Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

69 Al-Ĥāqqah ٱلْحَاقَّة

< Previous   52 Āyah   The Reality      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

69:1 ٱلْحَآقَّةُ
69:1 Kiran gaskiya! - Abubakar Gumi (Hausa)

69:2 مَا ٱلْحَآقَّةُ
69:2 Mẽne ne kiran gaskiya? - Abubakar Gumi (Hausa)

69:3 وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا ٱلْحَآقَّةُ
69:3 Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya? - Abubakar Gumi (Hausa)

69:4 كَذَّبَتْ ثَمُودُ وَعَادٌۢ بِٱلْقَارِعَةِ
69:4 Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya! - Abubakar Gumi (Hausa)

69:5 فَأَمَّا ثَمُودُ فَأُهْلِكُوا۟ بِٱلطَّاغِيَةِ
69:5 To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:6 وَأَمَّا عَادٌ فَأُهْلِكُوا۟ بِرِيحٍ صَرْصَرٍ عَاتِيَةٍ
69:6 Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:7 سَخَّرَهَا عَلَيْهِمْ سَبْعَ لَيَالٍ وَثَمَـٰنِيَةَ أَيَّامٍ حُسُومًا فَتَرَى ٱلْقَوْمَ فِيهَا صَرْعَىٰ كَأَنَّهُمْ أَعْجَازُ نَخْلٍ خَاوِيَةٍ
69:7 (Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:8 فَهَلْ تَرَىٰ لَهُم مِّنۢ بَاقِيَةٍ
69:8 To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu? - Abubakar Gumi (Hausa)

69:9 وَجَآءَ فِرْعَوْنُ وَمَن قَبْلَهُۥ وَٱلْمُؤْتَفِكَـٰتُ بِٱلْخَاطِئَةِ
69:9 Kuma Fir'auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:10 فَعَصَوْا۟ رَسُولَ رَبِّهِمْ فَأَخَذَهُمْ أَخْذَةً رَّابِيَةً
69:10 Dõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu mai ƙãruwar (tsanani). - Abubakar Gumi (Hausa)

69:11 إِنَّا لَمَّا طَغَا ٱلْمَآءُ حَمَلْنَـٰكُمْ فِى ٱلْجَارِيَةِ
69:11 Lalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙẽtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:12 لِنَجْعَلَهَا لَكُمْ تَذْكِرَةً وَتَعِيَهَآ أُذُنٌ وَٰعِيَةٌ
69:12 Dõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi). - Abubakar Gumi (Hausa)

69:13 فَإِذَا نُفِخَ فِى ٱلصُّورِ نَفْخَةٌ وَٰحِدَةٌ
69:13 To, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:14 وَحُمِلَتِ ٱلْأَرْضُ وَٱلْجِبَالُ فَدُكَّتَا دَكَّةً وَٰحِدَةً
69:14 Kuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:15 فَيَوْمَئِذٍ وَقَعَتِ ٱلْوَاقِعَةُ
69:15 A ran nan, mai aukuwa zã ta auku. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:16 وَٱنشَقَّتِ ٱلسَّمَآءُ فَهِىَ يَوْمَئِذٍ وَاهِيَةٌ
69:16 Kuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:17 وَٱلْمَلَكُ عَلَىٰٓ أَرْجَآئِهَا ۚ وَيَحْمِلُ عَرْشَ رَبِّكَ فَوْقَهُمْ يَوْمَئِذٍ ثَمَـٰنِيَةٌ
69:17 Kuma malã'iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã'iku) takwas na ɗauke da Al'arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:18 يَوْمَئِذٍ تُعْرَضُونَ لَا تَخْفَىٰ مِنكُمْ خَافِيَةٌ
69:18 A rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓõyẽwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:19 فَأَمَّا مَنْ أُوتِىَ كِتَـٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ فَيَقُولُ هَآؤُمُ ٱقْرَءُوا۟ كِتَـٰبِيَهْ
69:19 To, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa), "Ku karɓa, ku karanta littafina." - Abubakar Gumi (Hausa)

69:20 إِنِّى ظَنَنتُ أَنِّى مُلَـٰقٍ حِسَابِيَهْ
69:20 "Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne." - Abubakar Gumi (Hausa)

69:21 فَهُوَ فِى عِيشَةٍ رَّاضِيَةٍ
69:21 Sabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:22 فِى جَنَّةٍ عَالِيَةٍ
69:22 A cikin Aljanna maɗaukakiya. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:23 قُطُوفُهَا دَانِيَةٌ
69:23 Nunannun 'yã'yan itãcenta makusantã ne (ga mai son ɗĩba), - Abubakar Gumi (Hausa)

69:24 كُلُوا۟ وَٱشْرَبُوا۟ هَنِيٓـًٔۢا بِمَآ أَسْلَفْتُمْ فِى ٱلْأَيَّامِ ٱلْخَالِيَةِ
69:24 (Ana ce musu) "Ku ci, kuma ku sha a cikin ni'ima, sabõda abin da kuka gabãtar a cikin kwãnukan da suka shige." - Abubakar Gumi (Hausa)

69:25 وَأَمَّا مَنْ أُوتِىَ كِتَـٰبَهُۥ بِشِمَالِهِۦ فَيَقُولُ يَـٰلَيْتَنِى لَمْ أُوتَ كِتَـٰبِيَهْ
69:25 Kuma wanda aka bai wa littãfinsa ga hagunsa, sai ya ce: "Kaitona, ba a kãwo mini littãfina ba!" - Abubakar Gumi (Hausa)

69:26 وَلَمْ أَدْرِ مَا حِسَابِيَهْ
69:26 "Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisãbina ba!" - Abubakar Gumi (Hausa)

69:27 يَـٰلَيْتَهَا كَانَتِ ٱلْقَاضِيَةَ
69:27 "In dã dai ita, tã kasance mai halakã ni gabã ɗaya ce! - Abubakar Gumi (Hausa)

69:28 مَآ أَغْنَىٰ عَنِّى مَالِيَهْ ۜ
69:28 "Dukiyãta ba ta wadatar da ni ba!" - Abubakar Gumi (Hausa)

69:29 هَلَكَ عَنِّى سُلْطَـٰنِيَهْ
69:29 "Ĩkona ya ɓace mini!" - Abubakar Gumi (Hausa)

69:30 خُذُوهُ فَغُلُّوهُ
69:30 (Sai a ce wa malã'iku) "Ku kãmã shi, sa'an nan ku sanyã shi a cikin ƙuƙumi." - Abubakar Gumi (Hausa)

69:31 ثُمَّ ٱلْجَحِيمَ صَلُّوهُ
69:31 "Sa'an nan, a cikin Jahĩm, ku ƙõna shi." - Abubakar Gumi (Hausa)

69:32 ثُمَّ فِى سِلْسِلَةٍ ذَرْعُهَا سَبْعُونَ ذِرَاعًا فَٱسْلُكُوهُ
69:32 "Sa'an nan, acikin sarƙa, tsawonta zirã'i saba'in, sai ku sanya shi." - Abubakar Gumi (Hausa)

69:33 إِنَّهُۥ كَانَ لَا يُؤْمِنُ بِٱللَّهِ ٱلْعَظِيمِ
69:33 "Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin ĩmãni da Allah, Mai girma!" - Abubakar Gumi (Hausa)

69:34 وَلَا يَحُضُّ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلْمِسْكِينِ
69:34 "Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci!" - Abubakar Gumi (Hausa)

69:35 فَلَيْسَ لَهُ ٱلْيَوْمَ هَـٰهُنَا حَمِيمٌ
69:35 "Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi." - Abubakar Gumi (Hausa)

69:36 وَلَا طَعَامٌ إِلَّا مِنْ غِسْلِينٍ
69:36 "Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn." - Abubakar Gumi (Hausa)

69:37 لَّا يَأْكُلُهُۥٓ إِلَّا ٱلْخَـٰطِـُٔونَ
69:37 "Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci." - Abubakar Gumi (Hausa)

69:38 فَلَآ أُقْسِمُ بِمَا تُبْصِرُونَ
69:38 To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba, - Abubakar Gumi (Hausa)

69:39 وَمَا لَا تُبْصِرُونَ
69:39 Da abin da bã ku iya gani. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:40 إِنَّهُۥ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ
69:40 Lalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:41 وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَاعِرٍ ۚ قَلِيلًا مَّا تُؤْمِنُونَ
69:41 Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:42 وَلَا بِقَوْلِ كَاهِنٍ ۚ قَلِيلًا مَّا تَذَكَّرُونَ
69:42 Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:43 تَنزِيلٌ مِّن رَّبِّ ٱلْعَـٰلَمِينَ
69:43 Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:44 وَلَوْ تَقَوَّلَ عَلَيْنَا بَعْضَ ٱلْأَقَاوِيلِ
69:44 Kuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:45 لَأَخَذْنَا مِنْهُ بِٱلْيَمِينِ
69:45 Dã Mun kãma shi da dãma. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:46 ثُمَّ لَقَطَعْنَا مِنْهُ ٱلْوَتِينَ
69:46 sa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:47 فَمَا مِنكُم مِّنْ أَحَدٍ عَنْهُ حَـٰجِزِينَ
69:47 Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbarMu) daga gare shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:48 وَإِنَّهُۥ لَتَذْكِرَةٌ لِّلْمُتَّقِينَ
69:48 Kuma lalle ne shi (Alƙur'ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:49 وَإِنَّا لَنَعْلَمُ أَنَّ مِنكُم مُّكَذِّبِينَ
69:49 Kuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:50 وَإِنَّهُۥ لَحَسْرَةٌ عَلَى ٱلْكَـٰفِرِينَ
69:50 Kuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:51 وَإِنَّهُۥ لَحَقُّ ٱلْيَقِينِ
69:51 Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙshẽni. - Abubakar Gumi (Hausa)

69:52 فَسَبِّحْ بِٱسْمِ رَبِّكَ ٱلْعَظِيمِ
69:52 Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma. - Abubakar Gumi (Hausa)