Selected
Original Text
Abubakar Gumi
Abdullah Yusuf Ali
Abdul Majid Daryabadi
Abul Ala Maududi
Ahmed Ali
Ahmed Raza Khan
A. J. Arberry
Ali Quli Qarai
Hasan al-Fatih Qaribullah and Ahmad Darwish
Mohammad Habib Shakir
Mohammed Marmaduke William Pickthall
Muhammad Sarwar
Muhammad Taqi-ud-Din al-Hilali and Muhammad Muhsin Khan
Safi-ur-Rahman al-Mubarakpuri
Saheeh International
Talal Itani
Transliteration
Wahiduddin Khan
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
In the name of Allah, Most Gracious, Most Merciful.
89:1
وَٱلْفَجْرِ
89:1
Inã rantsuwa da alfijiri. - Abubakar Gumi (Hausa)
89:2
وَلَيَالٍ عَشْرٍ
89:2
Da darũruwa gõma. - Abubakar Gumi (Hausa)
89:3
وَٱلشَّفْعِ وَٱلْوَتْرِ
89:3
Da (adadi na) cikã da (na) mãrã. - Abubakar Gumi (Hausa)
89:4
وَٱلَّيْلِ إِذَا يَسْرِ
89:4
Da dare idan yana shũɗewa. - Abubakar Gumi (Hausa)
89:5
هَلْ فِى ذَٰلِكَ قَسَمٌ لِّذِى حِجْرٍ
89:5
Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)? - Abubakar Gumi (Hausa)
89:6
أَلَمْ تَرَ كَيْفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِعَادٍ
89:6
Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba? - Abubakar Gumi (Hausa)
89:7
إِرَمَ ذَاتِ ٱلْعِمَادِ
89:7
Iramawa mãsu sakon ƙĩrar jiki. - Abubakar Gumi (Hausa)
89:8
ٱلَّتِى لَمْ يُخْلَقْ مِثْلُهَا فِى ٱلْبِلَـٰدِ
89:8
Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya). - Abubakar Gumi (Hausa)
89:9
وَثَمُودَ ٱلَّذِينَ جَابُوا۟ ٱلصَّخْرَ بِٱلْوَادِ
89:9
Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi suka yi gidãje)? - Abubakar Gumi (Hausa)
89:10
وَفِرْعَوْنَ ذِى ٱلْأَوْتَادِ
89:10
Da Fir'auna mai turãku. - Abubakar Gumi (Hausa)
89:11
ٱلَّذِينَ طَغَوْا۟ فِى ٱلْبِلَـٰدِ
89:11
Waɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa? - Abubakar Gumi (Hausa)
89:12
فَأَكْثَرُوا۟ فِيهَا ٱلْفَسَادَ
89:12
Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu. - Abubakar Gumi (Hausa)
89:13
فَصَبَّ عَلَيْهِمْ رَبُّكَ سَوْطَ عَذَابٍ
89:13
Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba. - Abubakar Gumi (Hausa)
89:14
إِنَّ رَبَّكَ لَبِٱلْمِرْصَادِ
89:14
Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka. - Abubakar Gumi (Hausa)
89:15
فَأَمَّا ٱلْإِنسَـٰنُ إِذَا مَا ٱبْتَلَىٰهُ رَبُّهُۥ فَأَكْرَمَهُۥ وَنَعَّمَهُۥ فَيَقُولُ رَبِّىٓ أَكْرَمَنِ
89:15
To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni." - Abubakar Gumi (Hausa)
89:16
وَأَمَّآ إِذَا مَا ٱبْتَلَىٰهُ فَقَدَرَ عَلَيْهِ رِزْقَهُۥ فَيَقُولُ رَبِّىٓ أَهَـٰنَنِ
89:16
Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni." - Abubakar Gumi (Hausa)
89:17
كَلَّا ۖ بَل لَّا تُكْرِمُونَ ٱلْيَتِيمَ
89:17
A'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya! - Abubakar Gumi (Hausa)
89:18
وَلَا تَحَـٰٓضُّونَ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلْمِسْكِينِ
89:18
Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci! - Abubakar Gumi (Hausa)
89:19
وَتَأْكُلُونَ ٱلتُّرَاثَ أَكْلًا لَّمًّا
89:19
Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa. - Abubakar Gumi (Hausa)
89:20
وَتُحِبُّونَ ٱلْمَالَ حُبًّا جَمًّا
89:20
Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa. - Abubakar Gumi (Hausa)
89:21
كَلَّآ إِذَا دُكَّتِ ٱلْأَرْضُ دَكًّا دَكًّا
89:21
A'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai. - Abubakar Gumi (Hausa)
89:22
وَجَآءَ رَبُّكَ وَٱلْمَلَكُ صَفًّا صَفًّا
89:22
Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, safũ- safu. - Abubakar Gumi (Hausa)
89:23
وَجِا۟ىٓءَ يَوْمَئِذٍۭ بِجَهَنَّمَ ۚ يَوْمَئِذٍ يَتَذَكَّرُ ٱلْإِنسَـٰنُ وَأَنَّىٰ لَهُ ٱلذِّكْرَىٰ
89:23
Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi! - Abubakar Gumi (Hausa)
89:24
يَقُولُ يَـٰلَيْتَنِى قَدَّمْتُ لِحَيَاتِى
89:24
Yana dinga cẽwa, "Kaitona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata!" - Abubakar Gumi (Hausa)
89:25
فَيَوْمَئِذٍ لَّا يُعَذِّبُ عَذَابَهُۥٓ أَحَدٌ
89:25
To, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah. - Abubakar Gumi (Hausa)
89:26
وَلَا يُوثِقُ وَثَاقَهُۥٓ أَحَدٌ
89:26
Kuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurinSa. - Abubakar Gumi (Hausa)
89:27
يَـٰٓأَيَّتُهَا ٱلنَّفْسُ ٱلْمُطْمَئِنَّةُ
89:27
Yã kai rai mai natsuwa! - Abubakar Gumi (Hausa)
89:28
ٱرْجِعِىٓ إِلَىٰ رَبِّكِ رَاضِيَةً مَّرْضِيَّةً
89:28
Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya) abar yardarwa (da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira). - Abubakar Gumi (Hausa)
89:29
فَٱدْخُلِى فِى عِبَـٰدِى
89:29
Sabõbda haka, ka shiga cikin bãyiNa (mãsu bin umurui a dũniya). - Abubakar Gumi (Hausa)
89:30
وَٱدْخُلِى جَنَّتِى
89:30
Kuma ka shiga AljannaTa (a Lãhira). - Abubakar Gumi (Hausa)