Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

20 Ţāhā طه

< Previous   135 Āyah   Ta-Ha      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

20:1 طه
20:1 ¦.H. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:2 مَآ أَنزَلْنَا عَلَيْكَ ٱلْقُرْءَانَ لِتَشْقَىٰٓ
20:2 Ba Mu saukar da Alƙur'ãni a gare ka dõmin ka wahala ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:3 إِلَّا تَذْكِرَةً لِّمَن يَخْشَىٰ
20:3 Fãce dõmin tunãtarwa ga wanda ke tsõron Allah. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:4 تَنزِيلًا مِّمَّنْ خَلَقَ ٱلْأَرْضَ وَٱلسَّمَـٰوَٰتِ ٱلْعُلَى
20:4 (An saukar da shi) saukarwa daga wanda Ya halitta ƙasa da sammai maɗaukaka. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:5 ٱلرَّحْمَـٰنُ عَلَى ٱلْعَرْشِ ٱسْتَوَىٰ
20:5 Mai rahama, Ya daidaita a kan Al'arshi. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:6 لَهُۥ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا وَمَا تَحْتَ ٱلثَّرَىٰ
20:6 Abin da yake a cikin sammai nãSa ne, da abin da yake a cikin ƙasa da abin da yake a tsakãninsu da abin da ke ƙarƙashin turɓãya. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:7 وَإِن تَجْهَرْ بِٱلْقَوْلِ فَإِنَّهُۥ يَعْلَمُ ٱلسِّرَّ وَأَخْفَى
20:7 Kuma idan ka bayyana da magana, to, lalle Shi, Yanã sanin asĩri da mafi bõyuwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:8 ٱللَّهُ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ ۖ لَهُ ٱلْأَسْمَآءُ ٱلْحُسْنَىٰ
20:8 Allah bãbu abin bautãwa fãce Shi. Yanã da sunãye mafiya kyau. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:9 وَهَلْ أَتَىٰكَ حَدِيثُ مُوسَىٰٓ
20:9 Kuma shin, lãbarin Mũsã yãje maka? - Abubakar Gumi (Hausa)

20:10 إِذْ رَءَا نَارًا فَقَالَ لِأَهْلِهِ ٱمْكُثُوٓا۟ إِنِّىٓ ءَانَسْتُ نَارًا لَّعَلِّىٓ ءَاتِيكُم مِّنْهَا بِقَبَسٍ أَوْ أَجِدُ عَلَى ٱلنَّارِ هُدًى
20:10 A lõkacin da ya ga wata wuta, sai ya ce wa iyãlinsa, "Ku dãkata. Lalle ne nĩ, na tsinkãyi wata wuta tsammãnĩna in zo mukuda makãmashi daga gare ta, kõ kuwa in sãmi wata shiriya a kan wutar." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:11 فَلَمَّآ أَتَىٰهَا نُودِىَ يَـٰمُوسَىٰٓ
20:11 Sa'an nan a lõkacin da ya je mata, aka kira shi, "Ya Mũsã!" - Abubakar Gumi (Hausa)

20:12 إِنِّىٓ أَنَا۠ رَبُّكَ فَٱخْلَعْ نَعْلَيْكَ ۖ إِنَّكَ بِٱلْوَادِ ٱلْمُقَدَّسِ طُوًى
20:12 "Lalle ne, Nĩ ne Ubangijnka, sai ka ɗẽbe takalmanka Lalle ne kanã a rãfin nan abin tsarkakẽwa, ¦uwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:13 وَأَنَا ٱخْتَرْتُكَ فَٱسْتَمِعْ لِمَا يُوحَىٰٓ
20:13 "Kuma Nĩ Nã zãɓe ka. Sai ka saurãra ga abin da ake yin wahayi." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:14 إِنَّنِىٓ أَنَا ٱللَّهُ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱعْبُدْنِى وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ لِذِكْرِىٓ
20:14 "Lalle, Nĩ Ni ne Allah. Bãbu abin bautawa fãce Ni. Sai ka bauta Mini, kuma ka tsayar da salla dõmin tuna Ni." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:15 إِنَّ ٱلسَّاعَةَ ءَاتِيَةٌ أَكَادُ أُخْفِيهَا لِتُجْزَىٰ كُلُّ نَفْسٍۭ بِمَا تَسْعَىٰ
20:15 "Lalle ne Sa'a mai zuwa ce, lnã kusa da In ɓõye ta dõmin a sãka wa dukan rai da abin da yake aikatãwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:16 فَلَا يَصُدَّنَّكَ عَنْهَا مَن لَّا يُؤْمِنُ بِهَا وَٱتَّبَعَ هَوَىٰهُ فَتَرْدَىٰ
20:16 "Sabõda haka, kada wanda bã ya yin ĩmãni da ita kumaya bi son zuciyarsa, ya taushe ka daga gare ta har ka halaka." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:17 وَمَا تِلْكَ بِيَمِينِكَ يَـٰمُوسَىٰ
20:17 "Kuma wãce ce waccan ga dãmanka yã Mũsa!" - Abubakar Gumi (Hausa)

20:18 قَالَ هِىَ عَصَاىَ أَتَوَكَّؤُا۟ عَلَيْهَا وَأَهُشُّ بِهَا عَلَىٰ غَنَمِى وَلِىَ فِيهَا مَـَٔارِبُ أُخْرَىٰ
20:18 Ya ce: "Ita sandãta ce, inã dõgara a kanta, kuma inã kakkaɓar ganye da ita a kan ƙananan bisãshẽna kuma inã da waɗansu bukãtõci na dabam a gare ta." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:19 قَالَ أَلْقِهَا يَـٰمُوسَىٰ
20:19 Ya ce: "Ka yi jĩfa da ĩta, yã Mũsã!" - Abubakar Gumi (Hausa)

20:20 فَأَلْقَىٰهَا فَإِذَا هِىَ حَيَّةٌ تَسْعَىٰ
20:20 Sai ya jẽfa ta. Sai gã ta dabbar macĩjiya, tanã tafiya da gaggãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:21 قَالَ خُذْهَا وَلَا تَخَفْ ۖ سَنُعِيدُهَا سِيرَتَهَا ٱلْأُولَىٰ
20:21 Ya ce: "Ka kãma ta kuma kada ka ji tsõro. Za Mu mayar da ita ga hãlinta na farko." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:22 وَٱضْمُمْ يَدَكَ إِلَىٰ جَنَاحِكَ تَخْرُجْ بَيْضَآءَ مِنْ غَيْرِ سُوٓءٍ ءَايَةً أُخْرَىٰ
20:22 "Kuma ka haɗa hannunka zuwa ga damtsenka, ya fita yanã fari, bãbu sõfane, wata ãyã ta dabam." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:23 لِنُرِيَكَ مِنْ ءَايَـٰتِنَا ٱلْكُبْرَى
20:23 "Dõmin Mu nũna maka daga ãyõyinMu manya." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:24 ٱذْهَبْ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ
20:24 "Ka tafi zuwa ga Fĩr'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi (da girman kai)." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:25 قَالَ رَبِّ ٱشْرَحْ لِى صَدْرِى
20:25 Ya ce: "Ya Ubangiji! Ka buɗa mini, ƙirjĩna. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:26 وَيَسِّرْ لِىٓ أَمْرِى
20:26 "Kuma ka sauƙaƙe mini al'amarĩna." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:27 وَٱحْلُلْ عُقْدَةً مِّن لِّسَانِى
20:27 "Kuma Ka warware mini wani ƙulli daga harshẽna." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:28 يَفْقَهُوا۟ قَوْلِى
20:28 "Su fahimci maganãta." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:29 وَٱجْعَل لِّى وَزِيرًا مِّنْ أَهْلِى
20:29 "Kuma Ka sanya mini wani mataimaki daga mutãnena." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:30 هَـٰرُونَ أَخِى
20:30 "Hãrũna ɗan'uwana." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:31 ٱشْدُدْ بِهِۦٓ أَزْرِى
20:31 "Ka ƙarfafa halittata da shi." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:32 وَأَشْرِكْهُ فِىٓ أَمْرِى
20:32 "Kuma Ka shigar da shi a cikin al'amarina." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:33 كَىْ نُسَبِّحَكَ كَثِيرًا
20:33 "Dõmin mu tsarkake Ka da yawa." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:34 وَنَذْكُرَكَ كَثِيرًا
20:34 "Kuma mu tuna Ka da yawa." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:35 إِنَّكَ كُنتَ بِنَا بَصِيرًا
20:35 "Lalle Kai, Ka kasance Mai gani gare mu." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:36 قَالَ قَدْ أُوتِيتَ سُؤْلَكَ يَـٰمُوسَىٰ
20:36 Ya ce: "Lalle ne, an bã ka rõƙonka, yã Mũsã!" - Abubakar Gumi (Hausa)

20:37 وَلَقَدْ مَنَنَّا عَلَيْكَ مَرَّةً أُخْرَىٰٓ
20:37 "Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun yi wata baiwa gare ka a wani lõkacin na dabam." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:38 إِذْ أَوْحَيْنَآ إِلَىٰٓ أُمِّكَ مَا يُوحَىٰٓ
20:38 "A lõkacin da Muka yi wahayin abin da aka yi wahayi zuwa ga uwarka." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:39 أَنِ ٱقْذِفِيهِ فِى ٱلتَّابُوتِ فَٱقْذِفِيهِ فِى ٱلْيَمِّ فَلْيُلْقِهِ ٱلْيَمُّ بِٱلسَّاحِلِ يَأْخُذْهُ عَدُوٌّ لِّى وَعَدُوٌّ لَّهُۥ ۚ وَأَلْقَيْتُ عَلَيْكَ مَحَبَّةً مِّنِّى وَلِتُصْنَعَ عَلَىٰ عَيْنِىٓ
20:39 "Cẽwa, Ki jẽfa shi a cikin akwatin nan, sa'an nan ki jẽfa shi a cikin kõgi, sa'an nan kogin ya jefa shi a gãɓa, wani maƙiyi Nãwa kuma maƙiyi nãsa ya ɗauke shi.' Kuma Na jẽfa wani so daga gare Ni a kanka. Kuma dõmin a riƙe ka da kyau a kan ganiNa." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:40 إِذْ تَمْشِىٓ أُخْتُكَ فَتَقُولُ هَلْ أَدُلُّكُمْ عَلَىٰ مَن يَكْفُلُهُۥ ۖ فَرَجَعْنَـٰكَ إِلَىٰٓ أُمِّكَ كَىْ تَقَرَّ عَيْنُهَا وَلَا تَحْزَنَ ۚ وَقَتَلْتَ نَفْسًا فَنَجَّيْنَـٰكَ مِنَ ٱلْغَمِّ وَفَتَنَّـٰكَ فُتُونًا ۚ فَلَبِثْتَ سِنِينَ فِىٓ أَهْلِ مَدْيَنَ ثُمَّ جِئْتَ عَلَىٰ قَدَرٍ يَـٰمُوسَىٰ
20:40 "A sa'ad da 'yar'uwrka ke tafiya har ta ce, shin, in shiryar da ku ga wanda ke rẽnonsa?' Sai Muka mayar da kai zuwa ga uwarka dõmin idonta ya yi sanyi kuma bã zã ta yi baƙin ciki ba. Kuma kã kashe wani rai, sa'an nan Muka tsẽrar da kai daga baƙin ciki, kuma Muka fitine ka da waɗansu fitinõni. Sa'an nan ka zauna shẽkaru a cikin mutãnen Madyana. Sa'an nan kuma ka zo a kan wata ƙaddara, yã Mũsã! - Abubakar Gumi (Hausa)

20:41 وَٱصْطَنَعْتُكَ لِنَفْسِى
20:41 "Kuma Na zãɓe ka dõmin Kaina." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:42 ٱذْهَبْ أَنتَ وَأَخُوكَ بِـَٔايَـٰتِى وَلَا تَنِيَا فِى ذِكْرِى
20:42 "Ka tafi kai da ɗan'uwanka game da ãyõyiNa, kuma kada ku yi rauni ga ambatõNa." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:43 ٱذْهَبَآ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ
20:43 "Ku tafi kũ biyu zuwa ga Fir'auna. Lalle shĩ ya ƙẽtare haddi (ga girman kai)." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:44 فَقُولَا لَهُۥ قَوْلًا لَّيِّنًا لَّعَلَّهُۥ يَتَذَكَّرُ أَوْ يَخْشَىٰ
20:44 "Sai ku gaya masa magana mai laushi, tsammãninsa yanã tunãwa kõ kuwa ya ji tsõro." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:45 قَالَا رَبَّنَآ إِنَّنَا نَخَافُ أَن يَفْرُطَ عَلَيْنَآ أَوْ أَن يَطْغَىٰ
20:45 Su biyu suka ce: "Ya Ubangijinmu! Lalle ne munã tsõron ya yi gaggawa a kanmu, kõ ya ƙẽtare haddi." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:46 قَالَ لَا تَخَافَآ ۖ إِنَّنِى مَعَكُمَآ أَسْمَعُ وَأَرَىٰ
20:46 Ya ce: "Kada ku ji tsõro. Lalle Nĩ, Inã tãre da ku, Inaji, kuma Inã gani." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:47 فَأْتِيَاهُ فَقُولَآ إِنَّا رَسُولَا رَبِّكَ فَأَرْسِلْ مَعَنَا بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ وَلَا تُعَذِّبْهُمْ ۖ قَدْ جِئْنَـٰكَ بِـَٔايَةٍ مِّن رَّبِّكَ ۖ وَٱلسَّلَـٰمُ عَلَىٰ مَنِ ٱتَّبَعَ ٱلْهُدَىٰٓ
20:47 "Sai ku jẽ masa sa'an nan ku ce, Lalle mũ, Manzanni biyune na Ubangijinka, sai ka saki Banĩ Isrã'ĩla tãre da mu. Kuma kada ka yi musu azãba. Haƙĩƙa mun zomaka da wata ãyã daga, Ubangijinka. Kuma aminci ya tabbata ga wanda ya bi shiriya." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:48 إِنَّا قَدْ أُوحِىَ إِلَيْنَآ أَنَّ ٱلْعَذَابَ عَلَىٰ مَن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ
20:48 "Lalle mũ, haƙĩƙa, an yi wahayi zuwa gare mu, cẽwaazãba tanã a kan wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:49 قَالَ فَمَن رَّبُّكُمَا يَـٰمُوسَىٰ
20:49 Ya ce: "To, wãne ne Ubangijinku? Ya Mũsã!" - Abubakar Gumi (Hausa)

20:50 قَالَ رَبُّنَا ٱلَّذِىٓ أَعْطَىٰ كُلَّ شَىْءٍ خَلْقَهُۥ ثُمَّ هَدَىٰ
20:50 Ya ce: "Ubangijinmu Shi ne wanda Ya bai wa dukan kõme halittarsa, sa'an nan Ya shiryar." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:51 قَالَ فَمَا بَالُ ٱلْقُرُونِ ٱلْأُولَىٰ
20:51 Ya ce: "To, mẽne hãlin ƙarnõnin farko?" - Abubakar Gumi (Hausa)

20:52 قَالَ عِلْمُهَا عِندَ رَبِّى فِى كِتَـٰبٍ ۖ لَّا يَضِلُّ رَبِّى وَلَا يَنسَى
20:52 Ya ce: "Saninsu yanã a wurin Ubangijĩna, Ubangijĩna bã Ya ɓacẽwa kuma bã Ya mantuwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:53 ٱلَّذِى جَعَلَ لَكُمُ ٱلْأَرْضَ مَهْدًا وَسَلَكَ لَكُمْ فِيهَا سُبُلًا وَأَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءً فَأَخْرَجْنَا بِهِۦٓ أَزْوَٰجًا مِّن نَّبَاتٍ شَتَّىٰ
20:53 "Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma Ya shigar muku da hanyõyi a cikinta, kuma Ya saukar da ruwa daga sama." Sa'an nan game da shi Muka fitar da nau'i-nau'i daga tsirũruwa dabam-dabam. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:54 كُلُوا۟ وَٱرْعَوْا۟ أَنْعَـٰمَكُمْ ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّأُو۟لِى ٱلنُّهَىٰ
20:54 Ku ci kuma ku yi kiwon dabbõbin ni'imarku. Lalle ne, a cikin wannan akwai ãyõyi ga masu hankali. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:55 ۞ مِنْهَا خَلَقْنَـٰكُمْ وَفِيهَا نُعِيدُكُمْ وَمِنْهَا نُخْرِجُكُمْ تَارَةً أُخْرَىٰ
20:55 Daga gare ta Muka halitta ku, kuma a cikinta Muke mayar da ku, kuma daga gare ta Muke fitar da ku a wani lõkaci na dabam. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:56 وَلَقَدْ أَرَيْنَـٰهُ ءَايَـٰتِنَا كُلَّهَا فَكَذَّبَ وَأَبَىٰ
20:56 Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun nũna masa ãyõyinMu dukansu sai ya ƙaryata, kuma ya ƙiya! - Abubakar Gumi (Hausa)

20:57 قَالَ أَجِئْتَنَا لِتُخْرِجَنَا مِنْ أَرْضِنَا بِسِحْرِكَ يَـٰمُوسَىٰ
20:57 Ya ce: "Shin kã zo mana ne dõmin ka fitar da mu daga ƙasarmu game da sihirinka, yã Mũsã?" - Abubakar Gumi (Hausa)

20:58 فَلَنَأْتِيَنَّكَ بِسِحْرٍ مِّثْلِهِۦ فَٱجْعَلْ بَيْنَنَا وَبَيْنَكَ مَوْعِدًا لَّا نُخْلِفُهُۥ نَحْنُ وَلَآ أَنتَ مَكَانًا سُوًى
20:58 "To, lalle ne munã zo maka da wani sihiri irinsa. Sai ka sanya wani wa'adi a tsakãninmu da tsakãninka bã mu sãɓa masa mũ kai kuma, bã ka sãɓãwa, a wani wuri mai dãcẽwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:59 قَالَ مَوْعِدُكُمْ يَوْمُ ٱلزِّينَةِ وَأَن يُحْشَرَ ٱلنَّاسُ ضُحًى
20:59 Ya ce: "Wa'adinku shi ne rãnar ƙawa kuma a tãra mutãne da hantsi." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:60 فَتَوَلَّىٰ فِرْعَوْنُ فَجَمَعَ كَيْدَهُۥ ثُمَّ أَتَىٰ
20:60 Sai Fir'auna ya jũya, sa'an nan ya tãra mugunyar dabãrarsa, sa'an nan kuma ya zo. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:61 قَالَ لَهُم مُّوسَىٰ وَيْلَكُمْ لَا تَفْتَرُوا۟ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا فَيُسْحِتَكُم بِعَذَابٍ ۖ وَقَدْ خَابَ مَنِ ٱفْتَرَىٰ
20:61 Mũsã ya ce musu, "Kaitõnku! Kada ku ƙirƙira ƙarya ga Allah har Ya tumɓuke ku da wata azãba. Kuma wanda ya ƙirƙira ƙarya, yã tãɓe." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:62 فَتَنَـٰزَعُوٓا۟ أَمْرَهُم بَيْنَهُمْ وَأَسَرُّوا۟ ٱلنَّجْوَىٰ
20:62 Sai suka yi jãyayya ga al'amarinsu a tsakãninsu kuma suka asirta gãnawa. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:63 قَالُوٓا۟ إِنْ هَـٰذَٰنِ لَسَـٰحِرَٰنِ يُرِيدَانِ أَن يُخْرِجَاكُم مِّنْ أَرْضِكُم بِسِحْرِهِمَا وَيَذْهَبَا بِطَرِيقَتِكُمُ ٱلْمُثْلَىٰ
20:63 Suka ce: "Lalle ne waɗannan biyun, haƙĩƙa masihirta ne sunã nufin su fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinsu kuma su tafi da tabĩ'arku mafĩficiya." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:64 فَأَجْمِعُوا۟ كَيْدَكُمْ ثُمَّ ٱئْتُوا۟ صَفًّا ۚ وَقَدْ أَفْلَحَ ٱلْيَوْمَ مَنِ ٱسْتَعْلَىٰ
20:64 "Sai ku haɗa dabãrarku sa'an nan kuma ku tafi a sahu guda, kuma haƙĩƙa, wanda ya rinjãya, a yau, ya rabbanta." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:65 قَالُوا۟ يَـٰمُوسَىٰٓ إِمَّآ أَن تُلْقِىَ وَإِمَّآ أَن نَّكُونَ أَوَّلَ مَنْ أَلْقَىٰ
20:65 Suka ce: "Ya Mũsã! Imma ka jefa, ko kuma mu kasance farkon mai jẽfawa." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:66 قَالَ بَلْ أَلْقُوا۟ ۖ فَإِذَا حِبَالُهُمْ وَعِصِيُّهُمْ يُخَيَّلُ إِلَيْهِ مِن سِحْرِهِمْ أَنَّهَا تَسْعَىٰ
20:66 Ya ce: "Ã'a, ku jẽfa." Sai gã igiyoyinsu da sandunansu anã sũranta su a gare shi, daga sihirinsu, lalle sunã tafiya da sauri. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:67 فَأَوْجَسَ فِى نَفْسِهِۦ خِيفَةً مُّوسَىٰ
20:67 Sai Mũsã ya ji tsõro a cikin ransa. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:68 قُلْنَا لَا تَخَفْ إِنَّكَ أَنتَ ٱلْأَعْلَىٰ
20:68 Muka ce: "Kada ka ji tsõro. lalle kai ne mafi ɗaukaka." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:69 وَأَلْقِ مَا فِى يَمِينِكَ تَلْقَفْ مَا صَنَعُوٓا۟ ۖ إِنَّمَا صَنَعُوا۟ كَيْدُ سَـٰحِرٍ ۖ وَلَا يُفْلِحُ ٱلسَّاحِرُ حَيْثُ أَتَىٰ
20:69 "Kuma ka jẽfa abin da ke a cikin hannun dãmanka, ta cafe abin da suka aikata. Lalle ne abin da suka aikata mãkircin masihirci ne kuma masihirci bã ya cin nasara a duk inda ya je." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:70 فَأُلْقِىَ ٱلسَّحَرَةُ سُجَّدًا قَالُوٓا۟ ءَامَنَّا بِرَبِّ هَـٰرُونَ وَمُوسَىٰ
20:70 Sai aka jẽfar da masihirtan sunã mãsu sujada, suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin Hãrũna da Mũsã." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:71 قَالَ ءَامَنتُمْ لَهُۥ قَبْلَ أَنْ ءَاذَنَ لَكُمْ ۖ إِنَّهُۥ لَكَبِيرُكُمُ ٱلَّذِى عَلَّمَكُمُ ٱلسِّحْرَ ۖ فَلَأُقَطِّعَنَّ أَيْدِيَكُمْ وَأَرْجُلَكُم مِّنْ خِلَـٰفٍ وَلَأُصَلِّبَنَّكُمْ فِى جُذُوعِ ٱلنَّخْلِ وَلَتَعْلَمُنَّ أَيُّنَآ أَشَدُّ عَذَابًا وَأَبْقَىٰ
20:71 Ya ce: "Kun yi ĩmãni sabõda shi a gabãnin in yi muku izni? Lalle shĩ, haƙĩƙa, babbanku ne wanda ya sanar da ku sihirin! To, lalle ne zan kakkãtse hannayenku da ƙafãfunku a tarnaƙi kuma lalle zan tsĩre ku a cikin kututturan itãcen dabĩno, kuma lalle zã ku sani wanenmu ne mafi tsananin azãba kuma wãne ne mafi wanzuwar (azãba)." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:72 قَالُوا۟ لَن نُّؤْثِرَكَ عَلَىٰ مَا جَآءَنَا مِنَ ٱلْبَيِّنَـٰتِ وَٱلَّذِى فَطَرَنَا ۖ فَٱقْضِ مَآ أَنتَ قَاضٍ ۖ إِنَّمَا تَقْضِى هَـٰذِهِ ٱلْحَيَوٰةَ ٱلدُّنْيَآ
20:72 Suka ce: "Bã zã mu fĩfĩta ka ba faufau a kan abin da ya zo mana na hujjõji. Munã rantsuwa da wanda Ya ƙãga halittarmu sai ka hukunta abin da kake mai hukuntãwa, ai kanã ƙãre wannan rãyuwar dũniya kawai ne." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:73 إِنَّآ ءَامَنَّا بِرَبِّنَا لِيَغْفِرَ لَنَا خَطَـٰيَـٰنَا وَمَآ أَكْرَهْتَنَا عَلَيْهِ مِنَ ٱلسِّحْرِ ۗ وَٱللَّهُ خَيْرٌ وَأَبْقَىٰٓ
20:73 "Lalle mũ, mun yi ĩmãni da Ubangijinmu dõmin Ya gãfarta mana laifuffukanmu da abin da ka tĩlasta mu a kansa na sihiri. Kuma Allah ne Mafi alhẽri, kumaMafi wanzuwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:74 إِنَّهُۥ مَن يَأْتِ رَبَّهُۥ مُجْرِمًا فَإِنَّ لَهُۥ جَهَنَّمَ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحْيَىٰ
20:74 Lalle shĩ wanda ya je wa Ubangijinsa yanã mai laifi, to lalle ne yanã da Jahannama, bã ya mutuwa a cikinta kuma bã ya rãyuwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:75 وَمَن يَأْتِهِۦ مُؤْمِنًا قَدْ عَمِلَ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ لَهُمُ ٱلدَّرَجَـٰتُ ٱلْعُلَىٰ
20:75 Kuma wanda ya je Masa yanã mai ĩmãni, alhãli kuwaya aikata aikin ƙwarai to waɗannan sunã da darajõji maɗaukaka. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:76 جَنَّـٰتُ عَدْنٍ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ خَـٰلِدِينَ فِيهَا ۚ وَذَٰلِكَ جَزَآءُ مَن تَزَكَّىٰ
20:76 Gidãjen Aljannar zama kõguna na gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu. Kuma wannan ne sakamakon wanda ya tsarkaku. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:77 وَلَقَدْ أَوْحَيْنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنْ أَسْرِ بِعِبَادِى فَٱضْرِبْ لَهُمْ طَرِيقًا فِى ٱلْبَحْرِ يَبَسًا لَّا تَخَـٰفُ دَرَكًا وَلَا تَخْشَىٰ
20:77 Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa, "Ka yi tafiyar dare da bãyiNa. Sa'an nan ka dõka musu hanya a cikin tẽku tana ƙẽƙasasshiya, bã ka tsõron riskuwa, kuma bã ka fargabar nutsẽwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:78 فَأَتْبَعَهُمْ فِرْعَوْنُ بِجُنُودِهِۦ فَغَشِيَهُم مِّنَ ٱلْيَمِّ مَا غَشِيَهُمْ
20:78 Sai Fir'auna ya bi su game da rundunarsa. Sai abin da ya rufe su daga tẽku ya rufe su. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:79 وَأَضَلَّ فِرْعَوْنُ قَوْمَهُۥ وَمَا هَدَىٰ
20:79 Kuma Fir'auna ya ɓatar da mutãnensa, kuma bai shiryar (dasu) ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:80 يَـٰبَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ قَدْ أَنجَيْنَـٰكُم مِّنْ عَدُوِّكُمْ وَوَٰعَدْنَـٰكُمْ جَانِبَ ٱلطُّورِ ٱلْأَيْمَنَ وَنَزَّلْنَا عَلَيْكُمُ ٱلْمَنَّ وَٱلسَّلْوَىٰ
20:80 Yã Banĩ Isrã'ĩla! Lalle Mun tsẽrar da ku daga maƙiyinku, kuma mun yi muku wa'adi a gẽfen Dũtsen nan na dãma, kuma Mun sassaukar da darɓa da tattabaru dõminku. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:81 كُلُوا۟ مِن طَيِّبَـٰتِ مَا رَزَقْنَـٰكُمْ وَلَا تَطْغَوْا۟ فِيهِ فَيَحِلَّ عَلَيْكُمْ غَضَبِى ۖ وَمَن يَحْلِلْ عَلَيْهِ غَضَبِى فَقَدْ هَوَىٰ
20:81 Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurtã ku kuma kada ku ƙẽtare haddi a cikinsa har hushĩNa ya sauka a kanku. Kuma wanda hushĩNa ya sauka a kansa, to, lalle ne, ya fãɗi. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:82 وَإِنِّى لَغَفَّارٌ لِّمَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ صَـٰلِحًا ثُمَّ ٱهْتَدَىٰ
20:82 Kuma lalle Nĩ haƙĩƙa Mai gãfara ne ga wanda ya tũba kuma ya yi ĩmãni, kuma ya aikata aikin ƙwarai, sa'an nan kuma ya nẽmi shiryuwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:83 ۞ وَمَآ أَعْجَلَكَ عَن قَوْمِكَ يَـٰمُوسَىٰ
20:83 "Kuma mẽne ne ya gaggautar da kai ga barin mutãnenka? Yã Mũsã!" - Abubakar Gumi (Hausa)

20:84 قَالَ هُمْ أُو۟لَآءِ عَلَىٰٓ أَثَرِى وَعَجِلْتُ إِلَيْكَ رَبِّ لِتَرْضَىٰ
20:84 Ya ce: "Su ne waɗannan a kan sãwũna, kuma na yi gaggãwa zuwa gare Ka, yã Ubangiji! Dõmin Ka yarda." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:85 قَالَ فَإِنَّا قَدْ فَتَنَّا قَوْمَكَ مِنۢ بَعْدِكَ وَأَضَلَّهُمُ ٱلسَّامِرِىُّ
20:85 Ya ce: "To, lalle ne, haƙĩƙa, Mun fitini, mutãnenka daga bayãnka, kuma sãmiri ya ɓatar da su." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:86 فَرَجَعَ مُوسَىٰٓ إِلَىٰ قَوْمِهِۦ غَضْبَـٰنَ أَسِفًا ۚ قَالَ يَـٰقَوْمِ أَلَمْ يَعِدْكُمْ رَبُّكُمْ وَعْدًا حَسَنًا ۚ أَفَطَالَ عَلَيْكُمُ ٱلْعَهْدُ أَمْ أَرَدتُّمْ أَن يَحِلَّ عَلَيْكُمْ غَضَبٌ مِّن رَّبِّكُمْ فَأَخْلَفْتُم مَّوْعِدِى
20:86 Sai Mũsã ya kõma zuwa ga mutãnensa yanã mai hushi, mai baƙin ciki, ya ce: "Yã mutãnẽna! shin, Ubangijinku bai yi muku wa'adi ba, wa'adi mai kyau? Shin, lõkacin ya yi tsãwo a kanku ne, kõ kun yi nufi ne wani hushi ya sauka a kanku daga Ubangijinku, sabõda haka kuka sãɓã wa alkawarĩna?" - Abubakar Gumi (Hausa)

20:87 قَالُوا۟ مَآ أَخْلَفْنَا مَوْعِدَكَ بِمَلْكِنَا وَلَـٰكِنَّا حُمِّلْنَآ أَوْزَارًا مِّن زِينَةِ ٱلْقَوْمِ فَقَذَفْنَـٰهَا فَكَذَٰلِكَ أَلْقَى ٱلسَّامِرِىُّ
20:87 Suka ce: "Ba mu sãɓa wa alkawarinka ba da ĩkonmu kuma amma an ɗõra mana waɗansu kãya masu nauyi daga abin ƙawar mutãnen ne, sai muka jẽfar da su. Sa'an nan kamar haka ne sãmiri ya jẽfa." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:88 فَأَخْرَجَ لَهُمْ عِجْلًا جَسَدًا لَّهُۥ خُوَارٌ فَقَالُوا۟ هَـٰذَآ إِلَـٰهُكُمْ وَإِلَـٰهُ مُوسَىٰ فَنَسِىَ
20:88 "Sai ya fitar musu da wani maraƙi, jikin mutãne, yanã rũri, sa'an nan suka ce: wannan ne gunkinku kuma gunkin Mũsã, sai ya manta." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:89 أَفَلَا يَرَوْنَ أَلَّا يَرْجِعُ إِلَيْهِمْ قَوْلًا وَلَا يَمْلِكُ لَهُمْ ضَرًّا وَلَا نَفْعًا
20:89 Shin, to, bã su ganin cẽwabã ya mayar musu da magana, kuma bã ya mallakar wata cũta a gare su, kuma bã ya mallakar amfãni? - Abubakar Gumi (Hausa)

20:90 وَلَقَدْ قَالَ لَهُمْ هَـٰرُونُ مِن قَبْلُ يَـٰقَوْمِ إِنَّمَا فُتِنتُم بِهِۦ ۖ وَإِنَّ رَبَّكُمُ ٱلرَّحْمَـٰنُ فَٱتَّبِعُونِى وَأَطِيعُوٓا۟ أَمْرِى
20:90 Kuma, haƙĩƙa, Hãrũna yã ce musu daga gabãni, "Yã mutãnẽna! Lalle an fitinẽ ku da shi ne kawai. Kuma lalle Ubangijinku Mai rahama ne, sai ku bi ni, kuma ku yi ɗã'ã ga umurnĩna." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:91 قَالُوا۟ لَن نَّبْرَحَ عَلَيْهِ عَـٰكِفِينَ حَتَّىٰ يَرْجِعَ إِلَيْنَا مُوسَىٰ
20:91 Suka ce: "Ba zã mu gushe ba faufau a kansa munã mãsu lazimta, sai Mũsã ya kõmo zuwa gare mu." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:92 قَالَ يَـٰهَـٰرُونُ مَا مَنَعَكَ إِذْ رَأَيْتَهُمْ ضَلُّوٓا۟
20:92 (Mũsã) ya ce: "Yã Hãrũna! Mẽ ya hane ka, sa'ad da kagan su sun ɓace." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:93 أَلَّا تَتَّبِعَنِ ۖ أَفَعَصَيْتَ أَمْرِى
20:93 "Ba ka bĩ ni ba! Shin, to, ka sãɓã wa umurnina ne?" - Abubakar Gumi (Hausa)

20:94 قَالَ يَبْنَؤُمَّ لَا تَأْخُذْ بِلِحْيَتِى وَلَا بِرَأْسِىٓ ۖ إِنِّى خَشِيتُ أَن تَقُولَ فَرَّقْتَ بَيْنَ بَنِىٓ إِسْرَٰٓءِيلَ وَلَمْ تَرْقُبْ قَوْلِى
20:94 (Hãrũna) ya ce: "Yã ɗãn'uwãna! Kada ka yi kãmu ga gẽmũna kõ ga kaina. Lalle nĩ, nã ji tsõron ka ce: Ka rarraba a tsakãnin Banĩ Isrã'ĩla kuma ba ka tsare maganata ba." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:95 قَالَ فَمَا خَطْبُكَ يَـٰسَـٰمِرِىُّ
20:95 (Mũsã) ya ce: "Mẽne ne babban al'amarinka? Ya Sãmiri!" - Abubakar Gumi (Hausa)

20:96 قَالَ بَصُرْتُ بِمَا لَمْ يَبْصُرُوا۟ بِهِۦ فَقَبَضْتُ قَبْضَةً مِّنْ أَثَرِ ٱلرَّسُولِ فَنَبَذْتُهَا وَكَذَٰلِكَ سَوَّلَتْ لِى نَفْسِى
20:96 (Sãmiri) ya ce: "Nã ga abin da ba su gan shi ba shi, sai na yi damƙa, damƙa guda daga kufan sãwun Manzon, sa'an nan na jẽfa ta. Kuma haka dai raina ya ƙawãta mini." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:97 قَالَ فَٱذْهَبْ فَإِنَّ لَكَ فِى ٱلْحَيَوٰةِ أَن تَقُولَ لَا مِسَاسَ ۖ وَإِنَّ لَكَ مَوْعِدًا لَّن تُخْلَفَهُۥ ۖ وَٱنظُرْ إِلَىٰٓ إِلَـٰهِكَ ٱلَّذِى ظَلْتَ عَلَيْهِ عَاكِفًا ۖ لَّنُحَرِّقَنَّهُۥ ثُمَّ لَنَنسِفَنَّهُۥ فِى ٱلْيَمِّ نَسْفًا
20:97 (Mũsã) ya ce: "To, ka tafi, sabõda haka lalle ne kanã da a cikin rãyuwarka, ka ce 'Bãbu shãfa' kuma kanã da wani ma'alkawarta, bã zã a sãɓa maka gare ta ba. Kuma ka dũba zuwa ga gunkinka wanda ka yini a kansa kanã mai lazimta. Lalle ne muna ƙõne shi, sa'an nan kuma munã shẽƙe shi, a cikin tẽku, shẽƙẽwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:98 إِنَّمَآ إِلَـٰهُكُمُ ٱللَّهُ ٱلَّذِى لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ ۚ وَسِعَ كُلَّ شَىْءٍ عِلْمًا
20:98 Abin sani kawai abin bautãwarku Allah kawai ne wanda bãbu wani abin bautãwa, fãce Shi kuma Yã yalwaci dukkan kõme da ilmi. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:99 كَذَٰلِكَ نَقُصُّ عَلَيْكَ مِنْ أَنۢبَآءِ مَا قَدْ سَبَقَ ۚ وَقَدْ ءَاتَيْنَـٰكَ مِن لَّدُنَّا ذِكْرًا
20:99 Kamar wancan ne Muke lãbartãwa a gare ka, daga lãbãran abin da ya gabãta, alhãli kuwa haƙĩƙa, Mun bã ka zikiri (Alƙur'ãni) daga gunMu. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:100 مَّنْ أَعْرَضَ عَنْهُ فَإِنَّهُۥ يَحْمِلُ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ وِزْرًا
20:100 Wanda ya kau da kai daga gare shi, to, lalle shĩ, yanãɗaukar wani nauyi a Rãnar ¡iyãma. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:101 خَـٰلِدِينَ فِيهِ ۖ وَسَآءَ لَهُمْ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ حِمْلًا
20:101 Sunã madawwama a cikinsa, kuma yã mũnana ya zama abin ɗauka, a Rãnar ¡iyãma. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:102 يَوْمَ يُنفَخُ فِى ٱلصُّورِ ۚ وَنَحْشُرُ ٱلْمُجْرِمِينَ يَوْمَئِذٍ زُرْقًا
20:102 A Rãnar da ake hũrãwa a cikin ƙãho kuma Munã tãra mãsu laifi, a rãnar nan, sunã mãsu shũɗãyen idãnu. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:103 يَتَخَـٰفَتُونَ بَيْنَهُمْ إِن لَّبِثْتُمْ إِلَّا عَشْرًا
20:103 Suna ɓõye magana a tsakãninsu, (Sunã ce wa jũna) "Ba ku zauna ba (a cikin dũniya) fãce kwãna gõma." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:104 نَّحْنُ أَعْلَمُ بِمَا يَقُولُونَ إِذْ يَقُولُ أَمْثَلُهُمْ طَرِيقَةً إِن لَّبِثْتُمْ إِلَّا يَوْمًا
20:104 Mu ne mafi sani ga abin da suke faɗa a sa'ad da mafĩficinsu ga hanya ke cẽwa, "Ba ku zauna ba fãce a yini guda." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:105 وَيَسْـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلْجِبَالِ فَقُلْ يَنسِفُهَا رَبِّى نَسْفًا
20:105 Kuma sunã tambayar ka daga duwãtsu sai ka ce: "Ubangijina Yana shẽƙe su shẽƙẽwa, - Abubakar Gumi (Hausa)

20:106 فَيَذَرُهَا قَاعًا صَفْصَفًا
20:106 Sa'an nan Yanã barin (wurinsu) faƙo mai santsi. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:107 لَّا تَرَىٰ فِيهَا عِوَجًا وَلَآ أَمْتًا
20:107 "Bã ka ganin karkata a cikinsa, kuma bã ka ganin wani tudu." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:108 يَوْمَئِذٍ يَتَّبِعُونَ ٱلدَّاعِىَ لَا عِوَجَ لَهُۥ ۖ وَخَشَعَتِ ٱلْأَصْوَاتُ لِلرَّحْمَـٰنِ فَلَا تَسْمَعُ إِلَّا هَمْسًا
20:108 A rãnar nan sunã biyar mai kira, bãbu karkata a gare shi, kuma sautuka suka yi kawaici ga Mai rahama, bã ka sauraren kõme fãce sautin tafiya. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:109 يَوْمَئِذٍ لَّا تَنفَعُ ٱلشَّفَـٰعَةُ إِلَّا مَنْ أَذِنَ لَهُ ٱلرَّحْمَـٰنُ وَرَضِىَ لَهُۥ قَوْلًا
20:109 A yinin nan cẽto bã ya yin amfãni fãce wanda Mai rahama Ya yi masa izni kuma Ya yarda da shi, da magan - Abubakar Gumi (Hausa)

20:110 يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ وَلَا يُحِيطُونَ بِهِۦ عِلْمًا
20:110 Yanã sanin abin da ke a gaba gare su da abin da ke bãyansu, kuma bã su kẽwayẽwa da shi ga sani. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:111 ۞ وَعَنَتِ ٱلْوُجُوهُ لِلْحَىِّ ٱلْقَيُّومِ ۖ وَقَدْ خَابَ مَنْ حَمَلَ ظُلْمًا
20:111 Kuma fuskõki suka ƙanƙan da kai ga Rãyayye, Tsayayye, alhãli kuwa wanda ya ɗauko wani zãlunci ya tãɓe. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:112 وَمَن يَعْمَلْ مِنَ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَلَا يَخَافُ ظُلْمًا وَلَا هَضْمًا
20:112 Kuma wanda ya aikata wani abu daga ayyukan ƙwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bã ya tsõron wani zãlunci ko wata naƙasa. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:113 وَكَذَٰلِكَ أَنزَلْنَـٰهُ قُرْءَانًا عَرَبِيًّا وَصَرَّفْنَا فِيهِ مِنَ ٱلْوَعِيدِ لَعَلَّهُمْ يَتَّقُونَ أَوْ يُحْدِثُ لَهُمْ ذِكْرًا
20:113 Kuma haka Muka saukar da shi, Alƙur'ãni, yanã abin karantãwa, da Larabci kuma Muka jujjuya misãlai, a cikinsa, na tsõratarwa, tsammãninsu, sunã yin taƙawa ko ya sabbaba musu wata wa'aztuwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:114 فَتَعَـٰلَى ٱللَّهُ ٱلْمَلِكُ ٱلْحَقُّ ۗ وَلَا تَعْجَلْ بِٱلْقُرْءَانِ مِن قَبْلِ أَن يُقْضَىٰٓ إِلَيْكَ وَحْيُهُۥ ۖ وَقُل رَّبِّ زِدْنِى عِلْمًا
20:114 Sa'an nan Allah Mamallaki, Tabbatacce Yã ɗaukaka. Kuma kada ka yi gaggãwa da Alƙur'ãni a gabãnin a ƙãre wahayinsa zuwa gare ka. Kuma ka ce: "Yã Ubangiji! Ka ƙãra mini ilmi." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:115 وَلَقَدْ عَهِدْنَآ إِلَىٰٓ ءَادَمَ مِن قَبْلُ فَنَسِىَ وَلَمْ نَجِدْ لَهُۥ عَزْمًا
20:115 Kuma lalle, haƙĩƙa, Mun yi alkawari zuwa ga Ãdamu a gabãnin wannan, sai ya manta, kuma ba Mu sãmi ƙarfin zũciya a gare shiba. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:116 وَإِذْ قُلْنَا لِلْمَلَـٰٓئِكَةِ ٱسْجُدُوا۟ لِـَٔادَمَ فَسَجَدُوٓا۟ إِلَّآ إِبْلِيسَ أَبَىٰ
20:116 Kuma sa'ad da Muka ce wa malã'iku, "Ku yi sujada ga Ãdamu." Sai suka yi sujada, fãce Iblĩsa, yã ƙiya. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:117 فَقُلْنَا يَـٰٓـَٔادَمُ إِنَّ هَـٰذَا عَدُوٌّ لَّكَ وَلِزَوْجِكَ فَلَا يُخْرِجَنَّكُمَا مِنَ ٱلْجَنَّةِ فَتَشْقَىٰٓ
20:117 Sai Muka ce: "Ya Ãdamu! Lalle ne wannan maƙiyi ne gare ka da kuma ga mãtarka, sabõda haka kada ya fitar da ku daga Aljanna har ku wahala." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:118 إِنَّ لَكَ أَلَّا تَجُوعَ فِيهَا وَلَا تَعْرَىٰ
20:118 Lalle ne kã sãmu bã zã ka ji yunwa ba a cikinta, kuma bã zã ka yi tsiraici ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:119 وَأَنَّكَ لَا تَظْمَؤُا۟ فِيهَا وَلَا تَضْحَىٰ
20:119 "Lalle kai, bã zã ka ji ƙishirwa ba, kuma bã zã ka shiga hantsi ba." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:120 فَوَسْوَسَ إِلَيْهِ ٱلشَّيْطَـٰنُ قَالَ يَـٰٓـَٔادَمُ هَلْ أَدُلُّكَ عَلَىٰ شَجَرَةِ ٱلْخُلْدِ وَمُلْكٍ لَّا يَبْلَىٰ
20:120 Sai shaiɗan ya sanya waswãsi zuwa gare shi, ya ce: "Yã Ãdamu! Shin, in shiryar da kai ga itãciyar dawwama da mulki wanda bã ya ƙãrẽwa?" - Abubakar Gumi (Hausa)

20:121 فَأَكَلَا مِنْهَا فَبَدَتْ لَهُمَا سَوْءَٰتُهُمَا وَطَفِقَا يَخْصِفَانِ عَلَيْهِمَا مِن وَرَقِ ٱلْجَنَّةِ ۚ وَعَصَىٰٓ ءَادَمُ رَبَّهُۥ فَغَوَىٰ
20:121 Sai suka ci daga gare ta, sabõda haka al'aurunsu suka bayyana, kuma suka shiga sunã lulluɓãwa a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ãdamu ya sãɓã wa Ubangijinsa, sabõda haka ya ɓace. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:122 ثُمَّ ٱجْتَبَـٰهُ رَبُّهُۥ فَتَابَ عَلَيْهِ وَهَدَىٰ
20:122 Sa'an nan kuma Ubangjinsa Ya zãɓẽ shi, Ya karɓi tũba gare shi, kuma Ya shiryar (da shi). - Abubakar Gumi (Hausa)

20:123 قَالَ ٱهْبِطَا مِنْهَا جَمِيعًۢا ۖ بَعْضُكُمْ لِبَعْضٍ عَدُوٌّ ۖ فَإِمَّا يَأْتِيَنَّكُم مِّنِّى هُدًى فَمَنِ ٱتَّبَعَ هُدَاىَ فَلَا يَضِلُّ وَلَا يَشْقَىٰ
20:123 Ya ce: "Ku sauka kũ biyu daga gare ta gabã ɗaya, sãshenku yanã maƙiyi ga sãshe. To, imma dai wata shitiya ta jẽ muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiryarwãta, to, bã ya ɓacẽwa, kuma bã ya wahala." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:124 وَمَنْ أَعْرَضَ عَن ذِكْرِى فَإِنَّ لَهُۥ مَعِيشَةً ضَنكًا وَنَحْشُرُهُۥ يَوْمَ ٱلْقِيَـٰمَةِ أَعْمَىٰ
20:124 "Kuma wanda ya bijire daga ambatõNa (Alƙur'ãni) to, lalle ne rãyuwa mai ƙunci ta tabbata a gare shi, kuma Munã tãyar da shi a Rãnar ¡iyãma yanã makãho." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:125 قَالَ رَبِّ لِمَ حَشَرْتَنِىٓ أَعْمَىٰ وَقَدْ كُنتُ بَصِيرًا
20:125 Ya ce: "Ya Ubangiji! Don me Ka tãyar da ni makãho alhãli kuwa nã kasance mai gani?" - Abubakar Gumi (Hausa)

20:126 قَالَ كَذَٰلِكَ أَتَتْكَ ءَايَـٰتُنَا فَنَسِيتَهَا ۖ وَكَذَٰلِكَ ٱلْيَوْمَ تُنسَىٰ
20:126 Ya ce: "Kamar wancan ne ãyõyinMu suka jẽ maka sai ka mance su, kuma kamar hakar a yau ake mance ka." - Abubakar Gumi (Hausa)

20:127 وَكَذَٰلِكَ نَجْزِى مَنْ أَسْرَفَ وَلَمْ يُؤْمِنۢ بِـَٔايَـٰتِ رَبِّهِۦ ۚ وَلَعَذَابُ ٱلْـَٔاخِرَةِ أَشَدُّ وَأَبْقَىٰٓ
20:127 Kuma kamar haka Muke sãka wa wanda ya yawaita, kuma bai yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinsa ba. Kuma lalle ne azãbar Lãhira ce mafi tsanani, kuma mafi wanzuwa - Abubakar Gumi (Hausa)

20:128 أَفَلَمْ يَهْدِ لَهُمْ كَمْ أَهْلَكْنَا قَبْلَهُم مِّنَ ٱلْقُرُونِ يَمْشُونَ فِى مَسَـٰكِنِهِمْ ۗ إِنَّ فِى ذَٰلِكَ لَـَٔايَـٰتٍ لِّأُو۟لِى ٱلنُّهَىٰ
20:128 Shin, to, bai shiryar da su ba cẽwa da yawa Muka halakarda (kãfirai) daga ƙarnuka, a gabãninsu, sunã tafiya a cikin masaukansu? Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu hankula. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:129 وَلَوْلَا كَلِمَةٌ سَبَقَتْ مِن رَّبِّكَ لَكَانَ لِزَامًا وَأَجَلٌ مُّسَمًّى
20:129 Kuma bã dõmin wata kalma ba wadda ta gabãta daga Ubangijinka, da kuma ajali ambatacce haƙĩƙa, dã azãbarta kasance mai lazimta. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:130 فَٱصْبِرْ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ قَبْلَ طُلُوعِ ٱلشَّمْسِ وَقَبْلَ غُرُوبِهَا ۖ وَمِنْ ءَانَآئِ ٱلَّيْلِ فَسَبِّحْ وَأَطْرَافَ ٱلنَّهَارِ لَعَلَّكَ تَرْضَىٰ
20:130 Sai ka yi haƙuri a kan abin da suke cẽwa, kuma ka yi tasbĩhi da gõdẽ wa Ubangijinka a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta, kuma daga sã'õ'in dare sai ka yi tasbĩhi da sãsannin yini, tsammãninka zã ka sãmi yarda. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:131 وَلَا تَمُدَّنَّ عَيْنَيْكَ إِلَىٰ مَا مَتَّعْنَا بِهِۦٓ أَزْوَٰجًا مِّنْهُمْ زَهْرَةَ ٱلْحَيَوٰةِ ٱلدُّنْيَا لِنَفْتِنَهُمْ فِيهِ ۚ وَرِزْقُ رَبِّكَ خَيْرٌ وَأَبْقَىٰ
20:131 Kuma kada ka mĩƙar da idãnunka zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi da shi, nau'i-nau'i daga gare su, kamar huren rãyuwar dũniya yake, dõmin Mu fitine su a cikinsa, alhãli kuwa arzikin Ubangijinka, ne mafi alhẽri kuma mafi wanzuwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:132 وَأْمُرْ أَهْلَكَ بِٱلصَّلَوٰةِ وَٱصْطَبِرْ عَلَيْهَا ۖ لَا نَسْـَٔلُكَ رِزْقًا ۖ نَّحْنُ نَرْزُقُكَ ۗ وَٱلْعَـٰقِبَةُ لِلتَّقْوَىٰ
20:132 Kuma ka umurci iyãlanka da salla, kuma ka yi haƙuri a kanta. Bã Mu tambayar ka wani arziki Mu ne Muke azurta ka. Kuma ãƙiba mai kyau tanã ga taƙawa. - Abubakar Gumi (Hausa)

20:133 وَقَالُوا۟ لَوْلَا يَأْتِينَا بِـَٔايَةٍ مِّن رَّبِّهِۦٓ ۚ أَوَلَمْ تَأْتِهِم بَيِّنَةُ مَا فِى ٱلصُّحُفِ ٱلْأُولَىٰ
20:133 Kuma suka ce: "Don me bã ya zo mana da wata ãyã daga Ubangijinsa?" Shin, kuwa hujjar abin da ke a cikin littattafan farko, ba ta jẽ musu ba? - Abubakar Gumi (Hausa)

20:134 وَلَوْ أَنَّآ أَهْلَكْنَـٰهُم بِعَذَابٍ مِّن قَبْلِهِۦ لَقَالُوا۟ رَبَّنَا لَوْلَآ أَرْسَلْتَ إِلَيْنَا رَسُولًا فَنَتَّبِعَ ءَايَـٰتِكَ مِن قَبْلِ أَن نَّذِلَّ وَنَخْزَىٰ
20:134 Kuma dã dai Mun halaka sũ da wata azãba daga gabãninsa, lalle ne dã sun ce: "Yã Ubangijinmu! Dã Kã aiko da wani Manzo zuwa gare mu har mu bibiyi ãyõyinKa daga gabãnin mu ƙasƙanta, kuma mu wulãkantu!" - Abubakar Gumi (Hausa)

20:135 قُلْ كُلٌّ مُّتَرَبِّصٌ فَتَرَبَّصُوا۟ ۖ فَسَتَعْلَمُونَ مَنْ أَصْحَـٰبُ ٱلصِّرَٰطِ ٱلسَّوِىِّ وَمَنِ ٱهْتَدَىٰ
20:135 Ka ce: "Kõwa mai tsumãye ne. Sai ku yi tsumãye. Sa'an nan zã ku san su wa ne ma'abũta tafarki madaidaici, kuma wane ne ya nẽmi shiryuwa." - Abubakar Gumi (Hausa)