Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

52 Aţ-Ţūr ٱلطُّور

< Previous   49 Āyah   The Mount      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

52:1 وَٱلطُّورِ
52:1 Inã rantsuwa da ¦ũr (Dũtsen Mũsã). - Abubakar Gumi (Hausa)

52:2 وَكِتَـٰبٍ مَّسْطُورٍ
52:2 Da wani littãfi rubũtacce. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:3 فِى رَقٍّ مَّنشُورٍ
52:3 A cikin wata takardar fãta shimfiɗaɗɗa. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:4 وَٱلْبَيْتِ ٱلْمَعْمُورِ
52:4 Da Gidan da aka rãyar da shi (da ibãda). - Abubakar Gumi (Hausa)

52:5 وَٱلسَّقْفِ ٱلْمَرْفُوعِ
52:5 Da rufin nan da aka ɗaukaka. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:6 وَٱلْبَحْرِ ٱلْمَسْجُورِ
52:6 Da tẽkun nan da aka cika (da ruwa). - Abubakar Gumi (Hausa)

52:7 إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ لَوَٰقِعٌ
52:7 Lalle, azãbar Ubangijinka, haƙĩƙa, mai aukuwa ce. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:8 مَّا لَهُۥ مِن دَافِعٍ
52:8 Bã ta da mai tunkuɗẽwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:9 يَوْمَ تَمُورُ ٱلسَّمَآءُ مَوْرًا
52:9 Rãnar da samã ke yin mõtsi tanã kai kãwo. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:10 وَتَسِيرُ ٱلْجِبَالُ سَيْرًا
52:10 Kuma duwãtsu nã tafiya sunã shũɗẽwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:11 فَوَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ
52:11 To, bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:12 ٱلَّذِينَ هُمْ فِى خَوْضٍ يَلْعَبُونَ
52:12 Waɗanda suke a cikin kududdufi sunã wãsã. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:13 يَوْمَ يُدَعُّونَ إِلَىٰ نَارِ جَهَنَّمَ دَعًّا
52:13 Rãnar da zã a tunkuɗa su zuwa wutar Jahannama, tunkuɗãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:14 هَـٰذِهِ ٱلنَّارُ ٱلَّتِى كُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ
52:14 (A ce musu): "Wannan ita ce wutar da kuka kasance kunã ƙaryatãwa game da ita." - Abubakar Gumi (Hausa)

52:15 أَفَسِحْرٌ هَـٰذَآ أَمْ أَنتُمْ لَا تُبْصِرُونَ
52:15 "To, shin wannan sihiri ne kõ kuwa kũ ne bã ku gani?" - Abubakar Gumi (Hausa)

52:16 ٱصْلَوْهَا فَٱصْبِرُوٓا۟ أَوْ لَا تَصْبِرُوا۟ سَوَآءٌ عَلَيْكُمْ ۖ إِنَّمَا تُجْزَوْنَ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
52:16 "Ku shigẽ ta. To, ku yi haƙuri ko kuma kada ku yi haƙuri, dai dai ne a kanku, kawai anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

52:17 إِنَّ ٱلْمُتَّقِينَ فِى جَنَّـٰتٍ وَنَعِيمٍ
52:17 Lalle, mãsu taƙawa, sunã a cikin gidãjen Aljanna da wata ni'ima. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:18 فَـٰكِهِينَ بِمَآ ءَاتَىٰهُمْ رَبُّهُمْ وَوَقَىٰهُمْ رَبُّهُمْ عَذَابَ ٱلْجَحِيمِ
52:18 Sunã mãsu jin dãɗi da abin da Ubangijinsu Ya ba su, kuma Ubangijinsu Ya tsãre musu azãbar Jahĩm. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:19 كُلُوا۟ وَٱشْرَبُوا۟ هَنِيٓـًٔۢا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
52:19 (A ce musu): "Ku ci, ku sha, da ni'ima, dõmin abin da kuka kasance kunã aikatãwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

52:20 مُتَّكِـِٔينَ عَلَىٰ سُرُرٍ مَّصْفُوفَةٍ ۖ وَزَوَّجْنَـٰهُم بِحُورٍ عِينٍ
52:20 Sunã kishingiɗe a kan karagu waɗanda ke cikin sahu, kuma Muka aurar da su waɗansu mãtã mãsu farin idãnu, mãsu girmansu. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:21 وَٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَٱتَّبَعَتْهُمْ ذُرِّيَّتُهُم بِإِيمَـٰنٍ أَلْحَقْنَا بِهِمْ ذُرِّيَّتَهُمْ وَمَآ أَلَتْنَـٰهُم مِّنْ عَمَلِهِم مِّن شَىْءٍ ۚ كُلُّ ٱمْرِئٍۭ بِمَا كَسَبَ رَهِينٌ
52:21 Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma zũriyarsu suka bĩ su ga ĩmãnin, Mun riskar da zũriyarsu da su, alhãli kuwa bã da Mun rage musu kõme ba daga aikinsu, kõwane mutum jingina ne ga abin da ya sana'anta. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:22 وَأَمْدَدْنَـٰهُم بِفَـٰكِهَةٍ وَلَحْمٍ مِّمَّا يَشْتَهُونَ
52:22 Kuma Muka yalwata musu 'ya'yan itãce da nãma irin wanda suke marmari. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:23 يَتَنَـٰزَعُونَ فِيهَا كَأْسًا لَّا لَغْوٌ فِيهَا وَلَا تَأْثِيمٌ
52:23 Sunã mĩƙa wa jũnansu a cikinta hinjãlan giya, wadda bãbu yãsassar magana a cikinta, kuma bãbu jin nauyin zunubi. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:24 ۞ وَيَطُوفُ عَلَيْهِمْ غِلْمَانٌ لَّهُمْ كَأَنَّهُمْ لُؤْلُؤٌ مَّكْنُونٌ
52:24 Kuma waɗansu samãri nã gẽwayãwa a kansu, kamar dai sũ lu'ulu'u ne wanda ke kulle. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:25 وَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَآءَلُونَ
52:25 Waɗansunsu suka fuskanta zuwa ga waɗansu, sunã tambayar jũna. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:26 قَالُوٓا۟ إِنَّا كُنَّا قَبْلُ فِىٓ أَهْلِنَا مُشْفِقِينَ
52:26 Suka ce: "Lalle mũ mun kasance a gabãnin wannan (a dũniya) a cikin iyãlanmu munã jin tsõro." - Abubakar Gumi (Hausa)

52:27 فَمَنَّ ٱللَّهُ عَلَيْنَا وَوَقَىٰنَا عَذَابَ ٱلسَّمُومِ
52:27 "To, Allah Yã yi mana kyautar falala, kuma Yã tsare mana azãbar iskar zãfi." - Abubakar Gumi (Hausa)

52:28 إِنَّا كُنَّا مِن قَبْلُ نَدْعُوهُ ۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلْبَرُّ ٱلرَّحِيمُ
52:28 "Lalle mũ mun kasance, a gãbanin haka, munã kiran sa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai kyautatãwa, Mai rahama." - Abubakar Gumi (Hausa)

52:29 فَذَكِّرْ فَمَآ أَنتَ بِنِعْمَتِ رَبِّكَ بِكَاهِنٍ وَلَا مَجْنُونٍ
52:29 To, ka tunãtar kai fa sabõda ni'imar Ubangjinka, bã bõka kake ba, kuma bã mahaukaci ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:30 أَمْ يَقُولُونَ شَاعِرٌ نَّتَرَبَّصُ بِهِۦ رَيْبَ ٱلْمَنُونِ
52:30 Shin zã su ce: "Mawãƙi ne, munã jiran, masĩfun mutuwa game da shĩ"? - Abubakar Gumi (Hausa)

52:31 قُلْ تَرَبَّصُوا۟ فَإِنِّى مَعَكُم مِّنَ ٱلْمُتَرَبِّصِينَ
52:31 Ka ce: "Ku yi jira, domin nĩ ma lalle inã a cikin mãsu jira tãre da ku." - Abubakar Gumi (Hausa)

52:32 أَمْ تَأْمُرُهُمْ أَحْلَـٰمُهُم بِهَـٰذَآ ۚ أَمْ هُمْ قَوْمٌ طَاغُونَ
52:32 Shin, hankulansu ne ke umarin su da wannan, kõ kuwa sũ wasu mutãne ne mãsu ƙetare haddi? - Abubakar Gumi (Hausa)

52:33 أَمْ يَقُولُونَ تَقَوَّلَهُۥ ۚ بَل لَّا يُؤْمِنُونَ
52:33 Shin, cẽwa suke yi: "Shi ne ke ƙãga faɗarsa"? Ã'a ba su dai yi ĩmãni ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:34 فَلْيَأْتُوا۟ بِحَدِيثٍ مِّثْلِهِۦٓ إِن كَانُوا۟ صَـٰدِقِينَ
52:34 Sai su zõ da wani lãbãri mai misãlinsa idan sun kasance sũmãsu gaskiya ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:35 أَمْ خُلِقُوا۟ مِنْ غَيْرِ شَىْءٍ أَمْ هُمُ ٱلْخَـٰلِقُونَ
52:35 Shin, an halitta su ne bã daga kõme ba, kõ kuwa sũ ne mãsu yin halitta? - Abubakar Gumi (Hausa)

52:36 أَمْ خَلَقُوا۟ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضَ ۚ بَل لَّا يُوقِنُونَ
52:36 Shin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ã'a ba su dai yi ĩmãnin yaƙĩni ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:37 أَمْ عِندَهُمْ خَزَآئِنُ رَبِّكَ أَمْ هُمُ ٱلْمُصَۣيْطِرُونَ
52:37 Shin, taskõkin Ubangijinka, sunã a wurinsu ne? Kõ kuwa sũ ne mãsu rinjãya? - Abubakar Gumi (Hausa)

52:38 أَمْ لَهُمْ سُلَّمٌ يَسْتَمِعُونَ فِيهِ ۖ فَلْيَأْتِ مُسْتَمِعُهُم بِسُلْطَـٰنٍ مُّبِينٍ
52:38 Shin, sunã da wani tsãni ne wanda suke (hawa sunã) saurãron (lãbãrin samã) a cikinsa? Sai mai saurarõnsu ya zo da wani dalĩli bayyananne. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:39 أَمْ لَهُ ٱلْبَنَـٰتُ وَلَكُمُ ٱلْبَنُونَ
52:39 Shin, Yanã da 'ya'ya mãtã ne kuma kũ, kunã da ɗiya maza ne? - Abubakar Gumi (Hausa)

52:40 أَمْ تَسْـَٔلُهُمْ أَجْرًا فَهُم مِّن مَّغْرَمٍ مُّثْقَلُونَ
52:40 Shin, kanã tambayar su wata ijãra ne, sabõda haka suka zama mãsu jin nauyin biyan tãrar? - Abubakar Gumi (Hausa)

52:41 أَمْ عِندَهُمُ ٱلْغَيْبُ فَهُمْ يَكْتُبُونَ
52:41 Shin, a wurinsu akwai ilmin gaibi, sabõda haka sunã rubũtãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

52:42 أَمْ يُرِيدُونَ كَيْدًا ۖ فَٱلَّذِينَ كَفَرُوا۟ هُمُ ٱلْمَكِيدُونَ
52:42 Shin, sunã nufin wani kaidi ne? To, waɗanda suka kãfirta sũ ne waɗanda ake yi wa kaidi. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:43 أَمْ لَهُمْ إِلَـٰهٌ غَيْرُ ٱللَّهِ ۚ سُبْحَـٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يُشْرِكُونَ
52:43 Shin, sunã da wani abin bautãwa ne wanda bã Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke yi na shirki! - Abubakar Gumi (Hausa)

52:44 وَإِن يَرَوْا۟ كِسْفًا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ سَاقِطًا يَقُولُوا۟ سَحَابٌ مَّرْكُومٌ
52:44 Kuma idan sun ga wani ɓaɓɓake daga samã yãnã fãɗuwa, sai su ce wani girgije ne, mai hauhawar jũna. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:45 فَذَرْهُمْ حَتَّىٰ يُلَـٰقُوا۟ يَوْمَهُمُ ٱلَّذِى فِيهِ يُصْعَقُونَ
52:45 To, ka bar su, sai sun haɗu da yinin nan da za a sũmar da su a cikinsa. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:46 يَوْمَ لَا يُغْنِى عَنْهُمْ كَيْدُهُمْ شَيْـًٔا وَلَا هُمْ يُنصَرُونَ
52:46 Rãnar da kaidinsu bã ya wadãtar masu da kõme, kuma bã a taimakon su. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:47 وَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ عَذَابًا دُونَ ذَٰلِكَ وَلَـٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ
52:47 Kuma lalle, waɗannan da suka yi zãluncin, sunã da azãba (a nan dũniya) banda waccan, kuma mafi yawansu ba su sani ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

52:48 وَٱصْبِرْ لِحُكْمِ رَبِّكَ فَإِنَّكَ بِأَعْيُنِنَا ۖ وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ حِينَ تَقُومُ
52:48 Sai ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kanã idãnunMu, kuma ka tsarkake Ubangijinka da (tasbĩhi) game da gõde Masa a lõkacin da kake tãshi tsaye (dõmin salla kõ wani abu). - Abubakar Gumi (Hausa)

52:49 وَمِنَ ٱلَّيْلِ فَسَبِّحْهُ وَإِدْبَـٰرَ ٱلنُّجُومِ
52:49 Kuma daga dare, sai ka tsarkake Shi (da tasbĩhin) dalõkacin jũyãwar taurãri. - Abubakar Gumi (Hausa)