Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

37 Aş-Şāffāt ٱلصَّافَّات

< Previous   182 Āyah   Those who set the Ranks      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

37:1 وَٱلصَّـٰٓفَّـٰتِ صَفًّا
37:1 Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi). - Abubakar Gumi (Hausa)

37:2 فَٱلزَّٰجِرَٰتِ زَجْرًا
37:2 Sa'an nan mãsu yin tsãwa dõmin gargaɗi. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:3 فَٱلتَّـٰلِيَـٰتِ ذِكْرًا
37:3 Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:4 إِنَّ إِلَـٰهَكُمْ لَوَٰحِدٌ
37:4 Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:5 رَّبُّ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا وَرَبُّ ٱلْمَشَـٰرِقِ
37:5 Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:6 إِنَّا زَيَّنَّا ٱلسَّمَآءَ ٱلدُّنْيَا بِزِينَةٍ ٱلْكَوَاكِبِ
37:6 Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:7 وَحِفْظًا مِّن كُلِّ شَيْطَـٰنٍ مَّارِدٍ
37:7 Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:8 لَّا يَسَّمَّعُونَ إِلَى ٱلْمَلَإِ ٱلْأَعْلَىٰ وَيُقْذَفُونَ مِن كُلِّ جَانِبٍ
37:8 Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:9 دُحُورًا ۖ وَلَهُمْ عَذَابٌ وَاصِبٌ
37:9 Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:10 إِلَّا مَنْ خَطِفَ ٱلْخَطْفَةَ فَأَتْبَعَهُۥ شِهَابٌ ثَاقِبٌ
37:10 Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:11 فَٱسْتَفْتِهِمْ أَهُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَم مَّنْ خَلَقْنَآ ۚ إِنَّا خَلَقْنَـٰهُم مِّن طِينٍ لَّازِبٍۭ
37:11 Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:12 بَلْ عَجِبْتَ وَيَسْخَرُونَ
37:12 Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:13 وَإِذَا ذُكِّرُوا۟ لَا يَذْكُرُونَ
37:13 Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:14 وَإِذَا رَأَوْا۟ ءَايَةً يَسْتَسْخِرُونَ
37:14 Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:15 وَقَالُوٓا۟ إِنْ هَـٰذَآ إِلَّا سِحْرٌ مُّبِينٌ
37:15 Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne." - Abubakar Gumi (Hausa)

37:16 أَءِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَـٰمًا أَءِنَّا لَمَبْعُوثُونَ
37:16 "Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne? - Abubakar Gumi (Hausa)

37:17 أَوَءَابَآؤُنَا ٱلْأَوَّلُونَ
37:17 "Ashe kõ da ubanninmu na farko?" - Abubakar Gumi (Hausa)

37:18 قُلْ نَعَمْ وَأَنتُمْ دَٰخِرُونَ
37:18 Ka ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu." - Abubakar Gumi (Hausa)

37:19 فَإِنَّمَا هِىَ زَجْرَةٌ وَٰحِدَةٌ فَإِذَا هُمْ يَنظُرُونَ
37:19 Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:20 وَقَالُوا۟ يَـٰوَيْلَنَا هَـٰذَا يَوْمُ ٱلدِّينِ
37:20 Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako." - Abubakar Gumi (Hausa)

37:21 هَـٰذَا يَوْمُ ٱلْفَصْلِ ٱلَّذِى كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ
37:21 Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:22 ۞ ٱحْشُرُوا۟ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوا۟ وَأَزْوَٰجَهُمْ وَمَا كَانُوا۟ يَعْبُدُونَ
37:22 Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:23 مِن دُونِ ٱللَّهِ فَٱهْدُوهُمْ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلْجَحِيمِ
37:23 Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:24 وَقِفُوهُمْ ۖ إِنَّهُم مَّسْـُٔولُونَ
37:24 Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:25 مَا لَكُمْ لَا تَنَاصَرُونَ
37:25 Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna? - Abubakar Gumi (Hausa)

37:26 بَلْ هُمُ ٱلْيَوْمَ مُسْتَسْلِمُونَ
37:26 Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:27 وَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَآءَلُونَ
37:27 Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:28 قَالُوٓا۟ إِنَّكُمْ كُنتُمْ تَأْتُونَنَا عَنِ ٱلْيَمِينِ
37:28 Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)." - Abubakar Gumi (Hausa)

37:29 قَالُوا۟ بَل لَّمْ تَكُونُوا۟ مُؤْمِنِينَ
37:29 Suka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:30 وَمَا كَانَ لَنَا عَلَيْكُم مِّن سُلْطَـٰنٍۭ ۖ بَلْ كُنتُمْ قَوْمًا طَـٰغِينَ
37:30 "Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka." - Abubakar Gumi (Hausa)

37:31 فَحَقَّ عَلَيْنَا قَوْلُ رَبِّنَآ ۖ إِنَّا لَذَآئِقُونَ
37:31 "Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne." - Abubakar Gumi (Hausa)

37:32 فَأَغْوَيْنَـٰكُمْ إِنَّا كُنَّا غَـٰوِينَ
37:32 "Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu." - Abubakar Gumi (Hausa)

37:33 فَإِنَّهُمْ يَوْمَئِذٍ فِى ٱلْعَذَابِ مُشْتَرِكُونَ
37:33 To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:34 إِنَّا كَذَٰلِكَ نَفْعَلُ بِٱلْمُجْرِمِينَ
37:34 Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:35 إِنَّهُمْ كَانُوٓا۟ إِذَا قِيلَ لَهُمْ لَآ إِلَـٰهَ إِلَّا ٱللَّهُ يَسْتَكْبِرُونَ
37:35 Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:36 وَيَقُولُونَ أَئِنَّا لَتَارِكُوٓا۟ ءَالِهَتِنَا لِشَاعِرٍ مَّجْنُونٍۭ
37:36 Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci? - Abubakar Gumi (Hausa)

37:37 بَلْ جَآءَ بِٱلْحَقِّ وَصَدَّقَ ٱلْمُرْسَلِينَ
37:37 Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:38 إِنَّكُمْ لَذَآئِقُوا۟ ٱلْعَذَابِ ٱلْأَلِيمِ
37:38 Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:39 وَمَا تُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ
37:39 Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:40 إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلْمُخْلَصِينَ
37:40 Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:41 أُو۟لَـٰٓئِكَ لَهُمْ رِزْقٌ مَّعْلُومٌ
37:41 Waɗannan sunã da abinci sananne. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:42 فَوَٰكِهُ ۖ وَهُم مُّكْرَمُونَ
37:42 'Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:43 فِى جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ
37:43 A cikin gidãjen Aljannar ni'ima. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:44 عَلَىٰ سُرُرٍ مُّتَقَـٰبِلِينَ
37:44 A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:45 يُطَافُ عَلَيْهِم بِكَأْسٍ مِّن مَّعِينٍۭ
37:45 Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:46 بَيْضَآءَ لَذَّةٍ لِّلشَّـٰرِبِينَ
37:46 Farã mai dãɗi ga mashãyan. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:47 لَا فِيهَا غَوْلٌ وَلَا هُمْ عَنْهَا يُنزَفُونَ
37:47 A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba, - Abubakar Gumi (Hausa)

37:48 وَعِندَهُمْ قَـٰصِرَٰتُ ٱلطَّرْفِ عِينٌ
37:48 Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:49 كَأَنَّهُنَّ بَيْضٌ مَّكْنُونٌ
37:49 Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:50 فَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَآءَلُونَ
37:50 Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:51 قَالَ قَآئِلٌ مِّنْهُمْ إِنِّى كَانَ لِى قَرِينٌ
37:51 Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)." - Abubakar Gumi (Hausa)

37:52 يَقُولُ أَءِنَّكَ لَمِنَ ٱلْمُصَدِّقِينَ
37:52 Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?" - Abubakar Gumi (Hausa)

37:53 أَءِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَـٰمًا أَءِنَّا لَمَدِينُونَ
37:53 "Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?" - Abubakar Gumi (Hausa)

37:54 قَالَ هَلْ أَنتُم مُّطَّلِعُونَ
37:54 (Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?" - Abubakar Gumi (Hausa)

37:55 فَٱطَّلَعَ فَرَءَاهُ فِى سَوَآءِ ٱلْجَحِيمِ
37:55 Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:56 قَالَ تَٱللَّهِ إِن كِدتَّ لَتُرْدِينِ
37:56 Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni." - Abubakar Gumi (Hausa)

37:57 وَلَوْلَا نِعْمَةُ رَبِّى لَكُنتُ مِنَ ٱلْمُحْضَرِينَ
37:57 "Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)." - Abubakar Gumi (Hausa)

37:58 أَفَمَا نَحْنُ بِمَيِّتِينَ
37:58 "Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba." - Abubakar Gumi (Hausa)

37:59 إِلَّا مَوْتَتَنَا ٱلْأُولَىٰ وَمَا نَحْنُ بِمُعَذَّبِينَ
37:59 "Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?" - Abubakar Gumi (Hausa)

37:60 إِنَّ هَـٰذَا لَهُوَ ٱلْفَوْزُ ٱلْعَظِيمُ
37:60 Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:61 لِمِثْلِ هَـٰذَا فَلْيَعْمَلِ ٱلْعَـٰمِلُونَ
37:61 Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:62 أَذَٰلِكَ خَيْرٌ نُّزُلًا أَمْ شَجَرَةُ ٱلزَّقُّومِ
37:62 Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm? - Abubakar Gumi (Hausa)

37:63 إِنَّا جَعَلْنَـٰهَا فِتْنَةً لِّلظَّـٰلِمِينَ
37:63 Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:64 إِنَّهَا شَجَرَةٌ تَخْرُجُ فِىٓ أَصْلِ ٱلْجَحِيمِ
37:64 Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:65 طَلْعُهَا كَأَنَّهُۥ رُءُوسُ ٱلشَّيَـٰطِينِ
37:65 Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:66 فَإِنَّهُمْ لَـَٔاكِلُونَ مِنْهَا فَمَالِـُٔونَ مِنْهَا ٱلْبُطُونَ
37:66 To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:67 ثُمَّ إِنَّ لَهُمْ عَلَيْهَا لَشَوْبًا مِّنْ حَمِيمٍ
37:67 Sa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:68 ثُمَّ إِنَّ مَرْجِعَهُمْ لَإِلَى ٱلْجَحِيمِ
37:68 Sa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:69 إِنَّهُمْ أَلْفَوْا۟ ءَابَآءَهُمْ ضَآلِّينَ
37:69 Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:70 فَهُمْ عَلَىٰٓ ءَاثَـٰرِهِمْ يُهْرَعُونَ
37:70 Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:71 وَلَقَدْ ضَلَّ قَبْلَهُمْ أَكْثَرُ ٱلْأَوَّلِينَ
37:71 Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:72 وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا فِيهِم مُّنذِرِينَ
37:72 Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:73 فَٱنظُرْ كَيْفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلْمُنذَرِينَ
37:73 Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:74 إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلْمُخْلَصِينَ
37:74 Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:75 وَلَقَدْ نَادَىٰنَا نُوحٌ فَلَنِعْمَ ٱلْمُجِيبُونَ
37:75 Kuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:76 وَنَجَّيْنَـٰهُ وَأَهْلَهُۥ مِنَ ٱلْكَرْبِ ٱلْعَظِيمِ
37:76 Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:77 وَجَعَلْنَا ذُرِّيَّتَهُۥ هُمُ ٱلْبَاقِينَ
37:77 Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:78 وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِى ٱلْـَٔاخِرِينَ
37:78 Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:79 سَلَـٰمٌ عَلَىٰ نُوحٍ فِى ٱلْعَـٰلَمِينَ
37:79 Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:80 إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ
37:80 Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:81 إِنَّهُۥ مِنْ عِبَادِنَا ٱلْمُؤْمِنِينَ
37:81 Lalle shi, yanã daga bãyinMu mũminai. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:82 ثُمَّ أَغْرَقْنَا ٱلْـَٔاخَرِينَ
37:82 Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:83 ۞ وَإِنَّ مِن شِيعَتِهِۦ لَإِبْرَٰهِيمَ
37:83 Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:84 إِذْ جَآءَ رَبَّهُۥ بِقَلْبٍ سَلِيمٍ
37:84 A lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:85 إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِۦ مَاذَا تَعْبُدُونَ
37:85 A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa?" - Abubakar Gumi (Hausa)

37:86 أَئِفْكًا ءَالِهَةً دُونَ ٱللَّهِ تُرِيدُونَ
37:86 "Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?" - Abubakar Gumi (Hausa)

37:87 فَمَا ظَنُّكُم بِرَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ
37:87 "To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?" - Abubakar Gumi (Hausa)

37:88 فَنَظَرَ نَظْرَةً فِى ٱلنُّجُومِ
37:88 Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:89 فَقَالَ إِنِّى سَقِيمٌ
37:89 Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne." - Abubakar Gumi (Hausa)

37:90 فَتَوَلَّوْا۟ عَنْهُ مُدْبِرِينَ
37:90 Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:91 فَرَاغَ إِلَىٰٓ ءَالِهَتِهِمْ فَقَالَ أَلَا تَأْكُلُونَ
37:91 Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba? - Abubakar Gumi (Hausa)

37:92 مَا لَكُمْ لَا تَنطِقُونَ
37:92 "Me ya sãme ku, bã ku magana?" - Abubakar Gumi (Hausa)

37:93 فَرَاغَ عَلَيْهِمْ ضَرْبًۢا بِٱلْيَمِينِ
37:93 Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:94 فَأَقْبَلُوٓا۟ إِلَيْهِ يَزِفُّونَ
37:94 Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:95 قَالَ أَتَعْبُدُونَ مَا تَنْحِتُونَ
37:95 Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa, - Abubakar Gumi (Hausa)

37:96 وَٱللَّهُ خَلَقَكُمْ وَمَا تَعْمَلُونَ
37:96 "Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?" - Abubakar Gumi (Hausa)

37:97 قَالُوا۟ ٱبْنُوا۟ لَهُۥ بُنْيَـٰنًا فَأَلْقُوهُ فِى ٱلْجَحِيمِ
37:97 Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm." - Abubakar Gumi (Hausa)

37:98 فَأَرَادُوا۟ بِهِۦ كَيْدًا فَجَعَلْنَـٰهُمُ ٱلْأَسْفَلِينَ
37:98 Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:99 وَقَالَ إِنِّى ذَاهِبٌ إِلَىٰ رَبِّى سَيَهْدِينِ
37:99 Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni." - Abubakar Gumi (Hausa)

37:100 رَبِّ هَبْ لِى مِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ
37:100 "Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne." - Abubakar Gumi (Hausa)

37:101 فَبَشَّرْنَـٰهُ بِغُلَـٰمٍ حَلِيمٍ
37:101 Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:102 فَلَمَّا بَلَغَ مَعَهُ ٱلسَّعْىَ قَالَ يَـٰبُنَىَّ إِنِّىٓ أَرَىٰ فِى ٱلْمَنَامِ أَنِّىٓ أَذْبَحُكَ فَٱنظُرْ مَاذَا تَرَىٰ ۚ قَالَ يَـٰٓأَبَتِ ٱفْعَلْ مَا تُؤْمَرُ ۖ سَتَجِدُنِىٓ إِن شَآءَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلصَّـٰبِرِينَ
37:102 To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri." - Abubakar Gumi (Hausa)

37:103 فَلَمَّآ أَسْلَمَا وَتَلَّهُۥ لِلْجَبِينِ
37:103 To, a lõkacin da suka yi sallama, (Ibrahĩm) ya kãyar da shi ga gẽfen gõshinsa. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:104 وَنَـٰدَيْنَـٰهُ أَن يَـٰٓإِبْرَٰهِيمُ
37:104 Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm!" - Abubakar Gumi (Hausa)

37:105 قَدْ صَدَّقْتَ ٱلرُّءْيَآ ۚ إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ
37:105 "Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:106 إِنَّ هَـٰذَا لَهُوَ ٱلْبَلَـٰٓؤُا۟ ٱلْمُبِينُ
37:106 Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:107 وَفَدَيْنَـٰهُ بِذِبْحٍ عَظِيمٍ
37:107 Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:108 وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِى ٱلْـَٔاخِرِينَ
37:108 Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:109 سَلَـٰمٌ عَلَىٰٓ إِبْرَٰهِيمَ
37:109 Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:110 كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ
37:110 Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:111 إِنَّهُۥ مِنْ عِبَادِنَا ٱلْمُؤْمِنِينَ
37:111 Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:112 وَبَشَّرْنَـٰهُ بِإِسْحَـٰقَ نَبِيًّا مِّنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ
37:112 Kuma Muka yi masa bushãra Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:113 وَبَـٰرَكْنَا عَلَيْهِ وَعَلَىٰٓ إِسْحَـٰقَ ۚ وَمِن ذُرِّيَّتِهِمَا مُحْسِنٌ وَظَالِمٌ لِّنَفْسِهِۦ مُبِينٌ
37:113 Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin). - Abubakar Gumi (Hausa)

37:114 وَلَقَدْ مَنَنَّا عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَـٰرُونَ
37:114 Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:115 وَنَجَّيْنَـٰهُمَا وَقَوْمَهُمَا مِنَ ٱلْكَرْبِ ٱلْعَظِيمِ
37:115 Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:116 وَنَصَرْنَـٰهُمْ فَكَانُوا۟ هُمُ ٱلْغَـٰلِبِينَ
37:116 Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:117 وَءَاتَيْنَـٰهُمَا ٱلْكِتَـٰبَ ٱلْمُسْتَبِينَ
37:117 Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:118 وَهَدَيْنَـٰهُمَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلْمُسْتَقِيمَ
37:118 Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:119 وَتَرَكْنَا عَلَيْهِمَا فِى ٱلْـَٔاخِرِينَ
37:119 Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:120 سَلَـٰمٌ عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَـٰرُونَ
37:120 Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:121 إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ
37:121 Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:122 إِنَّهُمَا مِنْ عِبَادِنَا ٱلْمُؤْمِنِينَ
37:122 Lalle, sunã daga bãyinMu mũminai. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:123 وَإِنَّ إِلْيَاسَ لَمِنَ ٱلْمُرْسَلِينَ
37:123 Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:124 إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِۦٓ أَلَا تَتَّقُونَ
37:124 A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?" - Abubakar Gumi (Hausa)

37:125 أَتَدْعُونَ بَعْلًا وَتَذَرُونَ أَحْسَنَ ٱلْخَـٰلِقِينَ
37:125 "Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?" - Abubakar Gumi (Hausa)

37:126 ٱللَّهَ رَبَّكُمْ وَرَبَّ ءَابَآئِكُمُ ٱلْأَوَّلِينَ
37:126 "Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko?" - Abubakar Gumi (Hausa)

37:127 فَكَذَّبُوهُ فَإِنَّهُمْ لَمُحْضَرُونَ
37:127 Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã). - Abubakar Gumi (Hausa)

37:128 إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلْمُخْلَصِينَ
37:128 Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:129 وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِى ٱلْـَٔاخِرِينَ
37:129 Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:130 سَلَـٰمٌ عَلَىٰٓ إِلْ يَاسِينَ
37:130 Aminci ya tabbata ga Ilyãs. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:131 إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِى ٱلْمُحْسِنِينَ
37:131 Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:132 إِنَّهُۥ مِنْ عِبَادِنَا ٱلْمُؤْمِنِينَ
37:132 Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:133 وَإِنَّ لُوطًا لَّمِنَ ٱلْمُرْسَلِينَ
37:133 Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:134 إِذْ نَجَّيْنَـٰهُ وَأَهْلَهُۥٓ أَجْمَعِينَ
37:134 A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:135 إِلَّا عَجُوزًا فِى ٱلْغَـٰبِرِينَ
37:135 Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba). - Abubakar Gumi (Hausa)

37:136 ثُمَّ دَمَّرْنَا ٱلْـَٔاخَرِينَ
37:136 Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:137 وَإِنَّكُمْ لَتَمُرُّونَ عَلَيْهِم مُّصْبِحِينَ
37:137 Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:138 وَبِٱلَّيْلِ ۗ أَفَلَا تَعْقِلُونَ
37:138 Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba? - Abubakar Gumi (Hausa)

37:139 وَإِنَّ يُونُسَ لَمِنَ ٱلْمُرْسَلِينَ
37:139 Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:140 إِذْ أَبَقَ إِلَى ٱلْفُلْكِ ٱلْمَشْحُونِ
37:140 A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:141 فَسَاهَمَ فَكَانَ مِنَ ٱلْمُدْحَضِينَ
37:141 Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:142 فَٱلْتَقَمَهُ ٱلْحُوتُ وَهُوَ مُلِيمٌ
37:142 Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:143 فَلَوْلَآ أَنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلْمُسَبِّحِينَ
37:143 To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba, - Abubakar Gumi (Hausa)

37:144 لَلَبِثَ فِى بَطْنِهِۦٓ إِلَىٰ يَوْمِ يُبْعَثُونَ
37:144 Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:145 ۞ فَنَبَذْنَـٰهُ بِٱلْعَرَآءِ وَهُوَ سَقِيمٌ
37:145 Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:146 وَأَنۢبَتْنَا عَلَيْهِ شَجَرَةً مِّن يَقْطِينٍ
37:146 Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:147 وَأَرْسَلْنَـٰهُ إِلَىٰ مِا۟ئَةِ أَلْفٍ أَوْ يَزِيدُونَ
37:147 Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka). - Abubakar Gumi (Hausa)

37:148 فَـَٔامَنُوا۟ فَمَتَّعْنَـٰهُمْ إِلَىٰ حِينٍ
37:148 Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:149 فَٱسْتَفْتِهِمْ أَلِرَبِّكَ ٱلْبَنَاتُ وَلَهُمُ ٱلْبَنُونَ
37:149 Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?" - Abubakar Gumi (Hausa)

37:150 أَمْ خَلَقْنَا ٱلْمَلَـٰٓئِكَةَ إِنَـٰثًا وَهُمْ شَـٰهِدُونَ
37:150 Kõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce? - Abubakar Gumi (Hausa)

37:151 أَلَآ إِنَّهُم مِّنْ إِفْكِهِمْ لَيَقُولُونَ
37:151 To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:152 وَلَدَ ٱللَّهُ وَإِنَّهُمْ لَكَـٰذِبُونَ
37:152 "Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:153 أَصْطَفَى ٱلْبَنَاتِ عَلَى ٱلْبَنِينَ
37:153 Shin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza? - Abubakar Gumi (Hausa)

37:154 مَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ
37:154 Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannanhukunci)? - Abubakar Gumi (Hausa)

37:155 أَفَلَا تَذَكَّرُونَ
37:155 Shin, bã ku tunãni? - Abubakar Gumi (Hausa)

37:156 أَمْ لَكُمْ سُلْطَـٰنٌ مُّبِينٌ
37:156 Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne? - Abubakar Gumi (Hausa)

37:157 فَأْتُوا۟ بِكِتَـٰبِكُمْ إِن كُنتُمْ صَـٰدِقِينَ
37:157 To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:158 وَجَعَلُوا۟ بَيْنَهُۥ وَبَيْنَ ٱلْجِنَّةِ نَسَبًا ۚ وَلَقَدْ عَلِمَتِ ٱلْجِنَّةُ إِنَّهُمْ لَمُحْضَرُونَ
37:158 Kuma suka sanya nasaba a tsakãninSa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)" - Abubakar Gumi (Hausa)

37:159 سُبْحَـٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يَصِفُونَ
37:159 Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:160 إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلْمُخْلَصِينَ
37:160 Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:161 فَإِنَّكُمْ وَمَا تَعْبُدُونَ
37:161 To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa, - Abubakar Gumi (Hausa)

37:162 مَآ أَنتُمْ عَلَيْهِ بِفَـٰتِنِينَ
37:162 Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:163 إِلَّا مَنْ هُوَ صَالِ ٱلْجَحِيمِ
37:163 Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:164 وَمَا مِنَّآ إِلَّا لَهُۥ مَقَامٌ مَّعْلُومٌ
37:164 "Kuma bãbu kõwa daga cikinmu, fãce yanã da matsayi sananne." - Abubakar Gumi (Hausa)

37:165 وَإِنَّا لَنَحْنُ ٱلصَّآفُّونَ
37:165 "Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)." - Abubakar Gumi (Hausa)

37:166 وَإِنَّا لَنَحْنُ ٱلْمُسَبِّحُونَ
37:166 "Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi." - Abubakar Gumi (Hausa)

37:167 وَإِن كَانُوا۟ لَيَقُولُونَ
37:167 Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa, - Abubakar Gumi (Hausa)

37:168 لَوْ أَنَّ عِندَنَا ذِكْرًا مِّنَ ٱلْأَوَّلِينَ
37:168 "Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko." - Abubakar Gumi (Hausa)

37:169 لَكُنَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلْمُخْلَصِينَ
37:169 "Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake." - Abubakar Gumi (Hausa)

37:170 فَكَفَرُوا۟ بِهِۦ ۖ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ
37:170 Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:171 وَلَقَدْ سَبَقَتْ كَلِمَتُنَا لِعِبَادِنَا ٱلْمُرْسَلِينَ
37:171 Kuma lalle, haƙĩƙa kalmarMu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:172 إِنَّهُمْ لَهُمُ ٱلْمَنصُورُونَ
37:172 Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:173 وَإِنَّ جُندَنَا لَهُمُ ٱلْغَـٰلِبُونَ
37:173 Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:174 فَتَوَلَّ عَنْهُمْ حَتَّىٰ حِينٍ
37:174 Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:175 وَأَبْصِرْهُمْ فَسَوْفَ يُبْصِرُونَ
37:175 Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:176 أَفَبِعَذَابِنَا يَسْتَعْجِلُونَ
37:176 Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

37:177 فَإِذَا نَزَلَ بِسَاحَتِهِمْ فَسَآءَ صَبَاحُ ٱلْمُنذَرِينَ
37:177 To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:178 وَتَوَلَّ عَنْهُمْ حَتَّىٰ حِينٍ
37:178 Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:179 وَأَبْصِرْ فَسَوْفَ يُبْصِرُونَ
37:179 Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:180 سُبْحَـٰنَ رَبِّكَ رَبِّ ٱلْعِزَّةِ عَمَّا يَصِفُونَ
37:180 Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:181 وَسَلَـٰمٌ عَلَى ٱلْمُرْسَلِينَ
37:181 Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni. - Abubakar Gumi (Hausa)

37:182 وَٱلْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ
37:182 Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu. - Abubakar Gumi (Hausa)