Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

102 At-Takāthur ٱلتَّكَاثُر

< Previous   8 Āyah   The Rivalry in world increase      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

102:1 أَلْهَىٰكُمُ ٱلتَّكَاثُرُ
102:1 Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (dagaibada mai amfaninku). - Abubakar Gumi (Hausa)

102:2 حَتَّىٰ زُرْتُمُ ٱلْمَقَابِرَ
102:2 Har kuka ziyarci kaburbura. - Abubakar Gumi (Hausa)

102:3 كَلَّا سَوْفَ تَعْلَمُونَ
102:3 A'aha! (Nan gaba) zã ku sani. - Abubakar Gumi (Hausa)

102:4 ثُمَّ كَلَّا سَوْفَ تَعْلَمُونَ
102:4 Sa'an nan, tabbas, zã ku sani. - Abubakar Gumi (Hausa)

102:5 كَلَّا لَوْ تَعْلَمُونَ عِلْمَ ٱلْيَقِينِ
102:5 Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni. - Abubakar Gumi (Hausa)

102:6 لَتَرَوُنَّ ٱلْجَحِيمَ
102:6 Lalle ne da kuna ganin Jahĩm. - Abubakar Gumi (Hausa)

102:7 ثُمَّ لَتَرَوُنَّهَا عَيْنَ ٱلْيَقِينِ
102:7 Sa'an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane. - Abubakar Gumi (Hausa)

102:8 ثُمَّ لَتُسْـَٔلُنَّ يَوْمَئِذٍ عَنِ ٱلنَّعِيمِ
102:8 Sa'an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku). - Abubakar Gumi (Hausa)