Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

99 Az-Zalzalah ٱلزَّلْرَلَة

< Previous   8 Āyah   The Earthquake      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

99:1 إِذَا زُلْزِلَتِ ٱلْأَرْضُ زِلْزَالَهَا
99:1 Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta. - Abubakar Gumi (Hausa)

99:2 وَأَخْرَجَتِ ٱلْأَرْضُ أَثْقَالَهَا
99:2 Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi. - Abubakar Gumi (Hausa)

99:3 وَقَالَ ٱلْإِنسَـٰنُ مَا لَهَا
99:3 Kuma mutum ya ce "Mẽ neya same ta?" - Abubakar Gumi (Hausa)

99:4 يَوْمَئِذٍ تُحَدِّثُ أَخْبَارَهَا
99:4 A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta. - Abubakar Gumi (Hausa)

99:5 بِأَنَّ رَبَّكَ أَوْحَىٰ لَهَا
99:5 cewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta. - Abubakar Gumi (Hausa)

99:6 يَوْمَئِذٍ يَصْدُرُ ٱلنَّاسُ أَشْتَاتًا لِّيُرَوْا۟ أَعْمَـٰلَهُمْ
99:6 A rãnar nan mutane za su fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu. - Abubakar Gumi (Hausa)

99:7 فَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ خَيْرًا يَرَهُۥ
99:7 To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

99:8 وَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ شَرًّا يَرَهُۥ
99:8 Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi. - Abubakar Gumi (Hausa)