Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

54 Al-Qamar ٱلْقَمَر

< Previous   55 Āyah   The Moon      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

54:1 ٱقْتَرَبَتِ ٱلسَّاعَةُ وَٱنشَقَّ ٱلْقَمَرُ
54:1 Sã'a ta yi kusa, kuma wata ya tsãge. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:2 وَإِن يَرَوْا۟ ءَايَةً يُعْرِضُوا۟ وَيَقُولُوا۟ سِحْرٌ مُّسْتَمِرٌّ
54:2 Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa!" - Abubakar Gumi (Hausa)

54:3 وَكَذَّبُوا۟ وَٱتَّبَعُوٓا۟ أَهْوَآءَهُمْ ۚ وَكُلُّ أَمْرٍ مُّسْتَقِرٌّ
54:3 Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:4 وَلَقَدْ جَآءَهُم مِّنَ ٱلْأَنۢبَآءِ مَا فِيهِ مُزْدَجَرٌ
54:4 Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:5 حِكْمَةٌۢ بَـٰلِغَةٌ ۖ فَمَا تُغْنِ ٱلنُّذُرُ
54:5 Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:6 فَتَوَلَّ عَنْهُمْ ۘ يَوْمَ يَدْعُ ٱلدَّاعِ إِلَىٰ شَىْءٍ نُّكُرٍ
54:6 Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:7 خُشَّعًا أَبْصَـٰرُهُمْ يَخْرُجُونَ مِنَ ٱلْأَجْدَاثِ كَأَنَّهُمْ جَرَادٌ مُّنتَشِرٌ
54:7 ¡asƙantattu ga idanunsu zã su fito daga kaburburansu, kamar dai sũ fãri ne waɗandasuka wãtse. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:8 مُّهْطِعِينَ إِلَى ٱلدَّاعِ ۖ يَقُولُ ٱلْكَـٰفِرُونَ هَـٰذَا يَوْمٌ عَسِرٌ
54:8 Sunã gaggãwar tafiya zuwa ga mai kiran, kãfirai na cẽwa, "Wannan yini ne mai wuya!" - Abubakar Gumi (Hausa)

54:9 ۞ كَذَّبَتْ قَبْلَهُمْ قَوْمُ نُوحٍ فَكَذَّبُوا۟ عَبْدَنَا وَقَالُوا۟ مَجْنُونٌ وَٱزْدُجِرَ
54:9 Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, sai suka ƙaryata BawanMu, kuma suka ce: "Shi mahaukaci ne." Kuma aka tsãwace shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:10 فَدَعَا رَبَّهُۥٓ أَنِّى مَغْلُوبٌ فَٱنتَصِرْ
54:10 Sabõda haka, ya kira Ubangijinsa (ya ce), "Lalle nĩ, an rinjãye ni, sai Ka yi taimako." - Abubakar Gumi (Hausa)

54:11 فَفَتَحْنَآ أَبْوَٰبَ ٱلسَّمَآءِ بِمَآءٍ مُّنْهَمِرٍ
54:11 Sai Muka bũɗe kõfõfin sama da ruwa mai zuba. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:12 وَفَجَّرْنَا ٱلْأَرْضَ عُيُونًا فَٱلْتَقَى ٱلْمَآءُ عَلَىٰٓ أَمْرٍ قَدْ قُدِرَ
54:12 Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙasã ta zama idãnun ruwa, daɗa ruwa ya haɗu a kan wani umurni da aka riga aka ƙaddara shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:13 وَحَمَلْنَـٰهُ عَلَىٰ ذَاتِ أَلْوَٰحٍ وَدُسُرٍ
54:13 Kuma Muka ɗauke Nũhu a kan (jirgi) na alluna da ƙũsõshi. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:14 تَجْرِى بِأَعْيُنِنَا جَزَآءً لِّمَن كَانَ كُفِرَ
54:14 Tanã gudãna, a kan idãnunMu, dõmin sakamako ga wanda aka yi wa kãfircin. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:15 وَلَقَد تَّرَكْنَـٰهَآ ءَايَةً فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍ
54:15 Kuma lalle, Mun bar ta ta zama ãyã. To, Shin, akwai mai tunãni - Abubakar Gumi (Hausa)

54:16 فَكَيْفَ كَانَ عَذَابِى وَنُذُرِ
54:16 To, yãyã azãbãTa take da gargaɗiNa? - Abubakar Gumi (Hausa)

54:17 وَلَقَدْ يَسَّرْنَا ٱلْقُرْءَانَ لِلذِّكْرِ فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍ
54:17 Kuma lalle ne, haƙĩkƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ãni, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

54:18 كَذَّبَتْ عَادٌ فَكَيْفَ كَانَ عَذَابِى وَنُذُرِ
54:18 Ãdãwa sun ƙaryata, to, yãya azãbãTa take, da gargaɗiNa? - Abubakar Gumi (Hausa)

54:19 إِنَّآ أَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ رِيحًا صَرْصَرًا فِى يَوْمِ نَحْسٍ مُّسْتَمِرٍّ
54:19 Lalle Mũ, Mun aika da iska mai tsananin sauti a kansu, a cikin wani yinin nahĩsa mai dõgẽwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:20 تَنزِعُ ٱلنَّاسَ كَأَنَّهُمْ أَعْجَازُ نَخْلٍ مُّنقَعِرٍ
54:20 Tanã fizgar mutãne kamar dai sũ kututturan dabĩno tumɓukakku ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:21 فَكَيْفَ كَانَ عَذَابِى وَنُذُرِ
54:21 To, yãya azãbãTa take da gargaɗiNa? - Abubakar Gumi (Hausa)

54:22 وَلَقَدْ يَسَّرْنَا ٱلْقُرْءَانَ لِلذِّكْرِ فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍ
54:22 Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

54:23 كَذَّبَتْ ثَمُودُ بِٱلنُّذُرِ
54:23 Samũdãwa sun ƙaryata game da gargaɗin. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:24 فَقَالُوٓا۟ أَبَشَرًا مِّنَّا وَٰحِدًا نَّتَّبِعُهُۥٓ إِنَّآ إِذًا لَّفِى ضَلَـٰلٍ وَسُعُرٍ
54:24 Sai suka ce: "Wani mutum daga cikinmu, shi kaɗai, wai mu bĩ shi! Lalle mũ a lõkacin, haƙĩƙa mun shiga wata ɓata da haukã. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:25 أَءُلْقِىَ ٱلذِّكْرُ عَلَيْهِ مِنۢ بَيْنِنَا بَلْ هُوَ كَذَّابٌ أَشِرٌ
54:25 "Shin, an jẽfa masa Manzancin ne, a tsakãninmu? Ã'a, shĩ dai gawurtaccen maƙaryaci ne mai girman kai!" - Abubakar Gumi (Hausa)

54:26 سَيَعْلَمُونَ غَدًا مَّنِ ٱلْكَذَّابُ ٱلْأَشِرُ
54:26 Zã su sani a gõbe, wãne ne gawurtaccen mai ƙaryar, mai girman kan? - Abubakar Gumi (Hausa)

54:27 إِنَّا مُرْسِلُوا۟ ٱلنَّاقَةِ فِتْنَةً لَّهُمْ فَٱرْتَقِبْهُمْ وَٱصْطَبِرْ
54:27 Lalle Mũ, mãsu aikãwa da rãƙumar ne, ta zame musu fitina, sai ka tsare su da kallo, kuma ka yi haƙuri. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:28 وَنَبِّئْهُمْ أَنَّ ٱلْمَآءَ قِسْمَةٌۢ بَيْنَهُمْ ۖ كُلُّ شِرْبٍ مُّحْتَضَرٌ
54:28 Kuma ka bã su lãbãri cẽwa ruwa rababbe ne a tsakãninsu (da rãƙumar), kõwane sha, mai shi yanã halartar sa. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:29 فَنَادَوْا۟ صَاحِبَهُمْ فَتَعَاطَىٰ فَعَقَرَ
54:29 Sai suka kira abokinsu, sai ya karɓa, sa'an nan ya sõke ta, - Abubakar Gumi (Hausa)

54:30 فَكَيْفَ كَانَ عَذَابِى وَنُذُرِ
54:30 To, yãya azãbaTa take da gargaɗiNa? - Abubakar Gumi (Hausa)

54:31 إِنَّآ أَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ صَيْحَةً وَٰحِدَةً فَكَانُوا۟ كَهَشِيمِ ٱلْمُحْتَظِرِ
54:31 Lalle Mũ, Mun aika tsãwa guda a kansu, sai suka kasance kamar yãyin mai shinge. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:32 وَلَقَدْ يَسَّرْنَا ٱلْقُرْءَانَ لِلذِّكْرِ فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍ
54:32 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur'ani, dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

54:33 كَذَّبَتْ قَوْمُ لُوطٍۭ بِٱلنُّذُرِ
54:33 Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata, game da gargaɗi. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:34 إِنَّآ أَرْسَلْنَا عَلَيْهِمْ حَاصِبًا إِلَّآ ءَالَ لُوطٍ ۖ نَّجَّيْنَـٰهُم بِسَحَرٍ
54:34 Lalle Mun aika iskar tsakuwa a kansu, fãce mabiyan Lũɗu, Mun tsirar da su a lõkacin asuba. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:35 نِّعْمَةً مِّنْ عِندِنَا ۚ كَذَٰلِكَ نَجْزِى مَن شَكَرَ
54:35 Sabõda wata ni'ima ta daga gare Mu. Kamar haka Muke sãka wa wanda ya gõde. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:36 وَلَقَدْ أَنذَرَهُم بَطْشَتَنَا فَتَمَارَوْا۟ بِٱلنُّذُرِ
54:36 Kuma lalle, haƙĩƙa, ya yi musu gargaɗin damƙarMu, sai suka yi musu game da gargaɗin. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:37 وَلَقَدْ رَٰوَدُوهُ عَن ضَيْفِهِۦ فَطَمَسْنَآ أَعْيُنَهُمْ فَذُوقُوا۟ عَذَابِى وَنُذُرِ
54:37 Kuma lalle haƙĩƙa, su, sun nẽme shi ta wajen bãƙinsa, sai Muka shãfe idãnunsu. "To, ku ɗanɗani azãbaTa da gargaɗĩNa." - Abubakar Gumi (Hausa)

54:38 وَلَقَدْ صَبَّحَهُم بُكْرَةً عَذَابٌ مُّسْتَقِرٌّ
54:38 Kuma lalle, haƙĩƙa, wata azãba matabbaciya tã wãye musu gari da yãƙi, tun da sãfe. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:39 فَذُوقُوا۟ عَذَابِى وَنُذُرِ
54:39 To, ku ɗanɗani azãbãTa da gargaɗĩNa. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:40 وَلَقَدْ يَسَّرْنَا ٱلْقُرْءَانَ لِلذِّكْرِ فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍ
54:40 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun sauƙaƙe Alƙur, ani dõmin tunãwa. To, shin, akwai mai tunãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

54:41 وَلَقَدْ جَآءَ ءَالَ فِرْعَوْنَ ٱلنُّذُرُ
54:41 Kuma lalle, haƙĩƙa, gargaɗin ya jẽ wa mabiyan Fir'auna. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:42 كَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا كُلِّهَا فَأَخَذْنَـٰهُمْ أَخْذَ عَزِيزٍ مُّقْتَدِرٍ
54:42 Sun ƙaryata game da ãyõyinMu, dukansu sai Muka kãma su, irin kãmun Mabuwãyi, Mai ĩkon yi. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:43 أَكُفَّارُكُمْ خَيْرٌ مِّنْ أُو۟لَـٰٓئِكُمْ أَمْ لَكُم بَرَآءَةٌ فِى ٱلزُّبُرِ
54:43 Shin, kãfiranku ne mafi alhẽri daga waɗancan, ko kuwa kunã da wata barã'a a cikin littattafai? - Abubakar Gumi (Hausa)

54:44 أَمْ يَقُولُونَ نَحْنُ جَمِيعٌ مُّنتَصِرٌ
54:44 Kõ zã su ce: "Mũ duka mãsu haɗa ƙarfi ne dõmin cin nasara?" - Abubakar Gumi (Hausa)

54:45 سَيُهْزَمُ ٱلْجَمْعُ وَيُوَلُّونَ ٱلدُّبُرَ
54:45 Zã a karya tãron, kuma su jũya bãya dõmin gudu. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:46 بَلِ ٱلسَّاعَةُ مَوْعِدُهُمْ وَٱلسَّاعَةُ أَدْهَىٰ وَأَمَرُّ
54:46 Ã'a, Sã'a ita cẽ lõkacin wa'adinsu, kuma Sã'ar tã fi tsananin masĩfa, kuma ta fiɗãci. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:47 إِنَّ ٱلْمُجْرِمِينَ فِى ضَلَـٰلٍ وَسُعُرٍ
54:47 Lalle ne, mãsu laifi sunã a cikin ɓata da hauka. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:48 يَوْمَ يُسْحَبُونَ فِى ٱلنَّارِ عَلَىٰ وُجُوهِهِمْ ذُوقُوا۟ مَسَّ سَقَرَ
54:48 Rãnar da zã a jã su a cikin wuta a kan fuskõkinsu. "Ku ɗanɗani shãfar wutar Saƙar." - Abubakar Gumi (Hausa)

54:49 إِنَّا كُلَّ شَىْءٍ خَلَقْنَـٰهُ بِقَدَرٍ
54:49 Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:50 وَمَآ أَمْرُنَآ إِلَّا وَٰحِدَةٌ كَلَمْحٍۭ بِٱلْبَصَرِ
54:50 Kuma umurninMu bai zamo ba fãce da kalma ɗaya, kamar walƙãwar ido. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:51 وَلَقَدْ أَهْلَكْنَآ أَشْيَاعَكُمْ فَهَلْ مِن مُّدَّكِرٍ
54:51 Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun halaka irin gayyarku. To, shin, akwai mai tunãni? - Abubakar Gumi (Hausa)

54:52 وَكُلُّ شَىْءٍ فَعَلُوهُ فِى ٱلزُّبُرِ
54:52 Kuma kõwane abu, da suka aikata shi, yanã a cikin littattafai. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:53 وَكُلُّ صَغِيرٍ وَكَبِيرٍ مُّسْتَطَرٌ
54:53 Kuma dukkan ƙarami da babba, rubutacce ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:54 إِنَّ ٱلْمُتَّقِينَ فِى جَنَّـٰتٍ وَنَهَرٍ
54:54 Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna da kõguna. - Abubakar Gumi (Hausa)

54:55 فِى مَقْعَدِ صِدْقٍ عِندَ مَلِيكٍ مُّقْتَدِرٍۭ
54:55 A cikin mazaunin gaskiya, wurin Mai ikon yi, Mai iya zartaswa. - Abubakar Gumi (Hausa)