Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

55 Ar-Raĥmān ٱلرَّحْمَٰن

< Previous   78 Āyah   The Beneficent      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

55:1 ٱلرَّحْمَـٰنُ
55:1 (Allah) Mai rahama. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:2 عَلَّمَ ٱلْقُرْءَانَ
55:2 Yã sanar da Alƙur'ani. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:3 خَلَقَ ٱلْإِنسَـٰنَ
55:3 Yã halitta mutum. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:4 عَلَّمَهُ ٱلْبَيَانَ
55:4 Yã sanar da shi bayãni (magana). - Abubakar Gumi (Hausa)

55:5 ٱلشَّمْسُ وَٱلْقَمَرُ بِحُسْبَانٍ
55:5 Rãnã da watã a kan lissãfi suke. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:6 وَٱلنَّجْمُ وَٱلشَّجَرُ يَسْجُدَانِ
55:6 Kuma tsirrai mãsu yãɗo da itãce sunã tawãlu'i. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:7 وَٱلسَّمَآءَ رَفَعَهَا وَوَضَعَ ٱلْمِيزَانَ
55:7 Kuma samã Ya ɗaukaka ta, Kuma Yã aza sikẽli. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:8 أَلَّا تَطْغَوْا۟ فِى ٱلْمِيزَانِ
55:8 Dõmin kada ku karkatar da sikẽlin. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:9 وَأَقِيمُوا۟ ٱلْوَزْنَ بِٱلْقِسْطِ وَلَا تُخْسِرُوا۟ ٱلْمِيزَانَ
55:9 Kuma ku daidaita awo da ãdalci, kuma kada ku rage sikẽlin. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:10 وَٱلْأَرْضَ وَضَعَهَا لِلْأَنَامِ
55:10 Kuma ƙasã Yã aza ta dõmin tãlikai. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:11 فِيهَا فَـٰكِهَةٌ وَٱلنَّخْلُ ذَاتُ ٱلْأَكْمَامِ
55:11 A cikinta akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno mai kwasfa. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:12 وَٱلْحَبُّ ذُو ٱلْعَصْفِ وَٱلرَّيْحَانُ
55:12 Da ƙwãya mai sõshiya da ƙamshi. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:13 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:13 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangjinku kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:14 خَلَقَ ٱلْإِنسَـٰنَ مِن صَلْصَـٰلٍ كَٱلْفَخَّارِ
55:14 Yã halitta mutum daga ƙẽkasasshen yumɓu kumar kasko. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:15 وَخَلَقَ ٱلْجَآنَّ مِن مَّارِجٍ مِّن نَّارٍ
55:15 Kuma ya halitta aljani daga bira daga wutã. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:16 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:16 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:17 رَبُّ ٱلْمَشْرِقَيْنِ وَرَبُّ ٱلْمَغْرِبَيْنِ
55:17 Ubangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:18 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:18 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:19 مَرَجَ ٱلْبَحْرَيْنِ يَلْتَقِيَانِ
55:19 Yã garwaya tẽku biyu (ruwan dãɗi da na zartsi) sunã haɗuwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:20 بَيْنَهُمَا بَرْزَخٌ لَّا يَبْغِيَانِ
55:20 A tsakãninsu akwai shãmaki, bã za su ƙetare haddi ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:21 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:21 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:22 يَخْرُجُ مِنْهُمَا ٱللُّؤْلُؤُ وَٱلْمَرْجَانُ
55:22 Lu'ulu'u da murjãni na fita daga gare su. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:23 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:23 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:24 وَلَهُ ٱلْجَوَارِ ٱلْمُنشَـَٔاتُ فِى ٱلْبَحْرِ كَٱلْأَعْلَـٰمِ
55:24 Kuma Yanã da manyan jirãge, waɗanda ake ƙãgãwa a cikin tẽku kamar manyan duwãtsu. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:25 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:25 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:26 كُلُّ مَنْ عَلَيْهَا فَانٍ
55:26 Dukkan wanda ke kanta mai ƙãrẽwa ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:27 وَيَبْقَىٰ وَجْهُ رَبِّكَ ذُو ٱلْجَلَـٰلِ وَٱلْإِكْرَامِ
55:27 Kuma Fuskarar Ubangijinka, Mai girman Jalala da karimci, ita ce take wanzuwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:28 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:28 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:29 يَسْـَٔلُهُۥ مَن فِى ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ ۚ كُلَّ يَوْمٍ هُوَ فِى شَأْنٍ
55:29 wanda ke a cikin sammai da ƙasã yanã rõƙon Sa (Allah), a kullum Allah na a cikin wani sha'ani. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:30 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:30 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:31 سَنَفْرُغُ لَكُمْ أَيُّهَ ٱلثَّقَلَانِ
55:31 Zã mu ɗauki lõkaci sabõda ku, yã kũ mãsu nauyin halitta biyu! - Abubakar Gumi (Hausa)

55:32 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:32 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:33 يَـٰمَعْشَرَ ٱلْجِنِّ وَٱلْإِنسِ إِنِ ٱسْتَطَعْتُمْ أَن تَنفُذُوا۟ مِنْ أَقْطَارِ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ فَٱنفُذُوا۟ ۚ لَا تَنفُذُونَ إِلَّا بِسُلْطَـٰنٍ
55:33 Ya jama'ar aljannu da mutãne! Idan kunã iya zarcẽwa daga sãsannin sammai da ƙasã to ku zarce. Bã za ku iya zarcẽwaba fãce da wani dalĩli. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:34 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:34 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:35 يُرْسَلُ عَلَيْكُمَا شُوَاظٌ مِّن نَّارٍ وَنُحَاسٌ فَلَا تَنتَصِرَانِ
55:35 Anã sako wani harshe daga wata wutã a kanku, da narkakkiyar tagulla. To, bã zã ku nẽmi taimako ba? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:36 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:36 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:37 فَإِذَا ٱنشَقَّتِ ٱلسَّمَآءُ فَكَانَتْ وَرْدَةً كَٱلدِّهَانِ
55:37 Sa'an nan idan sama ta tsãge kuma ta zama jã kamar jar fãta. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:38 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:38 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:39 فَيَوْمَئِذٍ لَّا يُسْـَٔلُ عَن ذَنۢبِهِۦٓ إِنسٌ وَلَا جَآنٌّ
55:39 To, a ran nan bã zã a tambayi wani mutum laifinsa ba, kuma haka aljani. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:40 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:40 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:41 يُعْرَفُ ٱلْمُجْرِمُونَ بِسِيمَـٰهُمْ فَيُؤْخَذُ بِٱلنَّوَٰصِى وَٱلْأَقْدَامِ
55:41 zã a iya sanin mãsu laifi da alãmarsu, sabõda haka sai a kãma kwarkaɗarsu da sãwãyensu. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:42 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:42 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:43 هَـٰذِهِۦ جَهَنَّمُ ٱلَّتِى يُكَذِّبُ بِهَا ٱلْمُجْرِمُونَ
55:43 Wannan Jahannama ce wadda mãsu laifi ke ƙaryatãwa game da ita. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:44 يَطُوفُونَ بَيْنَهَا وَبَيْنَ حَمِيمٍ ءَانٍ
55:44 Sunã kẽwaya a tsakaninta da ruwan ɗimi mai tsananin tafasa. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:45 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:45 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:46 وَلِمَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِۦ جَنَّتَانِ
55:46 Kuma wanda ya ji tsõron tsayãwa a gaba ga Ubangijinsa yanã da Aljanna biyu. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:47 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:47 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:48 ذَوَاتَآ أَفْنَانٍ
55:48 Mãsu rassan itãce. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:49 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:49 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:50 فِيهِمَا عَيْنَانِ تَجْرِيَانِ
55:50 A cikinsu akwai marẽmari biyu sunã gudãna. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:51 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:51 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:52 فِيهِمَا مِن كُلِّ فَـٰكِهَةٍ زَوْجَانِ
55:52 A cikinsu akwai nau'i biyu daga kõwane 'ya'yan itãcen marmari. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:53 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:53 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:54 مُتَّكِـِٔينَ عَلَىٰ فُرُشٍۭ بَطَآئِنُهَا مِنْ إِسْتَبْرَقٍ ۚ وَجَنَى ٱلْجَنَّتَيْنِ دَانٍ
55:54 Sunã gincire a kan waɗansu shimfiɗu cikinsu tufãfin alharĩni mai kauri ne kuma nũnannun 'yã'yan itãcen Aljannar biyu kusakusa suke. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:55 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:55 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:56 فِيهِنَّ قَـٰصِرَٰتُ ٱلطَّرْفِ لَمْ يَطْمِثْهُنَّ إِنسٌ قَبْلَهُمْ وَلَا جَآنٌّ
55:56 A cikinsu akwai mãtã mãsu taƙaita ganinsu, wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗebe budurcinsu ba kuma haka wani aljani. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:57 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:57 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:58 كَأَنَّهُنَّ ٱلْيَاقُوتُ وَٱلْمَرْجَانُ
55:58 Kamar dai su yaƙũtu ne da murjãni. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:59 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:59 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:60 هَلْ جَزَآءُ ٱلْإِحْسَـٰنِ إِلَّا ٱلْإِحْسَـٰنُ
55:60 Shin, kyautatãwa nã da wani sakamako? (Ã'aha) fãce kyautatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:61 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:61 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:62 وَمِن دُونِهِمَا جَنَّتَانِ
55:62 Kuma baicinsu akwai waɗansu gidãjen Aljanna biyu. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:63 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:63 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:64 مُدْهَآمَّتَانِ
55:64 Mãsu duhun inuwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:65 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:65 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:66 فِيهِمَا عَيْنَانِ نَضَّاخَتَانِ
55:66 A cikinsu akwai marẽmari biyu masu kwarãrar ruwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:67 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:67 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:68 فِيهِمَا فَـٰكِهَةٌ وَنَخْلٌ وَرُمَّانٌ
55:68 A cikinsu akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno darummãni. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:69 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:69 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:70 فِيهِنَّ خَيْرَٰتٌ حِسَانٌ
55:70 A cikinsu, akwai wasu mãtã mãsu kyaun hãlãye, mãsu kyaun halitta. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:71 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:71 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:72 حُورٌ مَّقْصُورَٰتٌ فِى ٱلْخِيَامِ
55:72 Mãsu farin idãnu da baƙinsu waɗanda aka tsare a cikin haimõmi. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:73 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:73 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:74 لَمْ يَطْمِثْهُنَّ إِنسٌ قَبْلَهُمْ وَلَا جَآنٌّ
55:74 Wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗẽbe budurcinsu ba, kuma haka wani aljani. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:75 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:75 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:76 مُتَّكِـِٔينَ عَلَىٰ رَفْرَفٍ خُضْرٍ وَعَبْقَرِىٍّ حِسَانٍ
55:76 Sunã gincire a kan wasu matãsai mãsu kõren launi da katĩfun Abkara kyãwãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

55:77 فَبِأَىِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ
55:77 To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

55:78 تَبَـٰرَكَ ٱسْمُ رَبِّكَ ذِى ٱلْجَلَـٰلِ وَٱلْإِكْرَامِ
55:78 Sũnan Ubangjinka, Mai girman Jalãla da Karimci, ya tsarkaka. - Abubakar Gumi (Hausa)