Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

85 Al-Burūj ٱلْبُرُوج

< Previous   22 Āyah   The Mansions of the Stars      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

85:1 وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلْبُرُوجِ
85:1 Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara. - Abubakar Gumi (Hausa)

85:2 وَٱلْيَوْمِ ٱلْمَوْعُودِ
85:2 Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa, - Abubakar Gumi (Hausa)

85:3 وَشَاهِدٍ وَمَشْهُودٍ
85:3 Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta a cikinsa - Abubakar Gumi (Hausa)

85:4 قُتِلَ أَصْحَـٰبُ ٱلْأُخْدُودِ
85:4 An la'ani mutãnen rãmi. - Abubakar Gumi (Hausa)

85:5 ٱلنَّارِ ذَاتِ ٱلْوَقُودِ
85:5 Wato wuta wadda aka hura. - Abubakar Gumi (Hausa)

85:6 إِذْ هُمْ عَلَيْهَا قُعُودٌ
85:6 A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune. - Abubakar Gumi (Hausa)

85:7 وَهُمْ عَلَىٰ مَا يَفْعَلُونَ بِٱلْمُؤْمِنِينَ شُهُودٌ
85:7 Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce. - Abubakar Gumi (Hausa)

85:8 وَمَا نَقَمُوا۟ مِنْهُمْ إِلَّآ أَن يُؤْمِنُوا۟ بِٱللَّهِ ٱلْعَزِيزِ ٱلْحَمِيدِ
85:8 Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa. - Abubakar Gumi (Hausa)

85:9 ٱلَّذِى لَهُۥ مُلْكُ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَىْءٍ شَهِيدٌ
85:9 Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake. - Abubakar Gumi (Hausa)

85:10 إِنَّ ٱلَّذِينَ فَتَنُوا۟ ٱلْمُؤْمِنِينَ وَٱلْمُؤْمِنَـٰتِ ثُمَّ لَمْ يَتُوبُوا۟ فَلَهُمْ عَذَابُ جَهَنَّمَ وَلَهُمْ عَذَابُ ٱلْحَرِيقِ
85:10 Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara. - Abubakar Gumi (Hausa)

85:11 إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّـٰلِحَـٰتِ لَهُمْ جَنَّـٰتٌ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا ٱلْأَنْهَـٰرُ ۚ ذَٰلِكَ ٱلْفَوْزُ ٱلْكَبِيرُ
85:11 Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba. - Abubakar Gumi (Hausa)

85:12 إِنَّ بَطْشَ رَبِّكَ لَشَدِيدٌ
85:12 Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai. - Abubakar Gumi (Hausa)

85:13 إِنَّهُۥ هُوَ يُبْدِئُ وَيُعِيدُ
85:13 Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa). - Abubakar Gumi (Hausa)

85:14 وَهُوَ ٱلْغَفُورُ ٱلْوَدُودُ
85:14 Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya. - Abubakar Gumi (Hausa)

85:15 ذُو ٱلْعَرْشِ ٱلْمَجِيدُ
85:15 Mai Al'arshi mai girma - Abubakar Gumi (Hausa)

85:16 فَعَّالٌ لِّمَا يُرِيدُ
85:16 Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi. - Abubakar Gumi (Hausa)

85:17 هَلْ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلْجُنُودِ
85:17 Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka. - Abubakar Gumi (Hausa)

85:18 فِرْعَوْنَ وَثَمُودَ
85:18 Fir'auna da samũdãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

85:19 بَلِ ٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ فِى تَكْذِيبٍ
85:19 Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

85:20 وَٱللَّهُ مِن وَرَآئِهِم مُّحِيطٌۢ
85:20 Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da saninSa). - Abubakar Gumi (Hausa)

85:21 بَلْ هُوَ قُرْءَانٌ مَّجِيدٌ
85:21 Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma. - Abubakar Gumi (Hausa)

85:22 فِى لَوْحٍ مَّحْفُوظٍۭ
85:22 A cikin Allo tsararre. - Abubakar Gumi (Hausa)