Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

88 Al-Ghāshiyah ٱلْغَاشِيَة

< Previous   26 Āyah   The Overwhelming      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

88:1 هَلْ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلْغَـٰشِيَةِ
88:1 Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka? - Abubakar Gumi (Hausa)

88:2 وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ خَـٰشِعَةٌ
88:2 Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

88:3 عَامِلَةٌ نَّاصِبَةٌ
88:3 Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya. - Abubakar Gumi (Hausa)

88:4 تَصْلَىٰ نَارًا حَامِيَةً
88:4 Zã su shiga wata wuta mai zãfi. - Abubakar Gumi (Hausa)

88:5 تُسْقَىٰ مِنْ عَيْنٍ ءَانِيَةٍ
88:5 Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

88:6 لَّيْسَ لَهُمْ طَعَامٌ إِلَّا مِن ضَرِيعٍ
88:6 Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi. - Abubakar Gumi (Hausa)

88:7 لَّا يُسْمِنُ وَلَا يُغْنِى مِن جُوعٍ
88:7 Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

88:8 وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَّاعِمَةٌ
88:8 Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

88:9 لِّسَعْيِهَا رَاضِيَةٌ
88:9 Game da aikinsu, masu yarda ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

88:10 فِى جَنَّةٍ عَالِيَةٍ
88:10 (Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya. - Abubakar Gumi (Hausa)

88:11 لَّا تَسْمَعُ فِيهَا لَـٰغِيَةً
88:11 Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta. - Abubakar Gumi (Hausa)

88:12 فِيهَا عَيْنٌ جَارِيَةٌ
88:12 A cikinta akwai marmaro mai gudãna. - Abubakar Gumi (Hausa)

88:13 فِيهَا سُرُرٌ مَّرْفُوعَةٌ
88:13 A cikinta akwai gadãje maɗaukaka. - Abubakar Gumi (Hausa)

88:14 وَأَكْوَابٌ مَّوْضُوعَةٌ
88:14 Da kõfuna ar'aje. - Abubakar Gumi (Hausa)

88:15 وَنَمَارِقُ مَصْفُوفَةٌ
88:15 Da filõli jẽre, - Abubakar Gumi (Hausa)

88:16 وَزَرَابِىُّ مَبْثُوثَةٌ
88:16 Da katifu shimfiɗe. - Abubakar Gumi (Hausa)

88:17 أَفَلَا يَنظُرُونَ إِلَى ٱلْإِبِلِ كَيْفَ خُلِقَتْ
88:17 Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su? - Abubakar Gumi (Hausa)

88:18 وَإِلَى ٱلسَّمَآءِ كَيْفَ رُفِعَتْ
88:18 Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta? - Abubakar Gumi (Hausa)

88:19 وَإِلَى ٱلْجِبَالِ كَيْفَ نُصِبَتْ
88:19 Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su? - Abubakar Gumi (Hausa)

88:20 وَإِلَى ٱلْأَرْضِ كَيْفَ سُطِحَتْ
88:20 Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta? - Abubakar Gumi (Hausa)

88:21 فَذَكِّرْ إِنَّمَآ أَنتَ مُذَكِّرٌ
88:21 sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai. - Abubakar Gumi (Hausa)

88:22 لَّسْتَ عَلَيْهِم بِمُصَيْطِرٍ
88:22 Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

88:23 إِلَّا مَن تَوَلَّىٰ وَكَفَرَ
88:23 Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta. - Abubakar Gumi (Hausa)

88:24 فَيُعَذِّبُهُ ٱللَّهُ ٱلْعَذَابَ ٱلْأَكْبَرَ
88:24 To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma. - Abubakar Gumi (Hausa)

88:25 إِنَّ إِلَيْنَآ إِيَابَهُمْ
88:25 Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take. - Abubakar Gumi (Hausa)

88:26 ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا حِسَابَهُم
88:26 Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi. - Abubakar Gumi (Hausa)