Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

53 An-Najm ٱلنَّجْم

< Previous   62 Āyah   The Star      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

53:1 وَٱلنَّجْمِ إِذَا هَوَىٰ
53:1 Inã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:2 مَا ضَلَّ صَاحِبُكُمْ وَمَا غَوَىٰ
53:2 Ma'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:3 وَمَا يَنطِقُ عَنِ ٱلْهَوَىٰٓ
53:3 Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:4 إِنْ هُوَ إِلَّا وَحْىٌ يُوحَىٰ
53:4 (Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:5 عَلَّمَهُۥ شَدِيدُ ٱلْقُوَىٰ
53:5 (Malã'ika) mai tsananin ƙarfi ya sanar da shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:6 ذُو مِرَّةٍ فَٱسْتَوَىٰ
53:6 Ma'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:7 وَهُوَ بِٱلْأُفُقِ ٱلْأَعْلَىٰ
53:7 Alhãli kuwa yanã a sararin samã mafi aukaka. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:8 ثُمَّ دَنَا فَتَدَلَّىٰ
53:8 Sa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:9 فَكَانَ قَابَ قَوْسَيْنِ أَوْ أَدْنَىٰ
53:9 Har ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:10 فَأَوْحَىٰٓ إِلَىٰ عَبْدِهِۦ مَآ أَوْحَىٰ
53:10 Sa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa). - Abubakar Gumi (Hausa)

53:11 مَا كَذَبَ ٱلْفُؤَادُ مَا رَأَىٰٓ
53:11 Zũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:12 أَفَتُمَـٰرُونَهُۥ عَلَىٰ مَا يَرَىٰ
53:12 Shin, zã ku yi masa musu a kan abin da yake gani? - Abubakar Gumi (Hausa)

53:13 وَلَقَدْ رَءَاهُ نَزْلَةً أُخْرَىٰ
53:13 Kuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:14 عِندَ سِدْرَةِ ٱلْمُنتَهَىٰ
53:14 A wurin da magaryar tuƙẽwa take. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:15 عِندَهَا جَنَّةُ ٱلْمَأْوَىٰٓ
53:15 A inda taken, nan Aljannar makoma take. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:16 إِذْ يَغْشَى ٱلسِّدْرَةَ مَا يَغْشَىٰ
53:16 Lõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:17 مَا زَاغَ ٱلْبَصَرُ وَمَا طَغَىٰ
53:17 Ganinsa bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:18 لَقَدْ رَأَىٰ مِنْ ءَايَـٰتِ رَبِّهِ ٱلْكُبْرَىٰٓ
53:18 Lalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma daga ãyõyin Ubangijinsa. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:19 أَفَرَءَيْتُمُ ٱللَّـٰتَ وَٱلْعُزَّىٰ
53:19 Shin, kun ga Lãta da uzza? - Abubakar Gumi (Hausa)

53:20 وَمَنَوٰةَ ٱلثَّالِثَةَ ٱلْأُخْرَىٰٓ
53:20 Da (wani gunki wai shi) Manãta, na ukunsu? - Abubakar Gumi (Hausa)

53:21 أَلَكُمُ ٱلذَّكَرُ وَلَهُ ٱلْأُنثَىٰ
53:21 Ashe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ (Allah) kuma da ɗiya mace? - Abubakar Gumi (Hausa)

53:22 تِلْكَ إِذًا قِسْمَةٌ ضِيزَىٰٓ
53:22 Wannan fa ya zama rabo naƙasasshe. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:23 إِنْ هِىَ إِلَّآ أَسْمَآءٌ سَمَّيْتُمُوهَآ أَنتُمْ وَءَابَآؤُكُم مَّآ أَنزَلَ ٱللَّهُ بِهَا مِن سُلْطَـٰنٍ ۚ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَمَا تَهْوَى ٱلْأَنفُسُ ۖ وَلَقَدْ جَآءَهُم مِّن رَّبِّهِمُ ٱلْهُدَىٰٓ
53:23 Waɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kãfirai) bã su biyar kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kõma wa zaton). - Abubakar Gumi (Hausa)

53:24 أَمْ لِلْإِنسَـٰنِ مَا تَمَنَّىٰ
53:24 Ko (an fai cẽwa) mutum zai sãmi abin da yake gũri? - Abubakar Gumi (Hausa)

53:25 فَلِلَّهِ ٱلْـَٔاخِرَةُ وَٱلْأُولَىٰ
53:25 To, Lãhira da dũniya na Allah kawai ne (wanda ya nẽme su daga wani, yã yi kuskure). - Abubakar Gumi (Hausa)

53:26 ۞ وَكَم مِّن مَّلَكٍ فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ لَا تُغْنِى شَفَـٰعَتُهُمْ شَيْـًٔا إِلَّا مِنۢ بَعْدِ أَن يَأْذَنَ ٱللَّهُ لِمَن يَشَآءُ وَيَرْضَىٰٓ
53:26 Akwai malã'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bã ya wadãtar da kõme fãce bãyan Allah Yã yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:27 إِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤْمِنُونَ بِٱلْـَٔاخِرَةِ لَيُسَمُّونَ ٱلْمَلَـٰٓئِكَةَ تَسْمِيَةَ ٱلْأُنثَىٰ
53:27 Lalle waɗannan da bã su yin ĩmãni da Lãhira, haƙĩƙa sunã kiran malã'iku da sũnan mace. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:28 وَمَا لَهُم بِهِۦ مِنْ عِلْمٍ ۖ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ ۖ وَإِنَّ ٱلظَّنَّ لَا يُغْنِى مِنَ ٱلْحَقِّ شَيْـًٔا
53:28 Kuma bã su da wani ilmi game da shi, bã su bin kõme fãce zato alhãli kuwa lalle zato bã ya amfãnar da kõme daga gaskiya. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:29 فَأَعْرِضْ عَن مَّن تَوَلَّىٰ عَن ذِكْرِنَا وَلَمْ يُرِدْ إِلَّا ٱلْحَيَوٰةَ ٱلدُّنْيَا
53:29 Sabõda haka sai ka kau da kai daga wanda ya jũya bãya daga ambatonMu kuma bai yi nufin kõme ba fãce rãyuwar kusa (dũniya). - Abubakar Gumi (Hausa)

53:30 ذَٰلِكَ مَبْلَغُهُم مِّنَ ٱلْعِلْمِ ۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعْلَمُ بِمَنِ ٱهْتَدَىٰ
53:30 Wannan ita ce iyãkar abin da suke iya kai gare shi na ilmi. lalle Ubangijinka Shĩ ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga wanda ya nẽmi shiriya. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:31 وَلِلَّهِ مَا فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَمَا فِى ٱلْأَرْضِ لِيَجْزِىَ ٱلَّذِينَ أَسَـٰٓـُٔوا۟ بِمَا عَمِلُوا۟ وَيَجْزِىَ ٱلَّذِينَ أَحْسَنُوا۟ بِٱلْحُسْنَى
53:31 Kuma abin da ke cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã na Allah kawai ne, dõmin Yã sãka wa waɗanda suka mũnana da abin da suka aikata, kuma Ya sãka wa waɗanda suki kyautata da sakamakon da ya fi kyau. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:32 ٱلَّذِينَ يَجْتَنِبُونَ كَبَـٰٓئِرَ ٱلْإِثْمِ وَٱلْفَوَٰحِشَ إِلَّا ٱللَّمَمَ ۚ إِنَّ رَبَّكَ وَٰسِعُ ٱلْمَغْفِرَةِ ۚ هُوَ أَعْلَمُ بِكُمْ إِذْ أَنشَأَكُم مِّنَ ٱلْأَرْضِ وَإِذْ أَنتُمْ أَجِنَّةٌ فِى بُطُونِ أُمَّهَـٰتِكُمْ ۖ فَلَا تُزَكُّوٓا۟ أَنفُسَكُمْ ۖ هُوَ أَعْلَمُ بِمَنِ ٱتَّقَىٰٓ
53:32 Waɗanda ke nĩsantar manyan zunubai da abũbuwan alfãsha, fãce ƙanãnan laifuffuka, lalle Ubangijinka Mai yalwatattar gãfara ne, Shĩ ne Ya fi sani ga abinda ke gare ku a lõkacin da Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma a lõkacin da kuke tãyuna a cikin cikannan uwãyenku. Sabõda haka, kada ku tsarkake kanku, Shĩ ne Mafi sani ga wanda ya yi taƙawa. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:33 أَفَرَءَيْتَ ٱلَّذِى تَوَلَّىٰ
53:33 Shin, ka ga wannan da ya jũya baya? - Abubakar Gumi (Hausa)

53:34 وَأَعْطَىٰ قَلِيلًا وَأَكْدَىٰٓ
53:34 Ya yi kyauta kaɗan, kuma ya yi rowa? - Abubakar Gumi (Hausa)

53:35 أَعِندَهُۥ عِلْمُ ٱلْغَيْبِ فَهُوَ يَرَىٰٓ
53:35 Shin, akwai ilmin gaibi a wurinsa, Sabõda haka yanã ganin gaibin? - Abubakar Gumi (Hausa)

53:36 أَمْ لَمْ يُنَبَّأْ بِمَا فِى صُحُفِ مُوسَىٰ
53:36 Ko kuwa ba a ba shi lãbãri ba ga abin da yake a cikin Littafan Mũsã? - Abubakar Gumi (Hausa)

53:37 وَإِبْرَٰهِيمَ ٱلَّذِى وَفَّىٰٓ
53:37 Da Ibrãhĩm wanda ya cika alkawari? - Abubakar Gumi (Hausa)

53:38 أَلَّا تَزِرُ وَازِرَةٌ وِزْرَ أُخْرَىٰ
53:38 Cẽwa wani rai mai kãyan laifi bã ya ɗaukar kãyan laifin wani. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:39 وَأَن لَّيْسَ لِلْإِنسَـٰنِ إِلَّا مَا سَعَىٰ
53:39 Kuma mutum bã shi da kõme fãce abin da ya aikata. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:40 وَأَنَّ سَعْيَهُۥ سَوْفَ يُرَىٰ
53:40 Kuma lalle, aikinsa zã a gan shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:41 ثُمَّ يُجْزَىٰهُ ٱلْجَزَآءَ ٱلْأَوْفَىٰ
53:41 Sa'an nan a sãka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni? - Abubakar Gumi (Hausa)

53:42 وَأَنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلْمُنتَهَىٰ
53:42 Kuma lalle, makõmar zuwa Ubangijinka kawai take? - Abubakar Gumi (Hausa)

53:43 وَأَنَّهُۥ هُوَ أَضْحَكَ وَأَبْكَىٰ
53:43 Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kũka. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:44 وَأَنَّهُۥ هُوَ أَمَاتَ وَأَحْيَا
53:44 Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya kashe, kuma Ya rãyar. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:45 وَأَنَّهُۥ خَلَقَ ٱلزَّوْجَيْنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلْأُنثَىٰ
53:45 Kuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:46 مِن نُّطْفَةٍ إِذَا تُمْنَىٰ
53:46 Daga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:47 وَأَنَّ عَلَيْهِ ٱلنَّشْأَةَ ٱلْأُخْرَىٰ
53:47 Kuma a kansa ne ƙãga halitta ta biyu take. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:48 وَأَنَّهُۥ هُوَ أَغْنَىٰ وَأَقْنَىٰ
53:48 Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:49 وَأَنَّهُۥ هُوَ رَبُّ ٱلشِّعْرَىٰ
53:49 Kuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:50 وَأَنَّهُۥٓ أَهْلَكَ عَادًا ٱلْأُولَىٰ
53:50 Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:51 وَثَمُودَا۟ فَمَآ أَبْقَىٰ
53:51 Da Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:52 وَقَوْمَ نُوحٍ مِّن قَبْلُ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا۟ هُمْ أَظْلَمَ وَأَطْغَىٰ
53:52 Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi girman kai. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:53 وَٱلْمُؤْتَفِكَةَ أَهْوَىٰ
53:53 Da waɗanda aka birkice ƙasarsu, Ya kãyar da su. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:54 فَغَشَّىٰهَا مَا غَشَّىٰ
53:54 Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:55 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكَ تَتَمَارَىٰ
53:55 To, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake yin shakka? - Abubakar Gumi (Hausa)

53:56 هَـٰذَا نَذِيرٌ مِّنَ ٱلنُّذُرِ ٱلْأُولَىٰٓ
53:56 wannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:57 أَزِفَتِ ٱلْـَٔازِفَةُ
53:57 Makusanciya fa, tã yi kusa. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:58 لَيْسَ لَهَا مِن دُونِ ٱللَّهِ كَاشِفَةٌ
53:58 Bãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta. - Abubakar Gumi (Hausa)

53:59 أَفَمِنْ هَـٰذَا ٱلْحَدِيثِ تَعْجَبُونَ
53:59 Shin, kuma daga wannan lãbãri kuke mãmãki? - Abubakar Gumi (Hausa)

53:60 وَتَضْحَكُونَ وَلَا تَبْكُونَ
53:60 Kuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka? - Abubakar Gumi (Hausa)

53:61 وَأَنتُمْ سَـٰمِدُونَ
53:61 Alhãli kunã mãsu wãsã? - Abubakar Gumi (Hausa)

53:62 فَٱسْجُدُوا۟ لِلَّهِ وَٱعْبُدُوا۟ ۩
53:62 To, ku yi tawãli'u ga Allah, kuma ku bauta (masa). - Abubakar Gumi (Hausa)