Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

71 Nūĥ نُوح

< Previous   28 Āyah   Noah      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

71:1 إِنَّآ أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوْمِهِۦٓ أَنْ أَنذِرْ قَوْمَكَ مِن قَبْلِ أَن يَأْتِيَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
71:1 Lalle ne Mun aiki Nũhu zuwa ga mutãnensa, cẽwa ka yi gargaɗi ga mutãnenka gabãnin wata azãba mai raɗaɗi ta zo musu. - Abubakar Gumi (Hausa)

71:2 قَالَ يَـٰقَوْمِ إِنِّى لَكُمْ نَذِيرٌ مُّبِينٌ
71:2 Ya ce: "Ya mutãnena ni, a gare ku, mai gargaɗi ne, mai bayyanãwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

71:3 أَنِ ٱعْبُدُوا۟ ٱللَّهَ وَٱتَّقُوهُ وَأَطِيعُونِ
71:3 "Cewa ku bauta wa Allah, ku ji tsõronSa, kuma ku bĩ ni." - Abubakar Gumi (Hausa)

71:4 يَغْفِرْ لَكُم مِّن ذُنُوبِكُمْ وَيُؤَخِّرْكُمْ إِلَىٰٓ أَجَلٍ مُّسَمًّى ۚ إِنَّ أَجَلَ ٱللَّهِ إِذَا جَآءَ لَا يُؤَخَّرُ ۖ لَوْ كُنتُمْ تَعْلَمُونَ
71:4 "Allah zai gãfarta muku daga zunubanku kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajalin da aka ambata. Lalle ne ajalin Allah idan ya zo, ba za a jinkirta Shi ba, dã kun kasance masana (ga abin da nake faɗã dã, kun bar kãfirci)." - Abubakar Gumi (Hausa)

71:5 قَالَ رَبِّ إِنِّى دَعَوْتُ قَوْمِى لَيْلًا وَنَهَارًا
71:5 Nũhu) ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne, na kirãyi mutãnena, a cikin dare da yini." - Abubakar Gumi (Hausa)

71:6 فَلَمْ يَزِدْهُمْ دُعَآءِىٓ إِلَّا فِرَارًا
71:6 "To, amma kirana bai ƙãre su ba sai da, gudu (daga gare ni)." - Abubakar Gumi (Hausa)

71:7 وَإِنِّى كُلَّمَا دَعَوْتُهُمْ لِتَغْفِرَ لَهُمْ جَعَلُوٓا۟ أَصَـٰبِعَهُمْ فِىٓ ءَاذَانِهِمْ وَٱسْتَغْشَوْا۟ ثِيَابَهُمْ وَأَصَرُّوا۟ وَٱسْتَكْبَرُوا۟ ٱسْتِكْبَارًا
71:7 "Kuma lalle ne ni, kõ da yaushe na kirãye su dõmin Ka gãfarta musu, sai su sanya yatsunsu a cikin kunnuwansu, su lulluɓe da tufãfinsu, su dõge ga yin laifi. Sun yi girman kai iyãkar girman kai." - Abubakar Gumi (Hausa)

71:8 ثُمَّ إِنِّى دَعَوْتُهُمْ جِهَارًا
71:8 "Sa'an nan lalle ne ni, na kira su, a bayyane." - Abubakar Gumi (Hausa)

71:9 ثُمَّ إِنِّىٓ أَعْلَنتُ لَهُمْ وَأَسْرَرْتُ لَهُمْ إِسْرَارًا
71:9 "Sa'an nan lalle ne, na yi yẽkuwa sabõda su, kuma na gãna da su a cikin asĩri." - Abubakar Gumi (Hausa)

71:10 فَقُلْتُ ٱسْتَغْفِرُوا۟ رَبَّكُمْ إِنَّهُۥ كَانَ غَفَّارًا
71:10 "Shi na ce, 'Ku nẽmi gãfara daga Ubangijinku, lalle ne shi Ya kasance Mai gãfara ne." - Abubakar Gumi (Hausa)

71:11 يُرْسِلِ ٱلسَّمَآءَ عَلَيْكُم مِّدْرَارًا
71:11 "Ya sako (girgijen) sama a kanku da ruwa mai ɓuɓɓuga." - Abubakar Gumi (Hausa)

71:12 وَيُمْدِدْكُم بِأَمْوَٰلٍ وَبَنِينَ وَيَجْعَل لَّكُمْ جَنَّـٰتٍ وَيَجْعَل لَّكُمْ أَنْهَـٰرًا
71:12 "Kuma ya yalwata muku game da dũkiya da ɗiya, Ya sanya muku (albarka) ga gõnaki, kuma Ya sanya muku koguna." - Abubakar Gumi (Hausa)

71:13 مَّا لَكُمْ لَا تَرْجُونَ لِلَّهِ وَقَارًا
71:13 "Me ya sãme ku, bã ku fãtar sãmun natsuwa daga Allah," - Abubakar Gumi (Hausa)

71:14 وَقَدْ خَلَقَكُمْ أَطْوَارًا
71:14 "Alhãli kuwa, lalle ne, Ya halitta. ku, a cikin hãlãye?" - Abubakar Gumi (Hausa)

71:15 أَلَمْ تَرَوْا۟ كَيْفَ خَلَقَ ٱللَّهُ سَبْعَ سَمَـٰوَٰتٍ طِبَاقًا
71:15 "Ba ku ga yadda Allah Ya halitta wasu sammai bakwai ɗabaƙõƙĩ a kan jũna ba?" - Abubakar Gumi (Hausa)

71:16 وَجَعَلَ ٱلْقَمَرَ فِيهِنَّ نُورًا وَجَعَلَ ٱلشَّمْسَ سِرَاجًا
71:16 "Ya sanya watã a cikinsu, yana mai haske, Ya sanya rãnã babbar fitila?" - Abubakar Gumi (Hausa)

71:17 وَٱللَّهُ أَنۢبَتَكُم مِّنَ ٱلْأَرْضِ نَبَاتًا
71:17 "Kuma Allah Ya tsirar da ku daga ƙasa (kamar ganye) tsirarwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

71:18 ثُمَّ يُعِيدُكُمْ فِيهَا وَيُخْرِجُكُمْ إِخْرَاجًا
71:18 "Sa'an nan Ya mayar da ku a cikinta, kuma Ya fitar da ku fitarwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

71:19 وَٱللَّهُ جَعَلَ لَكُمُ ٱلْأَرْضَ بِسَاطًا
71:19 "Kuma Allah Ya sanya muku ƙasa shimfidaɗɗiya." - Abubakar Gumi (Hausa)

71:20 لِّتَسْلُكُوا۟ مِنْهَا سُبُلًا فِجَاجًا
71:20 "Dõmin ku shiga a cikinta, hanyõyi mãsu fãɗi." - Abubakar Gumi (Hausa)

71:21 قَالَ نُوحٌ رَّبِّ إِنَّهُمْ عَصَوْنِى وَٱتَّبَعُوا۟ مَن لَّمْ يَزِدْهُ مَالُهُۥ وَوَلَدُهُۥٓ إِلَّا خَسَارًا
71:21 Nũhu ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne sũ sun saɓa mini sun bi wanda dukiyarsa da ɗiyansa ba su ƙãre shi da kõme ba sai da hasãra." - Abubakar Gumi (Hausa)

71:22 وَمَكَرُوا۟ مَكْرًا كُبَّارًا
71:22 "Kuma sun yi wani mãkirci, mãkirci babba." - Abubakar Gumi (Hausa)

71:23 وَقَالُوا۟ لَا تَذَرُنَّ ءَالِهَتَكُمْ وَلَا تَذَرُنَّ وَدًّا وَلَا سُوَاعًا وَلَا يَغُوثَ وَيَعُوقَ وَنَسْرًا
71:23 "Kuma suka ce: Faufau kada ku bar gumãkanku, kuma faufau, kada ku bar wadda, kuma kada ku bar suwã kuma kada ku bar Yagũsa da Ya'ũƙa da Nasra." - Abubakar Gumi (Hausa)

71:24 وَقَدْ أَضَلُّوا۟ كَثِيرًا ۖ وَلَا تَزِدِ ٱلظَّـٰلِمِينَ إِلَّا ضَلَـٰلًا
71:24 "Kuma lalle ne sun ɓatar da (mutãne) mãsu yawa, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai (kõme) sai ɓata." - Abubakar Gumi (Hausa)

71:25 مِّمَّا خَطِيٓـَٔـٰتِهِمْ أُغْرِقُوا۟ فَأُدْخِلُوا۟ نَارًا فَلَمْ يَجِدُوا۟ لَهُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ أَنصَارًا
71:25 Sabõda laifukansu na ganganci aka nutsar da su, sa'an nan aka sanya su a wuta. Saboda haka ba su sãmã wa kansu wani mataimaki wanin Allah ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

71:26 وَقَالَ نُوحٌ رَّبِّ لَا تَذَرْ عَلَى ٱلْأَرْضِ مِنَ ٱلْكَـٰفِرِينَ دَيَّارًا
71:26 Kuma Nũhu ya ce: "Ya Ublngijina! Kada Ka bari, a kan ƙasa, daga cikin kãfirai, wanda ke zama a cikin gida." - Abubakar Gumi (Hausa)

71:27 إِنَّكَ إِن تَذَرْهُمْ يُضِلُّوا۟ عِبَادَكَ وَلَا يَلِدُوٓا۟ إِلَّا فَاجِرًا كَفَّارًا
71:27 "Lalle ne, Kai idan Ka bar su, zã su ɓatar da bãyinKa, kuma bã zã su haifi kowa ba fãce fãjiri mai yawan kãfirci" - Abubakar Gumi (Hausa)

71:28 رَّبِّ ٱغْفِرْ لِى وَلِوَٰلِدَىَّ وَلِمَن دَخَلَ بَيْتِىَ مُؤْمِنًا وَلِلْمُؤْمِنِينَ وَٱلْمُؤْمِنَـٰتِ وَلَا تَزِدِ ٱلظَّـٰلِمِينَ إِلَّا تَبَارًۢا
71:28 "Ya Ubanginjina! Ka yi mini gãfara (ni) da mahaifana biyu, da wanda ya shiga gidana, yana mai ĩmãni, da mũminai maza da mũminai mãtã, kuma kada Ka ƙãrã wa azzãlumai kõme sai halaka." - Abubakar Gumi (Hausa)