Selected

Original Text
Abubakar Gumi

Available Translations

80 `Abasa عَبَسَ

< Previous   42 Āyah   He Frowned      Next >  

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.

80:1 عَبَسَ وَتَوَلَّىٰٓ
80:1 Yã game huska kuma ya jũya bãya. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:2 أَن جَآءَهُ ٱلْأَعْمَىٰ
80:2 Sabõda makãho yã je masa. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:3 وَمَا يُدْرِيكَ لَعَلَّهُۥ يَزَّكَّىٰٓ
80:3 To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:4 أَوْ يَذَّكَّرُ فَتَنفَعَهُ ٱلذِّكْرَىٰٓ
80:4 Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi? - Abubakar Gumi (Hausa)

80:5 أَمَّا مَنِ ٱسْتَغْنَىٰ
80:5 Amma wanda ya wadãtu da dũkiya. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:6 فَأَنتَ لَهُۥ تَصَدَّىٰ
80:6 Sa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi! - Abubakar Gumi (Hausa)

80:7 وَمَا عَلَيْكَ أَلَّا يَزَّكَّىٰ
80:7 To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba? - Abubakar Gumi (Hausa)

80:8 وَأَمَّا مَن جَآءَكَ يَسْعَىٰ
80:8 Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:9 وَهُوَ يَخْشَىٰ
80:9 Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:10 فَأَنتَ عَنْهُ تَلَهَّىٰ
80:10 Kai kuma kã shagala ga barinsa! - Abubakar Gumi (Hausa)

80:11 كَلَّآ إِنَّهَا تَذْكِرَةٌ
80:11 A'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:12 فَمَن شَآءَ ذَكَرَهُۥ
80:12 Sabõda wanda ya so ya tunaShi (Allah). - Abubakar Gumi (Hausa)

80:13 فِى صُحُفٍ مُّكَرَّمَةٍ
80:13 (Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa, - Abubakar Gumi (Hausa)

80:14 مَّرْفُوعَةٍ مُّطَهَّرَةٍۭ
80:14 Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:15 بِأَيْدِى سَفَرَةٍ
80:15 A cikin hannãyen mala'iku marubũta. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:16 كِرَامٍۭ بَرَرَةٍ
80:16 Mãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:17 قُتِلَ ٱلْإِنسَـٰنُ مَآ أَكْفَرَهُۥ
80:17 An la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa! - Abubakar Gumi (Hausa)

80:18 مِنْ أَىِّ شَىْءٍ خَلَقَهُۥ
80:18 Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi? - Abubakar Gumi (Hausa)

80:19 مِن نُّطْفَةٍ خَلَقَهُۥ فَقَدَّرَهُۥ
80:19 Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye). - Abubakar Gumi (Hausa)

80:20 ثُمَّ ٱلسَّبِيلَ يَسَّرَهُۥ
80:20 Sa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:21 ثُمَّ أَمَاتَهُۥ فَأَقْبَرَهُۥ
80:21 Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:22 ثُمَّ إِذَا شَآءَ أَنشَرَهُۥ
80:22 Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:23 كَلَّا لَمَّا يَقْضِ مَآ أَمَرَهُۥ
80:23 Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari). - Abubakar Gumi (Hausa)

80:24 فَلْيَنظُرِ ٱلْإِنسَـٰنُ إِلَىٰ طَعَامِهِۦٓ
80:24 To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:25 أَنَّا صَبَبْنَا ٱلْمَآءَ صَبًّا
80:25 Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:26 ثُمَّ شَقَقْنَا ٱلْأَرْضَ شَقًّا
80:26 Sa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:27 فَأَنۢبَتْنَا فِيهَا حَبًّا
80:27 Sa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya, a cikinta. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:28 وَعِنَبًا وَقَضْبًا
80:28 Da inabi da ciyãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:29 وَزَيْتُونًا وَنَخْلًا
80:29 Da zaitũni da itãcen dabĩno. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:30 وَحَدَآئِقَ غُلْبًا
80:30 Da lambuna, mãsu yawan itãce. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:31 وَفَـٰكِهَةً وَأَبًّا
80:31 Da 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:32 مَّتَـٰعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَـٰمِكُمْ
80:32 Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:33 فَإِذَا جَآءَتِ ٱلصَّآخَّةُ
80:33 To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:34 يَوْمَ يَفِرُّ ٱلْمَرْءُ مِنْ أَخِيهِ
80:34 Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:35 وَأُمِّهِۦ وَأَبِيهِ
80:35 Da uwarsa da ubansa. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:36 وَصَـٰحِبَتِهِۦ وَبَنِيهِ
80:36 Da mãtarsa da ɗiyansa. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:37 لِكُلِّ ٱمْرِئٍ مِّنْهُمْ يَوْمَئِذٍ شَأْنٌ يُغْنِيهِ
80:37 Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:38 وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ مُّسْفِرَةٌ
80:38 Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:39 ضَاحِكَةٌ مُّسْتَبْشِرَةٌ
80:39 Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:40 وَوُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ عَلَيْهَا غَبَرَةٌ
80:40 Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:41 تَرْهَقُهَا قَتَرَةٌ
80:41 Baƙi zai rufe su. - Abubakar Gumi (Hausa)

80:42 أُو۟لَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلْكَفَرَةُ ٱلْفَجَرَةُ
80:42 Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu). - Abubakar Gumi (Hausa)