Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

86 Aţ-Ţāriq ٱلطَّارِق

< Previous   17 Āyah   The Nightcommer      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

86:1 وَٱلسَّمَآءِ وَٱلطَّارِقِ
86:1 Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare. - Abubakar Gumi (Hausa)

86:2 وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا ٱلطَّارِقُ
86:2 To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare? - Abubakar Gumi (Hausa)

86:3 ٱلنَّجْمُ ٱلثَّاقِبُ
86:3 Shi ne taurãron nan mai tsananin haske. - Abubakar Gumi (Hausa)

86:4 إِن كُلُّ نَفْسٍ لَّمَّا عَلَيْهَا حَافِظٌ
86:4 Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro. - Abubakar Gumi (Hausa)

86:5 فَلْيَنظُرِ ٱلْإِنسَـٰنُ مِمَّ خُلِقَ
86:5 To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi? - Abubakar Gumi (Hausa)

86:6 خُلِقَ مِن مَّآءٍ دَافِقٍ
86:6 An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna. - Abubakar Gumi (Hausa)

86:7 يَخْرُجُ مِنۢ بَيْنِ ٱلصُّلْبِ وَٱلتَّرَآئِبِ
86:7 Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji. - Abubakar Gumi (Hausa)

86:8 إِنَّهُۥ عَلَىٰ رَجْعِهِۦ لَقَادِرٌ
86:8 Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

86:9 يَوْمَ تُبْلَى ٱلسَّرَآئِرُ
86:9 Rãnar da ake jarrabawar asirai. - Abubakar Gumi (Hausa)

86:10 فَمَا لَهُۥ مِن قُوَّةٍ وَلَا نَاصِرٍ
86:10 Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah). - Abubakar Gumi (Hausa)

86:11 وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلرَّجْعِ
86:11 Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

86:12 وَٱلْأَرْضِ ذَاتِ ٱلصَّدْعِ
86:12 Da ƙasa ma'abũciyar tsãgẽwa, - Abubakar Gumi (Hausa)

86:13 إِنَّهُۥ لَقَوْلٌ فَصْلٌ
86:13 Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki - Abubakar Gumi (Hausa)

86:14 وَمَا هُوَ بِٱلْهَزْلِ
86:14 Kuma shĩ bã bananci bane - Abubakar Gumi (Hausa)

86:15 إِنَّهُمْ يَكِيدُونَ كَيْدًا
86:15 Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai. - Abubakar Gumi (Hausa)

86:16 وَأَكِيدُ كَيْدًا
86:16 Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi. - Abubakar Gumi (Hausa)

86:17 فَمَهِّلِ ٱلْكَـٰفِرِينَ أَمْهِلْهُمْ رُوَيْدًۢا
86:17 Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu. - Abubakar Gumi (Hausa)