Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

78 An-Naba' ٱلنَّبَأ

< Previous   40 Āyah   The Tidings      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

78:1 عَمَّ يَتَسَآءَلُونَ
78:1 A kan mẽ suke tambayar jũna? - Abubakar Gumi (Hausa)

78:2 عَنِ ٱلنَّبَإِ ٱلْعَظِيمِ
78:2 A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni)? - Abubakar Gumi (Hausa)

78:3 ٱلَّذِى هُمْ فِيهِ مُخْتَلِفُونَ
78:3 Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa? - Abubakar Gumi (Hausa)

78:4 كَلَّا سَيَعْلَمُونَ
78:4 A'aha! Zã su sani. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:5 ثُمَّ كَلَّا سَيَعْلَمُونَ
78:5 Kuma, a'aha! Zã su sani. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:6 أَلَمْ نَجْعَلِ ٱلْأَرْضَ مِهَـٰدًا
78:6 Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba? - Abubakar Gumi (Hausa)

78:7 وَٱلْجِبَالَ أَوْتَادًا
78:7 Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)? - Abubakar Gumi (Hausa)

78:8 وَخَلَقْنَـٰكُمْ أَزْوَٰجًا
78:8 Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã? - Abubakar Gumi (Hausa)

78:9 وَجَعَلْنَا نَوْمَكُمْ سُبَاتًا
78:9 Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa? - Abubakar Gumi (Hausa)

78:10 وَجَعَلْنَا ٱلَّيْلَ لِبَاسًا
78:10 Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura? - Abubakar Gumi (Hausa)

78:11 وَجَعَلْنَا ٱلنَّهَارَ مَعَاشًا
78:11 Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci? - Abubakar Gumi (Hausa)

78:12 وَبَنَيْنَا فَوْقَكُمْ سَبْعًا شِدَادًا
78:12 Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi? - Abubakar Gumi (Hausa)

78:13 وَجَعَلْنَا سِرَاجًا وَهَّاجًا
78:13 Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)? - Abubakar Gumi (Hausa)

78:14 وَأَنزَلْنَا مِنَ ٱلْمُعْصِرَٰتِ مَآءً ثَجَّاجًا
78:14 Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba? - Abubakar Gumi (Hausa)

78:15 لِّنُخْرِجَ بِهِۦ حَبًّا وَنَبَاتًا
78:15 Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi? - Abubakar Gumi (Hausa)

78:16 وَجَنَّـٰتٍ أَلْفَافًا
78:16 Da itãcen lambuna mãsu lillibniya? - Abubakar Gumi (Hausa)

78:17 إِنَّ يَوْمَ ٱلْفَصْلِ كَانَ مِيقَـٰتًا
78:17 Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:18 يَوْمَ يُنفَخُ فِى ٱلصُّورِ فَتَأْتُونَ أَفْوَاجًا
78:18 Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:19 وَفُتِحَتِ ٱلسَّمَآءُ فَكَانَتْ أَبْوَٰبًا
78:19 Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:20 وَسُيِّرَتِ ٱلْجِبَالُ فَكَانَتْ سَرَابًا
78:20 Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:21 إِنَّ جَهَنَّمَ كَانَتْ مِرْصَادًا
78:21 Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:22 لِّلطَّـٰغِينَ مَـَٔابًا
78:22 Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:23 لَّـٰبِثِينَ فِيهَآ أَحْقَابًا
78:23 Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:24 لَّا يَذُوقُونَ فِيهَا بَرْدًا وَلَا شَرَابًا
78:24 Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:25 إِلَّا حَمِيمًا وَغَسَّاقًا
78:25 Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:26 جَزَآءً وِفَاقًا
78:26 Sakamako mai dãcẽwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:27 إِنَّهُمْ كَانُوا۟ لَا يَرْجُونَ حِسَابًا
78:27 Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:28 وَكَذَّبُوا۟ بِـَٔايَـٰتِنَا كِذَّابًا
78:28 Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyinMu, ƙaryatãwa! - Abubakar Gumi (Hausa)

78:29 وَكُلَّ شَىْءٍ أَحْصَيْنَـٰهُ كِتَـٰبًا
78:29 Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:30 فَذُوقُوا۟ فَلَن نَّزِيدَكُمْ إِلَّا عَذَابًا
78:30 Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:31 إِنَّ لِلْمُتَّقِينَ مَفَازًا
78:31 Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:32 حَدَآئِقَ وَأَعْنَـٰبًا
78:32 Lambuna da inabõbi. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:33 وَكَوَاعِبَ أَتْرَابًا
78:33 Da cikakkun 'yammata, tsãrar jũna. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:34 وَكَأْسًا دِهَاقًا
78:34 Da hinjãlan giya cikakku. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:35 لَّا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا كِذَّٰبًا
78:35 Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:36 جَزَآءً مِّن رَّبِّكَ عَطَآءً حِسَابًا
78:36 Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:37 رَّبِّ ٱلسَّمَـٰوَٰتِ وَٱلْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ٱلرَّحْمَـٰنِ ۖ لَا يَمْلِكُونَ مِنْهُ خِطَابًا
78:37 Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:38 يَوْمَ يَقُومُ ٱلرُّوحُ وَٱلْمَلَـٰٓئِكَةُ صَفًّا ۖ لَّا يَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنْ أَذِنَ لَهُ ٱلرَّحْمَـٰنُ وَقَالَ صَوَابًا
78:38 Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:39 ذَٰلِكَ ٱلْيَوْمُ ٱلْحَقُّ ۖ فَمَن شَآءَ ٱتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ مَـَٔابًا
78:39 Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa. - Abubakar Gumi (Hausa)

78:40 إِنَّآ أَنذَرْنَـٰكُمْ عَذَابًا قَرِيبًا يَوْمَ يَنظُرُ ٱلْمَرْءُ مَا قَدَّمَتْ يَدَاهُ وَيَقُولُ ٱلْكَافِرُ يَـٰلَيْتَنِى كُنتُ تُرَٰبًۢا
78:40 Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!" - Abubakar Gumi (Hausa)