Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

74 Al-Muddaththir ٱلْمُدَّثِّر

< Previous   56 Āyah   The Cloaked One      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

74:1 يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْمُدَّثِّرُ
74:1 Yã wanda ya lulluɓa da mayãfi. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:2 قُمْ فَأَنذِرْ
74:2 Ka tãshi dõmin ka yi gargaɗi - Abubakar Gumi (Hausa)

74:3 وَرَبَّكَ فَكَبِّرْ
74:3 Kuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi, - Abubakar Gumi (Hausa)

74:4 وَثِيَابَكَ فَطَهِّرْ
74:4 Kuma tutãfinka, sai ka tsarkake su, - Abubakar Gumi (Hausa)

74:5 وَٱلرُّجْزَ فَٱهْجُرْ
74:5 Kuma gumãka, sai ka ƙaurace musu. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:6 وَلَا تَمْنُن تَسْتَكْثِرُ
74:6 Kada ka yi kyauta kana nẽman ƙãri - Abubakar Gumi (Hausa)

74:7 وَلِرَبِّكَ فَٱصْبِرْ
74:7 Kuma sabõda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure - Abubakar Gumi (Hausa)

74:8 فَإِذَا نُقِرَ فِى ٱلنَّاقُورِ
74:8 To, idan aka yi bũsa a cikin ƙaho. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:9 فَذَٰلِكَ يَوْمَئِذٍ يَوْمٌ عَسِيرٌ
74:9 To, wannan, a rãnar nan, yini ne mai wuya - Abubakar Gumi (Hausa)

74:10 عَلَى ٱلْكَـٰفِرِينَ غَيْرُ يَسِيرٍ
74:10 A kan kãfirai, bã mai sauƙi ba ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:11 ذَرْنِى وَمَنْ خَلَقْتُ وَحِيدًا
74:11 Ka bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai, - Abubakar Gumi (Hausa)

74:12 وَجَعَلْتُ لَهُۥ مَالًا مَّمْدُودًا
74:12 Kuma Na sanya masa dũkiya shimfiɗaɗɗiya - Abubakar Gumi (Hausa)

74:13 وَبَنِينَ شُهُودًا
74:13 Da ɗiyã halartattu, - Abubakar Gumi (Hausa)

74:14 وَمَهَّدتُّ لَهُۥ تَمْهِيدًا
74:14 Kuma Na shimfiɗa? masa kõme shimfiɗãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:15 ثُمَّ يَطْمَعُ أَنْ أَزِيدَ
74:15 Sa'an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri! - Abubakar Gumi (Hausa)

74:16 كَلَّآ ۖ إِنَّهُۥ كَانَ لِـَٔايَـٰتِنَا عَنِيدًا
74:16 Faufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyinMu, mai tsaurin kai. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:17 سَأُرْهِقُهُۥ صَعُودًا
74:17 Zã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:18 إِنَّهُۥ فَكَّرَ وَقَدَّرَ
74:18 Lalle ne, Shi, yã yi tunãni, kuma yã ƙaddara (abin da zai faɗã game da Alƙur'ãni) - Abubakar Gumi (Hausa)

74:19 فَقُتِلَ كَيْفَ قَدَّرَ
74:19 Sabõda haka, aka la'ane shi, kamar yadda ya ƙaddara. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:20 ثُمَّ قُتِلَ كَيْفَ قَدَّرَ
74:20 Sa'an nan, aka la'ane shi kamar yadda ya ƙaddara. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:21 ثُمَّ نَظَرَ
74:21 Sa'an nan, ya yi tunãni - Abubakar Gumi (Hausa)

74:22 ثُمَّ عَبَسَ وَبَسَرَ
74:22 Sa'an nan, ya gintse huska? kuma ya yi murtuk. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:23 ثُمَّ أَدْبَرَ وَٱسْتَكْبَرَ
74:23 Sa'an nan, ya jũya bãya, kuma ya bunƙãsa, - Abubakar Gumi (Hausa)

74:24 فَقَالَ إِنْ هَـٰذَآ إِلَّا سِحْرٌ يُؤْثَرُ
74:24 Sai ya ce: "Wannan abu dai bã kõme ba ne fãce wani sihiri, wanda aka ruwaito." - Abubakar Gumi (Hausa)

74:25 إِنْ هَـٰذَآ إِلَّا قَوْلُ ٱلْبَشَرِ
74:25 "Wannan maganar mutum dai ce." - Abubakar Gumi (Hausa)

74:26 سَأُصْلِيهِ سَقَرَ
74:26 Zã Ni ƙõna shi da Saƙar. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:27 وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا سَقَرُ
74:27 Kuma mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽwa Saƙar! - Abubakar Gumi (Hausa)

74:28 لَا تُبْقِى وَلَا تَذَرُ
74:28 Bã ta ragẽwa, kuma bã ta bari. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:29 لَوَّاحَةٌ لِّلْبَشَرِ
74:29 Mai nãcẽwa ga jiki ce (da (ƙũna). - Abubakar Gumi (Hausa)

74:30 عَلَيْهَا تِسْعَةَ عَشَرَ
74:30 A kanta akwai (matsara) gõma shã tara. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:31 وَمَا جَعَلْنَآ أَصْحَـٰبَ ٱلنَّارِ إِلَّا مَلَـٰٓئِكَةً ۙ وَمَا جَعَلْنَا عِدَّتَهُمْ إِلَّا فِتْنَةً لِّلَّذِينَ كَفَرُوا۟ لِيَسْتَيْقِنَ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْكِتَـٰبَ وَيَزْدَادَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓا۟ إِيمَـٰنًا ۙ وَلَا يَرْتَابَ ٱلَّذِينَ أُوتُوا۟ ٱلْكِتَـٰبَ وَٱلْمُؤْمِنُونَ ۙ وَلِيَقُولَ ٱلَّذِينَ فِى قُلُوبِهِم مَّرَضٌ وَٱلْكَـٰفِرُونَ مَاذَآ أَرَادَ ٱللَّهُ بِهَـٰذَا مَثَلًا ۚ كَذَٰلِكَ يُضِلُّ ٱللَّهُ مَن يَشَآءُ وَيَهْدِى مَن يَشَآءُ ۚ وَمَا يَعْلَمُ جُنُودَ رَبِّكَ إِلَّا هُوَ ۚ وَمَا هِىَ إِلَّا ذِكْرَىٰ لِلْبَشَرِ
74:31 Kuma ba Mu sanya ma'abũta wutã (wãto matsaranta) ba, fãce malã'iku, kuma ba Mu sanya adadinsu (gõma sha tara) ba, fãce dõmin fitina ga waɗanda suka kãfirta domin waɗanda aka bai wa littãfi su sãmi yaƙĩni kuma waɗanda suka yi ĩmãni su ƙãra ĩmãni, kuma waɗanda aka bai wa littãfi da mũminai bã zã su yi shakka ba, kuma domin wa ɗanda a cikin zukatansu akwai wata cuta da kãfirai su ce: "Mẽ Allah Yake nufi da wannan, ya kasance misãli?" Haka dai Allah ke ɓatar da wanda Ya so, kuma Ya shiryar da wanda ya so. Kuma bãbu wanda ya san mayãƙan Ubangijinka fãce Shi, kuma ita (wutar) ba ta kasance ba fãce wata tunãtarwa ce ga mutum. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:32 كَلَّا وَٱلْقَمَرِ
74:32 A'aha! Ina rantsuwa da watã. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:33 وَٱلَّيْلِ إِذْ أَدْبَرَ
74:33 Da dare a lõkacin da ya jũyar da baya. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:34 وَٱلصُّبْحِ إِذَآ أَسْفَرَ
74:34 Da sãfiya idan ta wãye. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:35 إِنَّهَا لَإِحْدَى ٱلْكُبَرِ
74:35 Ita (wutar) ɗayan manyan masĩfũ? ce. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:36 نَذِيرًا لِّلْبَشَرِ
74:36 Mai gargaɗĩ ce ga mutum. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:37 لِمَن شَآءَ مِنكُمْ أَن يَتَقَدَّمَ أَوْ يَتَأَخَّرَ
74:37 Ga wanda ya so, daga cikinku, ya gabãta ko ya jinkirta. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:38 كُلُّ نَفْسٍۭ بِمَا كَسَبَتْ رَهِينَةٌ
74:38 Kõwane rai ga abin da ya aikata jingina ce. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:39 إِلَّآ أَصْحَـٰبَ ٱلْيَمِينِ
74:39 Fãce mutãnen dãma. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:40 فِى جَنَّـٰتٍ يَتَسَآءَلُونَ
74:40 A cikin Aljanna suna tambayar jũna. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:41 عَنِ ٱلْمُجْرِمِينَ
74:41 Game da mãsu laifi. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:42 مَا سَلَكَكُمْ فِى سَقَرَ
74:42 (Su ce musu) "Me ya shigar da ku a cikin Saƙar?" - Abubakar Gumi (Hausa)

74:43 قَالُوا۟ لَمْ نَكُ مِنَ ٱلْمُصَلِّينَ
74:43 Suka ce: "Ba mu kasance munã a cikin mãsu salla ba." - Abubakar Gumi (Hausa)

74:44 وَلَمْ نَكُ نُطْعِمُ ٱلْمِسْكِينَ
74:44 "Kuma ba mu kasance muna ciyar da matalautã ba." - Abubakar Gumi (Hausa)

74:45 وَكُنَّا نَخُوضُ مَعَ ٱلْخَآئِضِينَ
74:45 "Kuma mun kasance muna kũtsãwa tãre da mãsu kũtsãwa." - Abubakar Gumi (Hausa)

74:46 وَكُنَّا نُكَذِّبُ بِيَوْمِ ٱلدِّينِ
74:46 "Mun kasance munã ƙaryata rãnar sãkamako." - Abubakar Gumi (Hausa)

74:47 حَتَّىٰٓ أَتَىٰنَا ٱلْيَقِينُ
74:47 "Har gaskiya (wãto mutuwa) ta zo mana." - Abubakar Gumi (Hausa)

74:48 فَمَا تَنفَعُهُمْ شَفَـٰعَةُ ٱلشَّـٰفِعِينَ
74:48 Sabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:49 فَمَا لَهُمْ عَنِ ٱلتَّذْكِرَةِ مُعْرِضِينَ
74:49 Haba! Me ya same su, suka zama mãsu bijirewa daga wa'azin gaskiya. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:50 كَأَنَّهُمْ حُمُرٌ مُّسْتَنفِرَةٌ
74:50 Kamar dai sũ, jãkuna firgitattu ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:51 فَرَّتْ مِن قَسْوَرَةٍۭ
74:51 Sun gudu daga zãki. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:52 بَلْ يُرِيدُ كُلُّ ٱمْرِئٍ مِّنْهُمْ أَن يُؤْتَىٰ صُحُفًا مُّنَشَّرَةً
74:52 A'aha! Kõwãne mutum daga cikinsu yanã son a zo masa da takardu (da sũnansa) ana wãtsãwa - Abubakar Gumi (Hausa)

74:53 كَلَّا ۖ بَل لَّا يَخَافُونَ ٱلْـَٔاخِرَةَ
74:53 A'aha! Kai dai, bã su jin tsõron Lãhira. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:54 كَلَّآ إِنَّهُۥ تَذْكِرَةٌ
74:54 A'aha! Lalle ne, shi (Alƙur'ãni) tunãtarwa ce. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:55 فَمَن شَآءَ ذَكَرَهُۥ
74:55 Dõmin wanda ya so, ya tuna. - Abubakar Gumi (Hausa)

74:56 وَمَا يَذْكُرُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ ۚ هُوَ أَهْلُ ٱلتَّقْوَىٰ وَأَهْلُ ٱلْمَغْفِرَةِ
74:56 Kuma bã zã su tuna ba fãce idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gãfara. - Abubakar Gumi (Hausa)