ أَيَّانَ يُبْعَثُونَ
16:21
Matattũ ne, bã su da rai, kuma ba su san a wane lõkaci ake tãyar da su ba. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:22
إِلَـٰهُكُمْ إِلَـٰهٌ وَٰحِدٌ ۚ فَٱلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِٱلْـَٔاخِرَةِ قُلُوبُهُم مُّنكِرَةٌ وَهُم مُّسْتَكْبِرُونَ
16:22
Abin bautawarku, abin bautãwa ne guda, to, waɗanda ba su yin ĩmãni da Lãhira, zukãtansu mãsu musu ne, kuma su makangara ne. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:23
لَا جَرَمَ أَنَّ ٱللَّهَ يَعْلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعْلِنُونَ ۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلْمُسْتَكْبِرِينَ
16:23
Haƙĩƙa, lalle ne, Allah Yanã sanin abin da suke asirtãwa da abin da suke bayyanãwa. Lalle ne Shi, bã Ya Son mãsu girman kai. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:24
وَإِذَا قِيلَ لَهُم مَّاذَآ أَنزَلَ رَبُّكُمْ ۙ قَالُوٓا۟ أَسَـٰطِيرُ ٱلْأَوَّلِينَ
16:24
Idan aka ce musu: "Mẽne ne Ubangijinku Ya saukar?" Sai su ce: "Tãtsũniyõyin mutãnen farko." - Abubakar Gumi (Hausa)
16:25
لِيَحْمِلُوٓا۟ أَوْزَارَهُمْ كَامِلَةً يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ ۙ وَمِنْ أَوْزَارِ ٱلَّذِينَ يُضِلُّونَهُم بِغَيْرِ عِلْمٍ ۗ أَلَا سَآءَ مَا يَزِرُونَ
16:25
Dõmin su ɗauki zunubansu cikakku a Rãnar ¡iyãma, kuma daga zunuban waɗanda suke ɓatarwa bã da wani ilmi ba. To, abin da suke ɗauka na zunubi ya mũnana. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:26
قَدْ مَكَرَ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ فَأَتَى ٱللَّهُ بُنْيَـٰنَهُم مِّنَ ٱلْقَوَاعِدِ فَخَرَّ عَلَيْهِمُ ٱلسَّقْفُ مِن فَوْقِهِمْ وَأَتَىٰهُمُ ٱلْعَذَابُ مِنْ حَيْثُ لَا يَشْعُرُونَ
16:26
Lalle ne waɗanda suke a gabãninsu sun yi mãkirci, sai Allah Ya je wa gininsu daga harsãshensa, sai rufi ya fãɗa a kansu daga bisansu, kuma azãba ta jẽ musu daga inda ba su sani ba. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:27
ثُمَّ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ يُخْزِيهِمْ وَيَقُولُ أَيْنَ شُرَكَآءِىَ ٱلَّذِينَ كُنتُمْ تُشَـٰٓقُّونَ فِيهِمْ ۚ قَالَ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْعِلْمَ إِنَّ ٱلْخِزْىَ ٱلْيَوْمَ وَٱلسُّوٓءَ عَلَى ٱلْكَـٰفِرِينَ
16:27
Sa'an nan a Rãnar ¡iyãma (Allah) Yanã kunyatã su, kuma Yanã cẽwa: "Inã abõkan tãrayyaTa, waɗanda kuka kasance kunã gãbã a cikin ɗaukaka sha'aninsu?" Waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: "Lalle ne wulãkanci a yau da cũta sun tabbata a kan kãfirai." - Abubakar Gumi (Hausa)
16:28
ٱلَّذِينَ تَتَوَفَّىٰهُمُ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ ظَالِمِىٓ أَنفُسِهِمْ ۖ فَأَلْقَوُا۟ ٱلسَّلَمَ مَا كُنَّا نَعْمَلُ مِن سُوٓءٍۭ ۚ بَلَىٰٓ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌۢ بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
16:28
Waɗanda malãiku suke karɓar rãyukansu sunã mãsu zãluntar kansu. Sai suka jẽfa nẽman sulhu (suka ce) "Ba mu kasance muna aikata wani mummũnan aiki ba." Kayya! Lalle Allah ne Masani ga abin da kuka kasance kunã aikatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:29
فَٱدْخُلُوٓا۟ أَبْوَٰبَ جَهَنَّمَ خَـٰلِدِينَ فِيهَا ۖ فَلَبِئْسَ مَثْوَى ٱلْمُتَكَبِّرِينَ
16:29
Sai ku shiga ƙõfõfin Jahannama, kunã madawwama a cikinta. Sa'an nan tir da mazaunin mãsu girman kai. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:30
۞ وَقِيلَ لِلَّذِينَ ٱتَّقَوْا۟ مَاذَآ أَنزَلَ رَبُّكُمْ ۚ قَالُوا۟ خَيْرًا ۗ لِّلَّذِينَ أَحْسَنُوا۟ فِى هَـٰذِهِ ٱلدُّنْيَا حَسَنَةٌ ۚ وَلَدَارُ ٱلْـَٔاخِرَةِ خَيْرٌ ۚ وَلَنِعْمَ دَارُ ٱلْمُتَّقِينَ
16:30
Kuma aka ce wa waɗanda suka yi taƙawa, "Mẽne ne Ubangijinku Ya saukar?" Suka ce, "Alhẽri Ya saukar, ga waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya akwai wani abu mai kyau, kuma haƙĩƙa, Lãhira ce mafi alhẽri." Kuma haƙĩƙa, mãdalla da gidan mãsu taƙawa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:31
جَنَّـٰتُ عَدْنٍ يَدْخُلُونَهَا تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ ۖ لَهُمْ فِيهَا مَا يَشَآءُونَ ۚ كَذَٰلِكَ يَجْزِى ٱللَّهُ ٱلْمُتَّقِينَ
16:31
Gidãjen Aljannar zama sunã shigarsu, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã da abin da suke so a cikinsu. Kamar haka Allah ke sãkã wa mãsu taƙawa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:32
ٱلَّذِينَ تَتَوَفَّىٰهُمُ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ طَيِّبِينَ ۙ يَقُولُونَ سَلَـٰمٌ عَلَيْكُمُ ٱدْخُلُوا۟ ٱلْجَنَّةَ بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
16:32
Waɗanda malã'iku suke karɓar rãyukansu sunã mãsu jin dãɗin rai, malã'ikun sunã cẽwa. "Aminci ya tabbata a kanku. Ku shiga Aljanna sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa." - Abubakar Gumi (Hausa)
16:33
هَلْ يَنظُرُونَ إِلَّآ أَن تَأْتِيَهُمُ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ أَوْ يَأْتِىَ أَمْرُ رَبِّكَ ۚ كَذَٰلِكَ فَعَلَ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ وَمَا ظَلَمَهُمُ ٱللَّهُ وَلَـٰكِن كَانُوٓا۟ أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ
16:33
Shin sunã jiran wani abu? Fãce malã'iku su jẽ musu kõ kuwa umurnin Ubangijinka. Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu, suka aikata. Kuma Allah bai zãlunce su ba, kuma amma kansu suka kasance sunã zãlunta. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:34
فَأَصَابَهُمْ سَيِّـَٔاتُ مَا عَمِلُوا۟ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُوا۟ بِهِۦ يَسْتَهْزِءُونَ
16:34
Sai mũnãnan abũbuwan da suka aikata ya sãme su, kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili ya wajaba a kansu. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:35
وَقَالَ ٱلَّذِينَ أَشْرَكُوا۟ لَوْ شَآءَ ٱللَّهُ مَا عَبَدْنَا مِن دُونِهِۦ مِن شَىْءٍ نَّحْنُ وَلَآ ءَابَآؤُنَا وَلَا حَرَّمْنَا مِن دُونِهِۦ مِن شَىْءٍ ۚ كَذَٰلِكَ فَعَلَ ٱلَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۚ فَهَلْ عَلَى ٱلرُّسُلِ إِلَّا ٱلْبَلَـٰغُ ٱلْمُبِينُ
16:35
Kuma waɗanda suka yi shirki suka ce: "Dã Allah Yã so, dã bamu bautã wa kõme ba, baicinSa, mũ ko ubannimmu kuma dã ba mu haramta kõme ba, baicin abin da Ya haramta." Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu suka aikata. To, shin, akwai wani abu a kan Manzanni, fãce iyarwa bayyananniyã? - Abubakar Gumi (Hausa)
16:36
وَلَقَدْ بَعَثْنَا فِى كُلِّ أُمَّةٍ رَّسُولًا أَنِ ٱعْبُدُوا۟ ٱللَّهَ وَٱجْتَنِبُوا۟ ٱلطَّـٰغُوتَ ۖ فَمِنْهُم مَّنْ هَدَى ٱللَّهُ وَمِنْهُم مَّنْ حَقَّتْ عَلَيْهِ ٱلضَّلَـٰلَةُ ۚ فَسِيرُوا۟ فِى ٱلْأَرْضِ فَٱنظُرُوا۟ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلْمُكَذِّبِينَ
16:36
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika a cikin kõwace al'umma da wani Manzo (ya ce): "Ku bauta wa Allah, kuma ku nĩsanci ¦ãgũtu." To, daga gare su akwai wanda Allah Ya shiryar, kuma daga cikinsu akwai wanda ɓata ta wajaba a kansa. Sai ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku dũba yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa ta kasance. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:37
إِن تَحْرِصْ عَلَىٰ هُدَىٰهُمْ فَإِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهْدِى مَن يُضِلُّ ۖ وَمَا لَهُم مِّن نَّـٰصِرِينَ
16:37
Idan ka yi kwaɗayi a kan shiryuwarsu, to, lalle ne, Allah bã Ya shiryar da wanda yake ɓatarwa, kuma bã su da waɗansu mataimaka. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:38
وَأَقْسَمُوا۟ بِٱللَّهِ جَهْدَ أَيْمَـٰنِهِمْ ۙ لَا يَبْعَثُ ٱللَّهُ مَن يَمُوتُ ۚ بَلَىٰ وَعْدًا عَلَيْهِ حَقًّا وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ
16:38
Kuma suka rantse da Allah iyãkar rantsuwarsu (cẽwa) Allah bã ya tãyar da wanda yake mutuwa! Na'am, Yanã tãyarwa. Wa'adi ne (Allah) Ya yi a kanSa tabbatacce, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:39
لِيُبَيِّنَ لَهُمُ ٱلَّذِى يَخْتَلِفُونَ فِيهِ وَلِيَعْلَمَ ٱلَّذِينَ كَفَرُوٓا۟ أَنَّهُمْ كَانُوا۟ كَـٰذِبِينَ
16:39
Dõmin Ya bayyana musu abin da suke sãɓã wa jũna a cikinsa, kuma dõmin waɗanda suka kãfirta su sani cẽwa lalle sũ ne suka kasance maƙaryatã. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:40
إِنَّمَا قَوْلُنَا لِشَىْءٍ إِذَآ أَرَدْنَـٰهُ أَن نَّقُولَ لَهُۥ كُن فَيَكُونُ
16:40
Abin sani kawai, MaganarMu ga wani abu idan Mun nufe shi, Mu ce masa, "Ka kasance; sai yanã kasancẽwa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:41
وَٱلَّذِينَ هَاجَرُوا۟ فِى ٱللَّهِ مِنۢ بَعْدِ مَا ظُلِمُوا۟ لَنُبَوِّئَنَّهُمْ فِى ٱلدُّنْيَا حَسَنَةً ۖ وَلَأَجْرُ ٱلْـَٔاخِرَةِ أَكْبَرُ ۚ لَوْ كَانُوا۟ يَعْلَمُونَ
16:41
Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin sha'anin Allah daga bãyan an zãlunce su, haƙĩƙa Munã zaunar da su a cikin dũniya da alhẽri kuma lalle lãdar Lãhira ce mafi girmã, dã sun kasance sunã sani. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:42
ٱلَّذِينَ صَبَرُوا۟ وَعَلَىٰ رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ
16:42
Waɗanda suka yi haƙuri, kuma ga Ubangijinsu suke dõgara. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:43
وَمَآ أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ إِلَّا رِجَالًا نُّوحِىٓ إِلَيْهِمْ ۚ فَسْـَٔلُوٓا۟ أَهْلَ ٱلذِّكْرِ إِن كُنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ
16:43
Kuma ba Mu aika daga gabaninka ba, fãce waɗansu mazãje Muna yin wahayi zuwa gare su. Sai ku tambayi mutãnen Ambato idan kun kasance ba ku sani ba. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:44
بِٱلْبَيِّنَـٰتِ وَٱلزُّبُرِ ۗ وَأَنزَلْنَآ إِلَيْكَ ٱلذِّكْرَ لِتُبَيِّنَ لِلنَّاسِ مَا نُزِّلَ إِلَيْهِمْ وَلَعَلَّهُمْ يَتَفَكَّرُونَ
16:44
Da hujjõji bayyanannu da littattafai kuma Mun saukar da Ambato zuwa gare ka, dõmin ka bayyana wa mutãne abin da aka sassaukar zuwa gare su, kuma don ɗammãninsu su yi tunãni. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:45
أَفَأَمِنَ ٱلَّذِينَ مَكَرُوا۟ ٱلسَّيِّـَٔاتِ أَن يَخْسِفَ ٱللَّهُ بِهِمُ ٱلْأَرْضَ أَوْ يَأْتِيَهُمُ ٱلْعَذَابُ مِنْ حَيْثُ لَا يَشْعُرُونَ
16:45
Shin fa, waɗanda suka yi mãkircin mũnãnan ayyuka sun amince da Allah, bã zai shafe ƙasa da su ba ko kuwa azãba bã zã ta je musu daga inda ba su sani ba? - Abubakar Gumi (Hausa)
16:46
أَوْ يَأْخُذَهُمْ فِى تَقَلُّبِهِمْ فَمَا هُم بِمُعْجِزِينَ
16:46
Ko kuwa Ya kama su a cikin jujjuyawarsu? Sabõda haka ba su zama masu buwãya ba. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:47
أَوْ يَأْخُذَهُمْ عَلَىٰ تَخَوُّفٍ فَإِنَّ رَبَّكُمْ لَرَءُوفٌ رَّحِيمٌ
16:47
Ko kuwa Ya kama su a kan naƙasa? To, lalle ne Ubangijinka haƙĩƙa Mai tausayi ne, Mai jin ƙai. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:48
أَوَلَمْ يَرَوْا۟ إِلَىٰ مَا خَلَقَ ٱللَّهُ مِن شَىْءٍ يَتَفَيَّؤُا۟ ظِلَـٰلُهُۥ عَنِ ٱلْيَمِينِ وَٱلشَّمَآئِلِ سُجَّدًا لِّلَّهِ وَهُمْ دَٰخِرُونَ
16:48
Shin, ba su Iura ba da abin da Allah Ya halitta kõ mene ne inuwõyinsu suna karkata daga dãma da wajãjen hagu, suna masu sujada ga Allah, alhãli suna masu ƙasƙantar da kai? - Abubakar Gumi (Hausa)
16:49
وَلِلَّهِ يَسْجُدُ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ مِن دَآبَّةٍ وَٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ وَهُمْ لَا يَسْتَكْبِرُونَ
16:49
Kuma ga Allah, abin da yake a cikin sammai da ƙasa na dabba da mala'iku, suke yin sujada, kuma bã su kangara. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:50
يَخَافُونَ رَبَّهُم مِّن فَوْقِهِمْ وَيَفْعَلُونَ مَا يُؤْمَرُونَ ۩
16:50
Suna tsõron Ubangijinsu daga bisansu, kuma suna aikata abin da ake umuruin su. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:51
۞ وَقَالَ ٱللَّهُ لَا تَتَّخِذُوٓا۟ إِلَـٰهَيْنِ ٱثْنَيْنِ ۖ إِنَّمَا هُوَ إِلَـٰهٌ وَٰحِدٌ ۖ فَإِيَّـٰىَ فَٱرْهَبُونِ
16:51
Kuma Allah Ya ce: "Kada ku riƙi abũbuwan bautãwa biyu. Abin sani kawai, wanda ake bautãwa guda ne, sa'an nan sai kuji tsõroNa, Ni kawai." - Abubakar Gumi (Hausa)
16:52
وَلَهُۥ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَلَهُ ٱلدِّينُ وَاصِبًا ۚ أَفَغَيْرَ ٱللَّهِ تَتَّقُونَ
16:52
Kuma Yana da abin da yake a cikin sammai da ƙasa, kuma Yana da addini wanda yake dawwamamme. Shin fa, wanin Allah kuke bĩ da taƙãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)
16:53
وَمَا بِكُم مِّن نِّعْمَةٍ فَمِنَ ٱللَّهِ ۖ ثُمَّ إِذَا مَسَّكُمُ ٱلضُّرُّ فَإِلَيْهِ تَجْـَٔرُونَ
16:53
Kuma abin da yake a gare ku na ni'ima, to, daga Allah ne. Sa'an nan kuma idan cũta ta shãfeku, to, zuwa gare Shi kuke hargõwa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:54
ثُمَّ إِذَا كَشَفَ ٱلضُّرَّ عَنكُمْ إِذَا فَرِيقٌ مِّنكُم بِرَبِّهِمْ يُشْرِكُونَ
16:54
sa'an nan idan Ya kuranye cũtar daga gare ku, sai gã wani ɓangare daga gare ku game da Ubangijinsu sunã shirki. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:55
لِيَكْفُرُوا۟ بِمَآ ءَاتَيْنَـٰهُمْ ۚ فَتَمَتَّعُوا۟ ۖ فَسَوْفَ تَعْلَمُونَ
16:55
Dõmin su kãfirta da abin da Muka bã su. To, ku ji dãɗi, sa'an nan da sannu zã ku sani. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:56
وَيَجْعَلُونَ لِمَا لَا يَعْلَمُونَ نَصِيبًا مِّمَّا رَزَقْنَـٰهُمْ ۗ تَٱللَّهِ لَتُسْـَٔلُنَّ عَمَّا كُنتُمْ تَفْتَرُونَ
16:56
Kuma sunã sanya rabõ ga abin da ba su sani ba daga abin da Muka azurtã su. Ranstuwa da Allah! Lalle ne zã a tambaye ku daga abin da kuka kasance kunã ƙirƙirãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:57
وَيَجْعَلُونَ لِلَّهِ ٱلْبَنَـٰتِ سُبْحَـٰنَهُۥ ۙ وَلَهُم مَّا يَشْتَهُونَ
16:57
Kuma sunã danganta 'ya'ya mãta ga Allah. Tsarkinsa yã tabbata! Kuma sũ ne da abin da suke sha'awa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:58
وَإِذَا بُشِّرَ أَحَدُهُم بِٱلْأُنثَىٰ ظَلَّ وَجْهُهُۥ مُسْوَدًّا وَهُوَ كَظِيمٌ
16:58
Kuma idan aka yi wa ɗayansu bushãra da mace sai fuskarsa ta wuni baƙa ƙirin, alhãli kuwa yanã mai cike da baƙin ciki. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:59
يَتَوَٰرَىٰ مِنَ ٱلْقَوْمِ مِن سُوٓءِ مَا بُشِّرَ بِهِۦٓ ۚ أَيُمْسِكُهُۥ عَلَىٰ هُونٍ أَمْ يَدُسُّهُۥ فِى ٱلتُّرَابِ ۗ أَلَا سَآءَ مَا يَحْكُمُونَ
16:59
Yanã ɓõyẽwa daga mutãne dõmin mũnin abin da aka yimasa bushãra da shi. Shin, zai riƙe shi a kan wulãkanci kõ zai turbuɗe shi a cikin turɓãya To, abin da suke hukuntãwa ya mũnana. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:60
لِلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِٱلْـَٔاخِرَةِ مَثَلُ ٱلسَّوْءِ ۖ وَلِلَّهِ ٱلْمَثَلُ ٱلْأَعْلَىٰ ۚ وَهُوَ ٱلْعَزِيزُ ٱلْحَكِيمُ
16:60
Ga waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba akwai sifar cũta kuma ga Allah akwai sifa mafi ɗaukaka. Kuma shi ne Mabuwãyi, Mai hikima. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:61
وَلَوْ يُؤَاخِذُ ٱللَّهُ ٱلنَّاسَ بِظُلْمِهِم مَّا تَرَكَ عَلَيْهَا مِن دَآبَّةٍ وَلَـٰكِن يُؤَخِّرُهُمْ إِلَىٰٓ أَجَلٍ مُّسَمًّى ۖ فَإِذَا جَآءَ أَجَلُهُمْ لَا يَسْتَـْٔخِرُونَ سَاعَةً ۖ وَلَا يَسْتَقْدِمُونَ
16:61
Kuma dã Allah Yanã kãma mutãne da zãluncinsu, dã bai bar wata dabba ba a kan ƙasa. Kuma amma Yanã jinkirta musu zuwa ga ajali ambatacce. Sa'an nan idan ajalinsu ya zo, bã zã a yi musu jinkiri ba kõ da sa'a guda, kuma bã zã su gabãta ba. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:62
وَيَجْعَلُونَ لِلَّهِ مَا يَكْرَهُونَ وَتَصِفُ أَلْسِنَتُهُمُ ٱلْكَذِبَ أَنَّ لَهُمُ ٱلْحُسْنَىٰ ۖ لَا جَرَمَ أَنَّ لَهُمُ ٱلنَّارَ وَأَنَّهُم مُّفْرَطُونَ
16:62
Kuma sunã sanyã wa Allah abin da suke ƙi, kuma harsunansu na siffanta ƙarya cẽwa lalle ne sunã da abũbuwa mãsu kyau. Bãbu shakka lalle ne sunã da wuta, kuma lalle sũ, waɗanda ake ƙyãlẽwa ne (a cikinta). - Abubakar Gumi (Hausa)
16:63
تَٱللَّهِ لَقَدْ أَرْسَلْنَآ إِلَىٰٓ أُمَمٍ مِّن قَبْلِكَ فَزَيَّنَ لَهُمُ ٱلشَّيْطَـٰنُ أَعْمَـٰلَهُمْ فَهُوَ وَلِيُّهُمُ ٱلْيَوْمَ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
16:63
Rantsuwar Allah! Lalle ne haƙĩƙa Mun aika zuwa ga al'ummomi daga gabãninka, sai Shaiɗan ya ƙawãce musu ayyukansu, sabõda haka shĩ ne majiɓincinsu, a yau, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:64
وَمَآ أَنزَلْنَا عَلَيْكَ ٱلْكِتَـٰبَ إِلَّا لِتُبَيِّنَ لَهُمُ ٱلَّذِى ٱخْتَلَفُوا۟ فِيهِ ۙ وَهُدًى وَرَحْمَةً لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ
16:64
Lalle ba Mu saukar da Littafi ba a kanka, fãce dõmin ka bayyanã musu abin da suka sãɓã wa jũna a cikinsa, kuma dõmin shiriya da rahama ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:65
وَٱللَّهُ أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً فَأَحْيَا بِهِ ٱلْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَآ ۚ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً لِّقَوْمٍ يَسْمَعُونَ
16:65
Kuma Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya rãyar da ƙasa da shi a bãyan mutuwarta. Lalle ne a cikin wannan haƙĩƙa akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke saurãre. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:66
وَإِنَّ لَكُمْ فِى ٱلْأَنْعَـٰمِ لَعِبْرَةً ۖ نُّسْقِيكُم مِّمَّا فِى بُطُونِهِۦ مِنۢ بَيْنِ فَرْثٍ وَدَمٍ لَّبَنًا خَالِصًا سَآئِغًا لِّلشَّـٰرِبِينَ
16:66
Kuma lalle ne, kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'ima; Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikin cikunansu, daga tsakãnin tukar tumbi da jini nõno tsantsan mai sauƙin haɗiya ga mãsu shã. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:67
وَمِن ثَمَرَٰتِ ٱلنَّخِيلِ وَٱلْأَعْنَـٰبِ تَتَّخِذُونَ مِنْهُ سَكَرًا وَرِزْقًا حَسَنًا ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ
16:67
Kuma daga 'ya'yan itãcen dabĩno da inabi. Kunã sãmudaga gare shi, abin mãye da abinci mai kyau. Lalle a cikin wannan, haƙĩƙa, akwai ãyã ga mutãne waɗanda suke hankalta. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:68
وَأَوْحَىٰ رَبُّكَ إِلَى ٱلنَّحْلِ أَنِ ٱتَّخِذِى مِنَ ٱلْجِبَالِ بُيُوتًا وَمِنَ ٱلشَّجَرِ وَمِمَّا يَعْرِشُونَ
16:68
Kuma Ubangjinka Yã yi wahayi zuwa ga ƙudan zuma cẽwa: "Ki riƙi gidãje daga duwãtsu, kuma daga itãce, kuma daga abin da suke ginãwa." - Abubakar Gumi (Hausa)
16:69
ثُمَّ كُلِى مِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِ فَٱسْلُكِى سُبُلَ رَبِّكِ ذُلُلًا ۚ يَخْرُجُ مِنۢ بُطُونِهَا شَرَابٌ مُّخْتَلِفٌ أَلْوَٰنُهُۥ فِيهِ شِفَآءٌ لِّلنَّاسِ ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَةً لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ
16:69
"Sa'an nan ki ci daga dukan 'ya'yan itãce, sabõda haka ki shiga hanyõyin Ubangijinka, sunã hõrarru." Wani abin shã yanã fita daga cikunanta, mai sãɓãwar launukansa a cikinsa akwai wata warkewa ga mutãne. Lalle ne, a cikin wannan, haƙĩƙa, akwaiãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin tunãni. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:70
وَٱللَّهُ خَلَقَكُمْ ثُمَّ يَتَوَفَّىٰكُمْ ۚ وَمِنكُم مَّن يُرَدُّ إِلَىٰٓ أَرْذَلِ ٱلْعُمُرِ لِكَىْ لَا يَعْلَمَ بَعْدَ عِلْمٍ شَيْـًٔا ۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌ قَدِيرٌ
16:70
Kuma Allah ne Ya halicce ku, sa'an nan Yanã karɓar rãyukanku, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwã zuwa ga mafi ƙasƙncin rãyuwa, dõmin kada ya san kõme a bãyan dã ya zama mai ilmi. Lalle Allah ne Masani Mai ĩkon yi. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:71
وَٱللَّهُ فَضَّلَ بَعْضَكُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ فِى ٱلرِّزْقِ ۚ فَمَا ٱلَّذِينَ فُضِّلُوا۟ بِرَآدِّى رِزْقِهِمْ عَلَىٰ مَا مَلَكَتْ أَيْمَـٰنُهُمْ فَهُمْ فِيهِ سَوَآءٌ ۚ أَفَبِنِعْمَةِ ٱللَّهِ يَجْحَدُونَ
16:71
Kuma Allah Ya fifita sãshenku a kan sãshe a arziki. Sa'an nan waɗanda aka fĩfĩta ba su zama mãsu mayar da arzikinsu a kan abin da hannãyensu na dãma suka mallaka ba, har su zama daidai a cikinsa. Shin fa, da ni'imar Allah suke musu? - Abubakar Gumi (Hausa)
16:72
وَٱللَّهُ جَعَلَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَٰجًا وَجَعَلَ لَكُم مِّنْ أَزْوَٰجِكُم بَنِينَ وَحَفَدَةً وَرَزَقَكُم مِّنَ ٱلطَّيِّبَـٰتِ ۚ أَفَبِٱلْبَـٰطِلِ يُؤْمِنُونَ وَبِنِعْمَتِ ٱللَّهِ هُمْ يَكْفُرُونَ
16:72
Kuma Allah Yã sanya muku mãtan aure daga kãwunanku, kuma Ya sanya muku daga mãtan aurenku ɗiyã da jĩkõki, kuma Ya arzũta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi. Shin fa, da ƙarya suke yin ĩmãni, kuma da ni'imar Allah sũ, suke kãfirta? - Abubakar Gumi (Hausa)
16:73
وَيَعْبُدُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَمْلِكُ لَهُمْ رِزْقًا مِّنَ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ شَيْـًٔا وَلَا يَسْتَطِيعُونَ
16:73
Kuma sunã bautã wa, baicin Allah, abin da yake bã ya mallakar wani arziki dõminsu, daga sammai da ƙasa game da kõme, kuma bã su iyawa (ga aikata kõme). - Abubakar Gumi (Hausa)
16:74
فَلَا تَضْرِبُوا۟ لِلَّهِ ٱلْأَمْثَالَ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَعْلَمُ وَأَنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ
16:74
Sa'an nan kada ku bãyar da waɗansu misãlai ga Allah. Lalle ne Allah Yanã sani, kuma kũ, ba ku sani ba. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:75
۞ ضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلًا عَبْدًا مَّمْلُوكًا لَّا يَقْدِرُ عَلَىٰ شَىْءٍ وَمَن رَّزَقْنَـٰهُ مِنَّا رِزْقًا حَسَنًا فَهُوَ يُنفِقُ مِنْهُ سِرًّا وَجَهْرًا ۖ هَلْ يَسْتَوُۥنَ ۚ ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ ۚ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
16:75
Allah Yã buga wani misali da wani bãwa wanda bã ya iya sãmun ĩko a kan yin kõme, da (wani bãwa) wanda Muka azurtã shi daga gare Mu da arziki mai kyau. Sa'an nan shĩ yanã ciyarwa daga arzikin, a asirce da bayyane. Shin sunã daidaita? Gõdiya ta tabbata ga Allah. Ã'a mafi yawansu ba su sani ba. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:76
وَضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلًا رَّجُلَيْنِ أَحَدُهُمَآ أَبْكَمُ لَا يَقْدِرُ عَلَىٰ شَىْءٍ وَهُوَ كَلٌّ عَلَىٰ مَوْلَىٰهُ أَيْنَمَا يُوَجِّههُّ لَا يَأْتِ بِخَيْرٍ ۖ هَلْ يَسْتَوِى هُوَ وَمَن يَأْمُرُ بِٱلْعَدْلِ ۙ وَهُوَ عَلَىٰ صِرَٰطٍ مُّسْتَقِيمٍ
16:76
Kuma Allah Ya buga wani misãli, maza biyu, ɗayansu bẽbe ne, ba ya iya sãmun ikon yin kõme, kuma shi nauyi ne a kan mai mallakarsa, inda duk ya fuskantar da shi, bã ya zuwa da wani alhẽri. Shin, yanã daidaita, shi da (namiji na biyu) wanda yake umurni da a yi ãdalci kuma yanã a kan tafarki madaidaici? - Abubakar Gumi (Hausa)
16:77
وَلِلَّهِ غَيْبُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۚ وَمَآ أَمْرُ ٱلسَّاعَةِ إِلَّا كَلَمْحِ ٱلْبَصَرِ أَوْ هُوَ أَقْرَبُ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ قَدِيرٌ
16:77
Kuma ga Allah gaibin sammai da ƙasa yake, kuma al'amarin Sã'a bai zama ba fãce kamar walƙãwar gani, kõ kuwa shĩ ne mafi kusa! Lalle Allah a kan dukan kõme Mai ikon yi ne. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:78
وَٱللَّهُ أَخْرَجَكُم مِّنۢ بُطُونِ أُمَّهَـٰتِكُمْ لَا تَعْلَمُونَ شَيْـًٔا وَجَعَلَ لَكُمُ ٱلسَّمْعَ وَٱلْأَبْصَـٰرَ وَٱلْأَفْـِٔدَةَ ۙ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ
16:78
Kuma Allah ne Ya fitar da ku daga cikunan iyãyenku, ba da kunã sanin kõme ba, kuma Ya sanya muku ji da gannai da zukãta, tsammãninku zã ku gõde. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:79
أَلَمْ يَرَوْا۟ إِلَى ٱلطَّيْرِ مُسَخَّرَٰتٍ فِى جَوِّ ٱلسَّمَآءِ مَا يُمْسِكُهُنَّ إِلَّا ٱللَّهُ ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ
16:79
Shin ba su ga tsuntsãye ba sunã hõrarru cikin sararin sama bãbu abin da yake riƙe su fãce Allah? Lalle ne a cikin wancan haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin ĩmãni. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:80
وَٱللَّهُ جَعَلَ لَكُم مِّنۢ بُيُوتِكُمْ سَكَنًا وَجَعَلَ لَكُم مِّن جُلُودِ ٱلْأَنْعَـٰمِ بُيُوتًا تَسْتَخِفُّونَهَا يَوْمَ ظَعْنِكُمْ وَيَوْمَ إِقَامَتِكُمْ ۙ وَمِنْ أَصْوَافِهَا وَأَوْبَارِهَا وَأَشْعَارِهَآ أَثَـٰثًا وَمَتَـٰعًا إِلَىٰ حِينٍ
16:80
Kuma Allah ne Ya sanya muku daga gidajenku wurin natsuwa, kuma Ya sanya muku daga fatun dabbõbin ni'ima wasu gidãje kunã ɗaukar su da sauƙi a rãnar tafiyarku da rãnar zamanku, kuma daga sũfinsu da gãshinsu da gẽzarsu (Allah) Ya sanya muku kãyan ɗãki da na jin dãɗi zuwa ga wani lõƙaci. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:81
وَٱللَّهُ جَعَلَ لَكُم مِّمَّا خَلَقَ ظِلَـٰلًا وَجَعَلَ لَكُم مِّنَ ٱلْجِبَالِ أَكْنَـٰنًا وَجَعَلَ لَكُمْ سَرَٰبِيلَ تَقِيكُمُ ٱلْحَرَّ وَسَرَٰبِيلَ تَقِيكُم بَأْسَكُمْ ۚ كَذَٰلِكَ يُتِمُّ نِعْمَتَهُۥ عَلَيْكُمْ لَعَلَّكُمْ تُسْلِمُونَ
16:81
Kuma Allah ne Ya sanyã muku inuwa daga abin da Ya halitta, kuma Ya sanyã muku ɗãkuna daga duwãtsu, kuma Ya sanyã muku waɗansu riguna sunã tsare muku zãfi, da waɗansu rĩguna sunã tsare muku makãminku. Kamar wancan ne (Allah) Yake cika ni'imarSa a kanku, tsammãnin ku, kuna sallamawa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:82
فَإِن تَوَلَّوْا۟ فَإِنَّمَا عَلَيْكَ ٱلْبَلَـٰغُ ٱلْمُبِينُ
16:82
To, idan sun jũya, to, abin da ya wajaba a kanka, shi ne iyarwã kawai, bayyananniyã. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:83
يَعْرِفُونَ نِعْمَتَ ٱللَّهِ ثُمَّ يُنكِرُونَهَا وَأَكْثَرُهُمُ ٱلْكَـٰفِرُونَ
16:83
Suna sanin ni'imar Allah, sa'an nan kuma sunã musunta, kuma mafi yawansu kãfirai ne. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:84
وَيَوْمَ نَبْعَثُ مِن كُلِّ أُمَّةٍ شَهِيدًا ثُمَّ لَا يُؤْذَنُ لِلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَلَا هُمْ يُسْتَعْتَبُونَ
16:84
Kuma a rãnar da Muke tãyar da mai shaida daga kõwace al'umma, sa'an nan kuma bã zã a yi izni ba ga waɗanda suka kãfirta, kuma ba su zama ana nẽman kõmawarsu ba. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:85
وَإِذَا رَءَا ٱلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ ٱلْعَذَابَ فَلَا يُخَفَّفُ عَنْهُمْ وَلَا هُمْ يُنظَرُونَ
16:85
Kuma idan waɗanda suka yi zãlunci suka ga azãba, sa'an nan bã za a saukake ta daga gare su ba, kuma bã su zama anã yi musu jinkiri ba. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:86
وَإِذَا رَءَا ٱلَّذِينَ أَشْرَكُوا۟ شُرَكَآءَهُمْ قَالُوا۟ رَبَّنَا هَـٰٓؤُلَآءِ شُرَكَآؤُنَا ٱلَّذِينَ كُنَّا نَدْعُوا۟ مِن دُونِكَ ۖ فَأَلْقَوْا۟ إِلَيْهِمُ ٱلْقَوْلَ إِنَّكُمْ لَكَـٰذِبُونَ
16:86
Kuma idan waɗanda suka yi shirka suka ga abũbuwan shirkarsu sai su ce: "Yã Ubangijinmu! Waɗannan ne abũbuwanshirkarmu waɗanda muka kasance munã kira baicinKa". Sai su jẽfamagana zuwa gare su, "Lalle ne ku, haƙĩƙa, maƙaryata ne." - Abubakar Gumi (Hausa)
16:87
وَأَلْقَوْا۟ إِلَى ٱللَّهِ يَوْمَئِذٍ ٱلسَّلَمَ ۖ وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُوا۟ يَفْتَرُونَ
16:87
Kuma su shiga nẽman sulhu zuwa ga Allah a rãnar nan, kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa ya ɓace daga gare su. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:88
ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ وَصَدُّوا۟ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ زِدْنَـٰهُمْ عَذَابًا فَوْقَ ٱلْعَذَابِ بِمَا كَانُوا۟ يُفْسِدُونَ
16:88
Waɗanda suka kãfirta kuma suka kange daga hanyar, Allah, Mun ƙãra musu wata azãba bisa ga azãbar, sabõda abin da suka kasance sunã yi na fasãdi. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:89
وَيَوْمَ نَبْعَثُ فِى كُلِّ أُمَّةٍ شَهِيدًا عَلَيْهِم مِّنْ أَنفُسِهِمْ ۖ وَجِئْنَا بِكَ شَهِيدًا عَلَىٰ هَـٰٓؤُلَآءِ ۚ وَنَزَّلْنَا عَلَيْكَ ٱلْكِتَـٰبَ تِبْيَـٰنًا لِّكُلِّ شَىْءٍ وَهُدًى وَرَحْمَةً وَبُشْرَىٰ لِلْمُسْلِمِينَ
16:89
Kuma a rãnar da Muke tãyar da shaidu a cikin kõwace al'umma a kansu daga kãwunansu, kuma Muka zo da kai kanã mai bãyar da shaida a kan waɗannan, kuma Mun saussaukar da Littãli a kanka dõmin yin bãyani ga dukkan kõme da shiriya da rahama da bushãra ga mãsu mĩƙa wuya (Musulmi). - Abubakar Gumi (Hausa)
16:90
۞ إِنَّ ٱللَّهَ يَأْمُرُ بِٱلْعَدْلِ وَٱلْإِحْسَـٰنِ وَإِيتَآئِ ذِى ٱلْقُرْبَىٰ وَيَنْهَىٰ عَنِ ٱلْفَحْشَآءِ وَٱلْمُنكَرِ وَٱلْبَغْىِ ۚ يَعِظُكُمْ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ
16:90
Lalle Allah nã yin umurni da ãdalci da kyautatãwa, da bai wa ma'abũcin zumunta, kuma yanã hani ga alfãsha da abin da aka ƙi da rarrabe jama'a. Yanã yi muku gargaɗi, ɗammãnin ku, kunã tunãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:91
وَأَوْفُوا۟ بِعَهْدِ ٱللَّهِ إِذَا عَـٰهَدتُّمْ وَلَا تَنقُضُوا۟ ٱلْأَيْمَـٰنَ بَعْدَ تَوْكِيدِهَا وَقَدْ جَعَلْتُمُ ٱللَّهَ عَلَيْكُمْ كَفِيلًا ۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَعْلَمُ مَا تَفْعَلُونَ
16:91
Kuma ku cika da alkãwarin Allah idan kun yi alkawari, kuma kada ku warware rantsuwõyinku a bãyan ƙarfafa su, alhãli kuma haƙĩƙa kun sanya Allah Mai lãmuncẽwa a kanku. Kuma lalle Allah ne Yake sanin abin da kuke aikatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:92
وَلَا تَكُونُوا۟ كَٱلَّتِى نَقَضَتْ غَزْلَهَا مِنۢ بَعْدِ قُوَّةٍ أَنكَـٰثًا تَتَّخِذُونَ أَيْمَـٰنَكُمْ دَخَلًۢا بَيْنَكُمْ أَن تَكُونَ أُمَّةٌ هِىَ أَرْبَىٰ مِنْ أُمَّةٍ ۚ إِنَّمَا يَبْلُوكُمُ ٱللَّهُ بِهِۦ ۚ وَلَيُبَيِّنَنَّ لَكُمْ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ مَا كُنتُمْ فِيهِ تَخْتَلِفُونَ
16:92
Kuma kada ku kasance kamar wadda ta warware zarenta a bãyan tukka, ya zama warwararku, kunã riƙon rantsuwõyinku dõmin yaudara a tsakãninku, dõmin kasancẽwar wata al'umma tãfi rĩba daga wata al'umma! Abin sani kawai Allah Yanã jarrabar ku da shi, kuma lalle ne yanã bayyana muku a Rãnar ¡iyãma, abin da kuka kasance, a cikinsa, kunã sãɓã wajũna. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:93
وَلَوْ شَآءَ ٱللَّهُ لَجَعَلَكُمْ أُمَّةً وَٰحِدَةً وَلَـٰكِن يُضِلُّ مَن يَشَآءُ وَيَهْدِى مَن يَشَآءُ ۚ وَلَتُسْـَٔلُنَّ عَمَّا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
16:93
Kuma dã Allah Ya so, haƙĩ ƙa, dã Ya sanya ku al'umma gudã, kuma Yanã ɓatar da wanda Ya so. kuma Yanã shiryar da wanda Ya so. Lalle ne anã tambayarku abin da kuka kasance kunã aikatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:94
وَلَا تَتَّخِذُوٓا۟ أَيْمَـٰنَكُمْ دَخَلًۢا بَيْنَكُمْ فَتَزِلَّ قَدَمٌۢ بَعْدَ ثُبُوتِهَا وَتَذُوقُوا۟ ٱلسُّوٓءَ بِمَا صَدَدتُّمْ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ ۖ وَلَكُمْ عَذَابٌ عَظِيمٌ
16:94
Kada ku riƙi rantsuwõyinku dõmin yaudara a tsakãninku, har ƙafa ta yi sulɓi a bãyan tabbatarta, kuma ku ɗanɗani azãba sabõda abin da kuka kange daga hanyar Allah. Kuma kunã da wata azãba mai girma. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:95
وَلَا تَشْتَرُوا۟ بِعَهْدِ ٱللَّهِ ثَمَنًا قَلِيلًا ۚ إِنَّمَا عِندَ ٱللَّهِ هُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
16:95
Kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da alkawarin Allah. Lalle ne abin da yake a wurin Allah shi ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance kunã sani. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:96
مَا عِندَكُمْ يَنفَدُ ۖ وَمَا عِندَ ٱللَّهِ بَاقٍ ۗ وَلَنَجْزِيَنَّ ٱلَّذِينَ صَبَرُوٓا۟ أَجْرَهُم بِأَحْسَنِ مَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ
16:96
Abin da yake a wurinku yanã ƙãrẽwa, kuma abin da yake a wurin Allah ne mai wanzuwã. Kuma lalle ne, Munã sãka wa waɗanda suka yi haƙuri da lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:97
مَنْ عَمِلَ صَـٰلِحًا مِّن ذَكَرٍ أَوْ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَلَنُحْيِيَنَّهُۥ حَيَوٰةً طَيِّبَةً ۖ وَلَنَجْزِيَنَّهُمْ أَجْرَهُم بِأَحْسَنِ مَا كَانُوا۟ يَعْمَلُونَ
16:97
Wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ kuwa mace, alhãli yanã mũmini, to, haƙĩƙa Munã rãyar da shi, rãyuwa mai dãɗi. Kuma haƙĩƙa Munã sãkã musu lãdarsu da mafi kyãwun abin da suka kasance sunã aikatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:98
فَإِذَا قَرَأْتَ ٱلْقُرْءَانَ فَٱسْتَعِذْ بِٱللَّهِ مِنَ ٱلشَّيْطَـٰنِ ٱلرَّجِيمِ
16:98
Sa'an nan idan ka karantã Alƙur'ãni, sai ka nẽmi tsari ga Allah daga shaiɗan jẽfaffe. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:99
إِنَّهُۥ لَيْسَ لَهُۥ سُلْطَـٰنٌ عَلَى ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَلَىٰ رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ
16:99
Lalle ne shi, bã shi da wani ƙarfi a kan waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sunã dõgara ga Ubangijinsu. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:100
إِنَّمَا سُلْطَـٰنُهُۥ عَلَى ٱلَّذِينَ يَتَوَلَّوْنَهُۥ وَٱلَّذِينَ هُم بِهِۦ مُشْرِكُونَ
16:100
Abin sani kawai ƙarfinsa yanã a kan waɗanda suke jiɓintar sa, kuma waɗanda suke sũ, game da shi, mãsu shirki ne. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:101
وَإِذَا بَدَّلْنَآ ءَايَةً مَّكَانَ ءَايَةٍ ۙ وَٱللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا يُنَزِّلُ قَالُوٓا۟ إِنَّمَآ أَنتَ مُفْتَرٍۭ ۚ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
16:101
Kuma idan Muka musanya wata ãyã a matsayin wata ãyã, kuma Allah ne Mafi sani ga abin da Yake saukarwa sai su ce: "Abin sani kawai, kai, aƙirƙiri ne." Ã'a, mafi yawansu bã swa sani. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:102
قُلْ نَزَّلَهُۥ رُوحُ ٱلْقُدُسِ مِن رَّبِّكَ بِٱلْحَقِّ لِيُثَبِّتَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَهُدًى وَبُشْرَىٰ لِلْمُسْلِمِينَ
16:102
Ka ce: "Rũhul ¡udusi ne ya sassaukar da shi, daga Ubangijinka da gaskiya, dõmin ya tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni, kuma (dõmin) shiriya da bushãra ga Musulmi." - Abubakar Gumi (Hausa)
16:103
وَلَقَدْ نَعْلَمُ أَنَّهُمْ يَقُولُونَ إِنَّمَا يُعَلِّمُهُۥ بَشَرٌ ۗ لِّسَانُ ٱلَّذِى يُلْحِدُونَ إِلَيْهِ أَعْجَمِىٌّ وَهَـٰذَا لِسَانٌ عَرَبِىٌّ مُّبِينٌ
16:103
Kuma lalle ne, haƙĩƙa Munã sanin (cẽwa) lalle ne sũ, sunã cẽwa, "Abin sani kawai wani mutum ne yake karantar da shi." Harshen wanda suke karkatai da maganar zuwa gare shi, Ba'ajame ne, kuma wannan (Alƙur'ãni) harshe ne Balãrabe bayyananne. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:104
إِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِـَٔايَـٰتِ ٱللَّهِ لَا يَهْدِيهِمُ ٱللَّهُ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
16:104
Lalle ne waɗanda bã su yin ĩmãni da ãyõyin Allah, Allahbã zai shiryar da su ba, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:105
إِنَّمَا يَفْتَرِى ٱلْكَذِبَ ٱلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِـَٔايَـٰتِ ٱللَّهِ ۖ وَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْكَـٰذِبُونَ
16:105
Abin sani kawai waɗanda bã su yin ĩmãni da ãyõyin Allah, sũ ne suke ƙirƙira ƙarya. Kuma waɗannan sũ ne maƙaryata. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:106
مَن كَفَرَ بِٱللَّهِ مِنۢ بَعْدِ إِيمَـٰنِهِۦٓ إِلَّا مَنْ أُكْرِهَ وَقَلْبُهُۥ مُطْمَئِنٌّۢ بِٱلْإِيمَـٰنِ وَلَـٰكِن مَّن شَرَحَ بِٱلْكُفْرِ صَدْرًا فَعَلَيْهِمْ غَضَبٌ مِّنَ ٱللَّهِ وَلَهُمْ عَذَابٌ عَظِيمٌ
16:106
Wanda ya kãfirta da Allah daga bãyan ĩmãninsa, fãce wanda aka tĩlasta alhãli kuwa zũciyarsa tanã natse da ĩmãni kuma wanda ya yi farin ciki da kãfirci, to, akwai fushi a kansa daga Allah, kuma sunã da wata azãba mai girma. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:107
ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمُ ٱسْتَحَبُّوا۟ ٱلْحَيَوٰةَ ٱلدُّنْيَا عَلَى ٱلْـَٔاخِرَةِ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَا يَهْدِى ٱلْقَوْمَ ٱلْكَـٰفِرِينَ
16:107
Waɗancan ne kãfirai dõmin sun fĩfĩta son dũniya a kan Lãhira, kuma lalle ne Allah bã Ya shiryar da mutãne kãfirai. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:108
أُو۟لَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ طَبَعَ ٱللَّهُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمْ وَسَمْعِهِمْ وَأَبْصَـٰرِهِمْ ۖ وَأُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْغَـٰفِلُونَ
16:108
Waɗancan ne waɗanda Allah Ya bice hasken zukãtansu da jinsu da gannansu. Kuma waɗancan sũ ne gafalallu. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:109
لَا جَرَمَ أَنَّهُمْ فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ هُمُ ٱلْخَـٰسِرُونَ
16:109
Bãbu shakka lalle ne a Lãhira sũ ne mãsu hasãra. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:110
ثُمَّ إِنَّ رَبَّكَ لِلَّذِينَ هَاجَرُوا۟ مِنۢ بَعْدِ مَا فُتِنُوا۟ ثُمَّ جَـٰهَدُوا۟ وَصَبَرُوٓا۟ إِنَّ رَبَّكَ مِنۢ بَعْدِهَا لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ
16:110
Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka yi hijirã daga bãyan an fitine su, sa'an nan kuma suka yi jihãdi, kuma suka yi haƙuri, lalle ne Ubangijinka, daga bãyanta haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:111
۞ يَوْمَ تَأْتِى كُلُّ نَفْسٍ تُجَـٰدِلُ عَن نَّفْسِهَا وَتُوَفَّىٰ كُلُّ نَفْسٍ مَّا عَمِلَتْ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ
16:111
A rãnar da kõwane rai zai je yanã jãyayyar tunkuɗẽwa daga kansa, kuma a cika wa kõwane rai (sakamakon) abin da ya aikata, kuma sũ bã zã a zãlunce su ba. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:112
وَضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلًا قَرْيَةً كَانَتْ ءَامِنَةً مُّطْمَئِنَّةً يَأْتِيهَا رِزْقُهَا رَغَدًا مِّن كُلِّ مَكَانٍ فَكَفَرَتْ بِأَنْعُمِ ٱللَّهِ فَأَذَٰقَهَا ٱللَّهُ لِبَاسَ ٱلْجُوعِ وَٱلْخَوْفِ بِمَا كَانُوا۟ يَصْنَعُونَ
16:112
Kuma Allah Ya buga misãli, wata alƙarya ta kasance amintacciyã, natsattsiyã, arzikinta yanã je mata a wadãce daga kõwane wuri sai ta kãfirta da ni'imõmin Allah, sabõda haka Allah ya ɗanɗana mata tufãfin yunwa da tsõro, sabõda abin da suka kasance sunã sanã'antãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:113
وَلَقَدْ جَآءَهُمْ رَسُولٌ مِّنْهُمْ فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَهُمُ ٱلْعَذَابُ وَهُمْ ظَـٰلِمُونَ
16:113
Kuma lalle ne haƙĩƙa wani Manzo daga gare su, ya jẽmusu, sai suka ƙaryata shi, sabõda haka azãba ta kãma su, alhãli kuwa sũ ne mãsu zãlunci. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:114
فَكُلُوا۟ مِمَّا رَزَقَكُمُ ٱللَّهُ حَلَـٰلًا طَيِّبًا وَٱشْكُرُوا۟ نِعْمَتَ ٱللَّهِ إِن كُنتُمْ إِيَّاهُ تَعْبُدُونَ
16:114
Sa'an nan ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku da shi, halas, kuma mai dãɗi, kuma ku gõde wa ni'imar Allah idan kun kasance shi kuke bautãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:115
إِنَّمَا حَرَّمَ عَلَيْكُمُ ٱلْمَيْتَةَ وَٱلدَّمَ وَلَحْمَ ٱلْخِنزِيرِ وَمَآ أُهِلَّ لِغَيْرِ ٱللَّهِ بِهِۦ ۖ فَمَنِ ٱضْطُرَّ غَيْرَ بَاغٍ وَلَا عَادٍ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
16:115
Abin sani kawai (Allah) Ya haramta muku mussai da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah game da shi. Sa'an nan wanda aka tĩlastaa kan jama'a kuma baicin mai zãlunci, to, lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:116
وَلَا تَقُولُوا۟ لِمَا تَصِفُ أَلْسِنَتُكُمُ ٱلْكَذِبَ هَـٰذَا حَلَـٰلٌ وَهَـٰذَا حَرَامٌ لِّتَفْتَرُوا۟ عَلَى ٱللَّهِ ٱلْكَذِبَ ۚ إِنَّ ٱلَّذِينَ يَفْتَرُونَ عَلَى ٱللَّهِ ٱلْكَذِبَ لَا يُفْلِحُونَ
16:116
Kuma kada ku ce, dõmin abin da harsunanku suke siffantawa da ƙarya, "Wannan halas ne, kuma wannan harãmun ne." Dõmin ku ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne, waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah bã zã su ci nasara ba. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:117
مَتَـٰعٌ قَلِيلٌ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
16:117
Jin dãɗi ne kaɗan. Kuma sunã da wata azãba mai raɗaɗi. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:118
وَعَلَى ٱلَّذِينَ هَادُوا۟ حَرَّمْنَا مَا قَصَصْنَا عَلَيْكَ مِن قَبْلُ ۖ وَمَا ظَلَمْنَـٰهُمْ وَلَـٰكِن كَانُوٓا۟ أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ
16:118
Kuma kan waɗanda suka tũba (Yãhũdu) Mun haramta abin da Muka bãyar da lãbari a gare ka daga gabãni, kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun kasance kansu suke zãlunta. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:119
ثُمَّ إِنَّ رَبَّكَ لِلَّذِينَ عَمِلُوا۟ ٱلسُّوٓءَ بِجَهَـٰلَةٍ ثُمَّ تَابُوا۟ مِنۢ بَعْدِ ذَٰلِكَ وَأَصْلَحُوٓا۟ إِنَّ رَبَّكَ مِنۢ بَعْدِهَا لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ
16:119
Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka aikata mummunan aiki da jãhilci, sa'an nan suka tũba daga bãyan wancan, kuma suka gyãra, lalle ne Ubangijinka, daga bãyanta haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:120
إِنَّ إِبْرَٰهِيمَ كَانَ أُمَّةً قَانِتًا لِّلَّهِ حَنِيفًا وَلَمْ يَكُ مِنَ ٱلْمُشْرِكِينَ
16:120
Lalle ne Ibrãhĩm ya kasance shũgaba, mai ƙasƙantar da kai ga Allah, mai karkatã zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:121
شَاكِرًا لِّأَنْعُمِهِ ۚ ٱجْتَبَىٰهُ وَهَدَىٰهُ إِلَىٰ صِرَٰطٍ مُّسْتَقِيمٍ
16:121
Mai gõdiya ga ni'imominSa (Allah), Ya zãɓe shi, kuma Ya shiryar da shi zuwa ga tafarki madaidaici. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:122
وَءَاتَيْنَـٰهُ فِى ٱلدُّنْيَا حَسَنَةً ۖ وَإِنَّهُۥ فِى ٱلْـَٔاخِرَةِ لَمِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ
16:122
Kuma Muka ba shi alhẽri a cikin dũniya, Kuma lalle shĩ, a Lãhira, yanã daga sãlihai. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:123
ثُمَّ أَوْحَيْنَآ إِلَيْكَ أَنِ ٱتَّبِعْ مِلَّةَ إِبْرَٰهِيمَ حَنِيفًا ۖ وَمَا كَانَ مِنَ ٱلْمُشْرِكِينَ
16:123
Sa'an nan kuma Muka yi wahayi zuwa gare ka (cẽwa), "Ka bi aƙĩdar Ibrahĩm, mai karkatã zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.' - Abubakar Gumi (Hausa)
16:124
إِنَّمَا جُعِلَ ٱلسَّبْتُ عَلَى ٱلَّذِينَ ٱخْتَلَفُوا۟ فِيهِ ۚ وَإِنَّ رَبَّكَ لَيَحْكُمُ بَيْنَهُمْ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ فِيمَا كَانُوا۟ فِيهِ يَخْتَلِفُونَ
16:124
Abin sani kawai, an sanya Asabar a kan waɗanda suka sãɓã wajũna a cikin sha'aninsa. Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Yanã yin hukunci a tsakaninsu a Rãnar ¡iyãma a cikin abin da suka kasance a cikinsa sunã sãɓã wa jũnã. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:125
ٱدْعُ إِلَىٰ سَبِيلِ رَبِّكَ بِٱلْحِكْمَةِ وَٱلْمَوْعِظَةِ ٱلْحَسَنَةِ ۖ وَجَـٰدِلْهُم بِٱلَّتِى هِىَ أَحْسَنُ ۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ ۖ وَهُوَ أَعْلَمُ بِٱلْمُهْتَدِينَ
16:125
Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa'azi mai kyau kuma ka yi jãyayya da su da magana wadda take mafi kyau. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMafi sani ga wanda ya ɓãce daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:126
وَإِنْ عَاقَبْتُمْ فَعَاقِبُوا۟ بِمِثْلِ مَا عُوقِبْتُم بِهِۦ ۖ وَلَئِن صَبَرْتُمْ لَهُوَ خَيْرٌ لِّلصَّـٰبِرِينَ
16:126
Kuma idan kuka sãka wa uƙũba to ku sãka wa uƙũba da misãlin abin da aka yi muku uƙũbar da shi. Kuma idan kun yi haƙuri, lalle shĩ ne mafi alhẽri ga mãsu haƙuri. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:127
وَٱصْبِرْ وَمَا صَبْرُكَ إِلَّا بِٱللَّهِ ۚ وَلَا تَحْزَنْ عَلَيْهِمْ وَلَا تَكُ فِى ضَيْقٍ مِّمَّا يَمْكُرُونَ
16:127
Kuma ka yi haƙuri, kuma haƙurinka bã zai zama ba fãce dõmin Allah, kuma kada ka yi baƙin ciki sabo da su, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke yi na mãkirci. - Abubakar Gumi (Hausa)
16:128
إِنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوا۟ وَّٱلَّذِينَ هُم مُّحْسِنُونَ
16:128
Lalle Allah Yanã tãre da waɗanda suka yi taƙawa da waɗanda suke sũ mãsu kyautatãwa ne. - Abubakar Gumi (Hausa)