Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

1 Al-Fātiĥah ٱلْفَاتِحَة

7 Āyah   The Opener      Next >  

1:1 بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1:1 Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. - Abubakar Gumi (Hausa)

1:2 ٱلْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ
1:2 Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu; - Abubakar Gumi (Hausa)

1:3 ٱلرَّحْمَـٰنِ ٱلرَّحِيمِ
1:3 Mai rahama, Mai jin ƙai; - Abubakar Gumi (Hausa)

1:4 مَـٰلِكِ يَوْمِ ٱلدِّينِ
1:4 Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako. - Abubakar Gumi (Hausa)

1:5 إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ
1:5 Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa. - Abubakar Gumi (Hausa)

1:6 ٱهْدِنَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلْمُسْتَقِيمَ
1:6 Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya. - Abubakar Gumi (Hausa)

1:7 صِرَٰطَ ٱلَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ ٱلْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلَا ٱلضَّآلِّينَ
1:7 Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba. - Abubakar Gumi (Hausa)