Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

87 Al-'A`lá ٱلْأَعْلَىٰ

< Previous   19 Āyah   The Most High      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

87:1 سَبِّحِ ٱسْمَ رَبِّكَ ٱلْأَعْلَى
87:1 Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka. - Abubakar Gumi (Hausa)

87:2 ٱلَّذِى خَلَقَ فَسَوَّىٰ
87:2 Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar. - Abubakar Gumi (Hausa)

87:3 وَٱلَّذِى قَدَّرَ فَهَدَىٰ
87:3 Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri). - Abubakar Gumi (Hausa)

87:4 وَٱلَّذِىٓ أَخْرَجَ ٱلْمَرْعَىٰ
87:4 Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã. - Abubakar Gumi (Hausa)

87:5 فَجَعَلَهُۥ غُثَآءً أَحْوَىٰ
87:5 Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa. - Abubakar Gumi (Hausa)

87:6 سَنُقْرِئُكَ فَلَا تَنسَىٰٓ
87:6 Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

87:7 إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُ ۚ إِنَّهُۥ يَعْلَمُ ٱلْجَهْرَ وَمَا يَخْفَىٰ
87:7 Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye. - Abubakar Gumi (Hausa)

87:8 وَنُيَسِّرُكَ لِلْيُسْرَىٰ
87:8 Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi. - Abubakar Gumi (Hausa)

87:9 فَذَكِّرْ إِن نَّفَعَتِ ٱلذِّكْرَىٰ
87:9 Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni. - Abubakar Gumi (Hausa)

87:10 سَيَذَّكَّرُ مَن يَخْشَىٰ
87:10 Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna. - Abubakar Gumi (Hausa)

87:11 وَيَتَجَنَّبُهَا ٱلْأَشْقَى
87:11 Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta, - Abubakar Gumi (Hausa)

87:12 ٱلَّذِى يَصْلَى ٱلنَّارَ ٱلْكُبْرَىٰ
87:12 Wanda zai shiga wutar da tã fi girma. - Abubakar Gumi (Hausa)

87:13 ثُمَّ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحْيَىٰ
87:13 Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

87:14 قَدْ أَفْلَحَ مَن تَزَكَّىٰ
87:14 Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo. - Abubakar Gumi (Hausa)

87:15 وَذَكَرَ ٱسْمَ رَبِّهِۦ فَصَلَّىٰ
87:15 Kuma ya ambaci sũnan Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla. - Abubakar Gumi (Hausa)

87:16 بَلْ تُؤْثِرُونَ ٱلْحَيَوٰةَ ٱلدُّنْيَا
87:16 Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya. - Abubakar Gumi (Hausa)

87:17 وَٱلْـَٔاخِرَةُ خَيْرٌ وَأَبْقَىٰٓ
87:17 Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

87:18 إِنَّ هَـٰذَا لَفِى ٱلصُّحُفِ ٱلْأُولَىٰ
87:18 Lalle ne, wannan yanã a cikin littafan farko. - Abubakar Gumi (Hausa)

87:19 صُحُفِ إِبْرَٰهِيمَ وَمُوسَىٰ
87:19 Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã. - Abubakar Gumi (Hausa)