Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

96 Al-`Alaq ٱلْعَلَق

< Previous   19 Āyah   The Clot      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

96:1 ٱقْرَأْ بِٱسْمِ رَبِّكَ ٱلَّذِى خَلَقَ
96:1 Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta. - Abubakar Gumi (Hausa)

96:2 خَلَقَ ٱلْإِنسَـٰنَ مِنْ عَلَقٍ
96:2 Ya hahitta mutum daga gudan jini. - Abubakar Gumi (Hausa)

96:3 ٱقْرَأْ وَرَبُّكَ ٱلْأَكْرَمُ
96:3 Ka yi karatu, kuma UbangiJinka shi ne Mafi karimci. - Abubakar Gumi (Hausa)

96:4 ٱلَّذِى عَلَّمَ بِٱلْقَلَمِ
96:4 Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami. - Abubakar Gumi (Hausa)

96:5 عَلَّمَ ٱلْإِنسَـٰنَ مَا لَمْ يَعْلَمْ
96:5 Ya sanar da mutum abin da bai sani ba. - Abubakar Gumi (Hausa)

96:6 كَلَّآ إِنَّ ٱلْإِنسَـٰنَ لَيَطْغَىٰٓ
96:6 A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu). - Abubakar Gumi (Hausa)

96:7 أَن رَّءَاهُ ٱسْتَغْنَىٰٓ
96:7 Dõmin yã ga kansa, yã wadãta. - Abubakar Gumi (Hausa)

96:8 إِنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلرُّجْعَىٰٓ
96:8 Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take. - Abubakar Gumi (Hausa)

96:9 أَرَءَيْتَ ٱلَّذِى يَنْهَىٰ
96:9 Shin, kã ga wanda ke hana. - Abubakar Gumi (Hausa)

96:10 عَبْدًا إِذَا صَلَّىٰٓ
96:10 Bãwã idan yã yi salla? - Abubakar Gumi (Hausa)

96:11 أَرَءَيْتَ إِن كَانَ عَلَى ٱلْهُدَىٰٓ
96:11 Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya? - Abubakar Gumi (Hausa)

96:12 أَوْ أَمَرَ بِٱلتَّقْوَىٰٓ
96:12 Ko ya yi umurni da taƙawa? - Abubakar Gumi (Hausa)

96:13 أَرَءَيْتَ إِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰٓ
96:13 Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya? - Abubakar Gumi (Hausa)

96:14 أَلَمْ يَعْلَم بِأَنَّ ٱللَّهَ يَرَىٰ
96:14 Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani? - Abubakar Gumi (Hausa)

96:15 كَلَّا لَئِن لَّمْ يَنتَهِ لَنَسْفَعًۢا بِٱلنَّاصِيَةِ
96:15 A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa. - Abubakar Gumi (Hausa)

96:16 نَاصِيَةٍ كَـٰذِبَةٍ خَاطِئَةٍ
96:16 Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi. - Abubakar Gumi (Hausa)

96:17 فَلْيَدْعُ نَادِيَهُۥ
96:17 Sai ya kirayi ƙungiyarsa. - Abubakar Gumi (Hausa)

96:18 سَنَدْعُ ٱلزَّبَانِيَةَ
96:18 Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma). - Abubakar Gumi (Hausa)

96:19 كَلَّا لَا تُطِعْهُ وَٱسْجُدْ وَٱقْتَرِب ۩
96:19 A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u, kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka). - Abubakar Gumi (Hausa)